Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilin da ya sa PDP ta koma neman kudi a hannun ƴaƴan jam'iyyarta
Jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, ta bayyana dalilin da ya sa za ta fara neman kudi a hannun 'ya'yan jam'iyyar a wani mataki na kawo ƙarshen siyasar ubangida a jam'iyyar.
A cewar jam'iyyar, matakin ba shi da nasaba da rikicin shugabanci da ta ke fuskanta da kuma ficewar da ake yi a jam'iyyar.
Mataimakiyar mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP Farida Umar, ta shaida wa BBC cewa, a yadda jam'iyyar ta ke a yanzu za mu mayarwa wa jama'a ita ne.
Ta ce," A lokacin da aka kafa jam'iyyar a baya ai ba ta da gwamna ko shugaban karamar hukuma ko Kansila, ba ta da komai, a don haka yanzu ma so muke mu mai da ta yadda ta ke a da."
"Idan 'ya'yan jam'iyya na biyan kudaden kasancewa 'yan jam'iyya yadda ya kamata, ba sai gwamnonin jam'iyya sun rika bayar da kudaden tafiyar da ita ba."In ji ta.
Farida Umar, ta ce Ida ana so jam'iiya ta ci gaba ai dole ne a lalubo hanyoyin da za a ciyar da ita gaba, ba wai lallai sai an jira wasu tsiraru ko masu rike da mukamai ba, don haka shi ya sa muka dauki wannan mataki.
Mataimakiyar mai magana da yawun jam'iyyar ta PDP, ta ce batun tallafawa jam'iyya ba wai lallai sai masu mulki ba, su kansu 'ya'yan jam'iyyar akwai rawar da za su taka wajen ciyar da ita gaba, kuma komai suka bayar komai kankantarsa don a tafiyar da jam'iyya zai taimaka.
Ta ce,"Ya kamata mutane su sani, wai don gwamnoni ko masu rike da mukaman siyasa na tallafawa jam'iyya, ba lallai a rinka bin abin da suke so ba, mu a jam'iyyarmu kowa daya ne, jam'iyya ce ta talaka, kuma duk wanda ke son tsayawa neman wani mukami ana ba shi dama muddin ya cika ka'idojin da ake so."
Farida Umar, ta ce ba za su fara amfani da wannan tsari ba har sai sun ji ta bakin talakawa 'ya'yan jam'iyyar idan sun amince sai a fara amfani da shi. Idan kuwa aka samu akasin haka to sai a nemi wata mafitar in ji ta.
Jam'iyyar PDP dai ta daɗe tana fama da rikice-rikice, musamman tun bayan zaɓen fitar da ƴan takara da Atiku ya doke Wike, lamarin da ya sa Wike da wasu gwamnoni suka ware, suka yi tallata Atiku a babban zaɓen.
Amma wannan rikicin ya samo asali daga babban taron jam'iyyar da aka yi a watan Nuwamba, inda babbar jam'iyyar ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki a matsayin sabon shugabanta, duk da irin jimirɗar da aka yi fama da ita gabanin zaɓen.
Kuma sauya shekar da wasu jiga-jigan jam'iyar suka yi ya sa tasirin jam'iyyar na raguwa.
Rikicin da jam'iyyar ke fama da shi ya ki ci ya ki cinyewa, ta yadda abubuwa daban-daban ke ɓullowa game da jam'iyyar a kullu-yaumin.