Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Na yi mamakin yadda ƴan PDP suka juya mani baya - Sule Lamido
Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP mai hamayya a Najeriya, Sule Lamido, ya zargi ƴan jama'iyyar tasa da juya masa baya kan ƙudirinsa na neman shugabancin jam'iyyar na ƙasa.
A tsakiyar makon nan ne Sule Lamido ya ce jam'iyyar ta hana shi damar sayen fom ɗin tsayawa takara a lokacin da ya je harabar sakatariyar jam'iyyar a Abuja domin sayen takardar.
Cikin wata hira da BBC, Sule Lamido ya ce ya yi "matuƙar mamaki da takaici" kan yadda abin da ya faru da shi a PDP.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya ce akwai "matuƙar raini" a matsayinsa na wanda ya bai wa PDP da Najeriya gudunmawa a yi ƙoƙarin hana shi tsayawa takara a jam'iyyar da suka yi fama wajen kafuwarta.
'Hira mafi wuya a rayuwata'
A lokacin tattaunawar da BBC, Sule Lamido ya nuna cewa wannan ce hira mafi wuya a gare shi.
"Domin kuwa abu ne da ya shafe ni, yin magana a kan siyasa ko a wani abu da ya shafi ƙasa, ko gwamnati, da duk wani abu da zan fadi ra'ayi, ba na shakkar magana a kansa, amma wannan abu ne da ya shafe ni,'' in ji shi.
''In aka ce abu a kaina ne to yana mani wuya da takaici da kuma ciwo na yi magana a kansa''.
Sule Lamido - wanda tsohon ministan harkokin wajen Najeriya ne - ya ce ya ji takaicin yadda waɗanda yake ganin makusanta ne suke yi masa yankan baya.
''A wayi gari na ce zan yi takara a cikin gidanmu, kuma a ce ƴan'uwana da dangina, abokan tafiyata da muke yin komai da komai tare, su ce wai ba za a ba ni takara ba, har sai na je kotu, ina ganin wannan shi ne babban abin takaici a rayuwata,'' in ji shi.
'An san da takarata'
Sule Lamido ya yi iƙirarin cewa mambobin jam'iyyar suna sane da batun takararsa, tun da farko.
''Mun yi magana da Maƙarfi, kuma ya ƙarfafa min gwiwa kan batun, sannan aka ware wa shiyyarmu ta arewa maso yamma, kujerar shugabancin jam'iyya'', in ji shi.
Sule Lamido ya yi ikirarin cewa gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya shirya wani taro a Abuja a ranar Larabar da ta gabata, da nufin mambobin jam'iyyar da suka fito daga shiyyar arewa maso yammacin ƙasar su zauna domin kasafta muƙamin da aka ware musu.
''Amma kafin taron sai a ranar Talata gwamnonin PDP suka kira wani taro domin sake duba batun''.
Sule Lamido ya yi zargin cewa a taron ne gwamnonin suka ce kada a kawo mutumin da ba sa goyon baya a matsayin shugaban PDP daga shiyyar arewa maso yamma.
''Daga nan sai suka riƙa kiran mutane ɗaya-bayan ɗaya domin shirya abin da suke so'', in ji shi.
'Yadda aka shatale ni'
Sule Lamido ya ce a wannan zama ne jagoran shugaban jam'iyyar na arewa maso yamma, Bello Hakatu ya ce ai mambobin arewa maso yamma ba su zauna ba, domin tattauna batun muƙamin da aka ware wa shiyyar.
Sule Lamido ya kuma zargi Bello Hayatu da Gwamnan Dauda Lawal da rashin faɗa wa taron cewa mambobinta na yankin arewa maso yamma ba su zauna domin tattauna muƙamin da aka ware musu ba.
Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya kuma ce a nan ne aka bijiro da batun muƙamin shugabancin jam'iyyar, inda tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau da Kabiru Tanimu Turaki suka nuna sha'awarsu ta zama shugaban jam'iyyar.
Sule Lamido ya kuma zargi gwamnan Bauchi da ƙoƙarin ƙaƙaba Mallam Shekarau.
''Dama Shekarau suke so, don ya gaya musu, sannan Bala Mohammed ya yi masa alƙawarin shi za a bai wa, amma a wuroin taro sai Kabiru Tanimu Turaki, shi ma ya nuna sha'awarsa''.
''Daga nan saia ka ce babu wani, sai Maƙarfi ya ce a a Sule Lamido ya ce min zai yi takara, amma ba ku kira shi ba, amma ba su kirani ba, kuma Bala da Fintiri duk babu wanda ba shi da numbata'', in ji Sule Lamido.
''Sai aka buƙaci Kabiru da Shekarau su je waje su tattauna a tsakaninsu, domin ɗaya ya janye wa ɗayan, sai kuma aka ce musu wai su kirani a waya, su fada min abin da aka cimma''.
'Abin akwai raini a ciki'
Sule Lamido ya ce abin tamkar raini ne a ce waɗanda yake ganin ba su kai shi kishin PDP ne za su kira shi kan batun jam'iyyar.
''Ba wai batun jiji-da-kai ko cika-baki ba, yanzu a ce Shekarau da Tanimu su ne za su kira a kan batun PDP, ai sai in ga kamar akwai raini a ciki''
''Bayan da Shekarau ya kirani ya kuma faɗa min abin da ke faruwa, sai na ce masa yanzu Shekarau kai ne za ka kira kan batun wai an ce mu yi sulhu? To gaskiya ni ba zan janye wa kowa ba'', kamar yadda Sule Lamidon ya shaida wa BBC.
''Daga nan na ce masa ni zan yi takara a je zaɓe koda kuwa ƙuri'a ɗaya zan samu'', in ji shi.
Sule Lamido ya ce a yanzu da aka hana shi damar sayen for ɗin takara, tuni ya garzayua kotu domin ƙalubalantar matakin.
'Ina son riƙe PDP ne don hana ƴanjam'iyyar shiga APC'
Sule Lamido ya ce abin da ya sa yake yunƙurin zama shugaban PDP shi ne domin hana ƴan jam'iyyar komawa APC.
''Dama ai so ake mu yi APC, mu manyan, to idan na zama shugaban PDP, wani ma ya sake zuwa ya ce mu yi APC ya gani'', in ji shi.
Jam'iyyar PDP dai na da tarin matsalolin rikicin cikin gida, lamarin da ya sanya wasu jiga-jigan jam'iyyar ficewa daga cikinta, inda wasu suka koma APC mai mulki.
Ka a ranar Alhamis ma sai da wasu ƴan majalisar wakilan ƙasar biyar daga jam'iyyar suka koma APC.
Baya ga gwamnoni aƙalla uku da suka fice daga jam'iyyar a shekarar nan, yanzu haka gwamnoni takwas ne dai suka rage wa jam'iyyar.