Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace dabara ta rage wa PDP?
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP na ci gaba da nutsewa cikin rikici bayan da kotuna daban-daban ke bayar da mabambantan hukunce-hukunce game da babban taronta na ƙasa.
A ranar Talata wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake dakatar da jam'iyyar daga gudanar da babban taronta da take shirin yi a garin Ibadan na jiyar Oyo.
Wannan shi ne karo na biyu da kotu ta hana gudanar da taron, wanda babbar jam'iyyar hamayyar ke shirin yi a ranakun 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Sai dai kafin wannan hukuncin na biyu, wata kotun a jiyar Oyo ta umarci jam'iyyar da ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta na babban taron, wanda hakan ya haifar taraddudi.
A wannan shari'a ta baya-baya, tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ne ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar hana shi yin takarar shugabancin jam'iyyar.
Lamido ya shigar da ƙara ne yana buƙatar kotu ta dakatar da jam'iyyar daga zaɓen fitar da sababbin shugabanni.
Wannan shi ne rikici na baya-bayan da PDP ta faɗa a ciki, bayan rikicin shugabanci da ta dade tana fama da shi.
A yanzu haka baya ga shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin Iliya Damagun, akwai wani ɓangaren da ke iƙirarin shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Abdulrahman Muhammed, wanda har ya kafa wani kwamitin amintattu na daban ƙarƙashin jagorancin Sanata Mao Ohuabunwa.
Martanin ɓangarorin PDP
Babandi Ibrahim Gumel, wanda shi ne shugaban jam'iyyar PDP a jihar Jigawa ya ce dalilin da suka sa ɓangaren Sule Lamiɗo ya yanke shawarar zuwa kotu shi ne saboda ''an gaza samun malaha ta hanyar lalama".
Ya ƙara da cewa Sule Lamido bai je kotu domin a hana jam'iyyar gudanar da babban taronta ba, sai dai "domin a yi taron yadda ya kamata, ba lallai sai an yi shi a lokacin da aka tsara ba a yanzu."
A ɗaya ɓangaren, ɗaya daga cikin ginshiƙan jam'iyyar da ke tare da shugaban jam'iyyar Iliya Damagun, Umar Tsauri ya ce lamarin abu ne da ya kamata a warware shi ta hanyar tattaunawa, ba a kotu ba.
Ya ce tuni jam'iyyar ta kafa kwamitin sulhuntawa tsakanin ɓangarorin da ke adawa da juna, amma ba a fara zama ba har zuwa lokacin da kotun ta yanke wannan hukunci.
Umar Tsauri ya ce "zuwa kotu ba ya taimaka wa jam'iyya kuma ɓatanci yake haifarwa".
Mece ce mafita?
Masani kan harkokin siyasa, Farfesa Abubakar Kari, malami a Jami'ar Abuja ya ce "akwai sarƙaƙaiya game da halin da jam'iyyar PDP take ciki kuma sai dai a yi hasashe game da makomar jam'iyyar".
Ya ambato zargin da wasu daga cikin ƴaƴan jam'iyyar ke yi na cewa akwai "wasu mutane da suke haddasa husuma a cikin jam'iyyar da gangan domin tabbatar da cewa ba ta taka rawar gani ba a babban zaɓen ƙasar mai zuwa."
Ya ce "abin da suke yi da gangan ne domin ganin jam'iyyar ta ɓalɓalce, ta rasa girma da kimarta."
Kari ya ƙara da cewa ba za a iya yin sulhu da irin waɗannan mutane ba.
Sai dai ya bayyana cewa akwai ɓangarorin da ke taƙaddama da shugabancin jam'iyyar wadanda za a iya sulhuntawa da su.
"Kamar irin su Sule Lamido, ana iya sulhuntawa da su, takara kawai ya ce yana so ya yi, kuma takara ba cin zaɓe ba ne.
"Idan aka dage cewa ba zai yi takara ba, har aka bari ya je kotu, ni ina ganin kamar shugabannin jam'iyyar sun daɓa wa kansu wuƙa ne a ciki."
A ƙarshe malamin jami'ar ya bayyana cewa babu tabbas game da yiwuwar ficewar PDP daga rikicin da take ciki gabanin babban zaɓe na 2027.
"Akwai wadanda za a iya sasanta rigimar da ake yi da su, akwai kuma wadanda sai dai a yi taho mu gama da su," a cewar Kari.
Wasa kusa da wuta
Masanin siyasar ya yi hasashen cewa idan har aka ƙara nan da wata uku ko huɗu jam'iyyar ba ta magance matsalolinta ba "to ina ganin zaɓukan 2027 sai dai su ji a salansa”.
Ya bayyana cewa ya zuwa watan Afrilu ko Mayun shekara ta 2026 za a fara maganar zaɓukan fitar da gwani, kuma a ƙa'ida shugaba da sakataren jam’iyya ne za su riƙa tura sunayen masu yin takara kuma wajibi ne sai hukumar zaɓe ta halarci tarukan da za a yi.
"To idan ana samun hukunce-hukuncen kotu wadanda za su hana hukumar zaɓe halartar wadannan taruka da kuma taƙaddama kan ko su wane ne shugabanni na haƙiƙa, ko da sun yi zaɓukan fitar da gwani ba lallai ne a sahhale wa waɗanda suka samu nasara su shiga zaɓe ba," in ji masanin.
Turmin tsakar gida...
Sai dai masanin siyasar ya bayyana cewa PDP ta sha shiga cikin rikita-rikita ta siyasa a baya, amma duk da haka ta sulhunta kuma ta ci gaba da kasancewa jam'iyya mai ƙarfi da kwarjini a faɗin ƙasar.
‘’Wannan ba shi ne karon farko da PDP ta taɓa samun kanta a irin wannan hali ba, duk da cewa a baya rikicin bai kai har gab da zaɓe ba.
"Idan an tuna bayan faɗuwa zaɓe a 2015, jam'iyyar ta faɗa cikin rikicin shugabanci har ta samu shugabanni biyu - Ali Modu Sharif da Ahmed Makarfi - har sai da aka kai kotun ƙoli."
Ya bayyana cewa har yanzu PDP na da ƙarfi, da ɗimbin magoya baya da kuma tsari a kowane yanki na ƙasar nan, "sai dai abin da ke faruwa a cikinta na mata illa sosai, kuma hakan na rage mata girma da ƙima."