Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kisan gilla biyar na baya-bayan nan da suka tayar da hankali a Kano
Al'ummar Kano da ma sassan Najeriya sun girgiza kan kisan da aka yi wa wata mata da ƴaƴanta shida a birnin na Kano.
Lamarin ya faru ne ranar Asabar a unguwar Charanci Ɗorayi a cikin ƙwaryar birnin Kano da tsakar rana.
Tuni rundunar ƴansandan jihar ta kama wasu mutum uku da ake zargi da aikata kisan, tare da ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Ba wannan ne karon farko da aka samu mummunan kisan gilla da ya tayar da hankali a jihar Kano ba.
A lokuta da dama da suka gabata, an riƙa samun labaran yadda ake yi wa mutanen kisan gilla a jihar, da ke zama cibiyar kasuwancin arewacin ƙasar.
Ga wasu lokuta biyar da aka gudanar da irin wannan kisan gilla da suka ɗauki hankali a jihar a baya-bayan nan.
Kisan mace da yaranta shida a Chiranci
A ranar Asabar 17 ga watan Janairun 2026 ne aka samu labarin kisan wata mata tare da ƴaƴanta shida a Unguwar Chiranci Ɗorayi.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce mutanen sun afka wa Fatima Abubakar mai shekara 35 da ƴaƴanta shida, da muggan makamai inda suka ji masu munanan raunuka.
Tuni dai rundunar ƴansandan ta sanar da kama wasu mutum uku da ake zargi da aikata kisan da rana tsaka, bayan da suka bubbuge su da makamai, suka kuma jefa wasu yaran cikin rijiyar gidan bayan kashe su.
Wannan al'amari ya jefa al'ummar jihar cikin jimami da kaɗuwa ganin yadda aka yi wa mutanen kisan gilla a cikin gidansu.
Ƙona kishiyoyi biyu a gidansu a Tudun Yola
A ranar 13 ga watan Nuwamban 2025 wasu mutane da ba a san kowa su wane ba, suka haura gidan wasu matan aure (uwargida da amarya) a unguwar Tudun Yola, inda suka halaka su tare da ƙona gawarwakinsu.
Shi ma wannan lamarin ya ɗaga wa al'ummar jihar hankali kasancewar shi ma ya faru ne da tsakar rana, lokacin da maigidan baya nan kuma babu zirga-zirgar mutane a unguwar.
Cikin wata sanarwa da rundunar yansandan jihar ta fitar a lokacin faruwar lamarin, ta ce tana cikin bincike domin farauto waɗanda ake zargi.
Ƴansandan sun ce sun gano wasu wayoyin hannu guda biyu - da suke tsammanin na waɗanda suka aikata laifin ne.
Sai dai bayan kisan baya-bayan nan na ranar Asabar, ƴansandan sun ce mutanen da suka kama na da alaƙa da kisan matan na unguwar Tudun Yola.
Kisan Sadiq Gentle
A farkon watan Agustan 2025 ne wasu mahara suka kai wa wani matashi, wanda babban jami'in yaɗa labarai ne a ma'aikatar tarihi da al'adu ta jihar.
Maharan sun ji wa matashin - mai suna Sadiq Gentle - munanan raunuka, lamarin da ya sa aka garzaya da shi asibitin Murtala kafin daga bisani ya mutu.
Mutuwar matashin ta girgiza al'umma da dama, ciki har da Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce kisan "keta haƙƙin bil'adama ne da ba za a lamunta ba".
Kisan DPO a Rano
A farkon watan Yulin 2025 ne wasu matasa suka kutsa ofishin ƴansanda da ke ƙaramar hukumar Rano a jihar tare da kashe babban baturen ƴansandan ƙaramar hukumar, CSP Baba Ali.
Lamarin ya faru ne bayan da wasu matasan garin suka zargi jami'an ƴansanda da hannu a mutuwar wani matashi a hannunsu bayan kama shi.
Kisan ya ɗaga wa jama'a da dama hankali ganin yadda aka yi ta yaɗa bidiyon DPOn a shafukan sada zumunta a lokacin da ake bugunsa har ya rasu.
Daga baya rundunar ƴansandan jihar ta ƙaddamar da bincike tare da kama wasu matasa da take zargi da hannu a lamarin ta kuma gurfanar da su a gaban kotu cikin watan Agustan shekarar.
Kwamishinan ƴansanda a jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce kisan jami'in nasu babban abin takaici da tashin hankali ne.
Ƙona mutane a masallacin Gezawa
A ranar 15 ga watan Mayun 2024 aka wayi gari da wani mummunan iftila'i da za a jima ba a manta da shi ba a Kano, bayan da wani matashi ya cinna wa masu ibada wuta a cikin masallaci sannan ya ƙulle su a lokacin sallar asuba.
Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 23, inda 15 suka mutu nan take yayin da sauran suka mutu a asibiti.
Shi ma wannan kisa ya ɗaga hankalin mutane tare da janyo suka daga ɓangarori daban-daban na ciki da wajen jihar.
Rahotanni a lokacin sun ce matashin mai shekara 38 ya cinna wutar ne sanadiyyar rikici da yake yi da wani ɗan'uwansa a kan rabon gado.
A watan Mayun 2025 ne dai babbar kotun musulunci da ke jihar Kano ta yanke wa mutumin mai suna - Shafiu Abubakar- hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifin da kashe masallatan.
Baya ga waɗannan na baya-bayan nan akwai wasu kashe-kashen da suka shahara a jihar da ba za a manta da su ba, kamar na Hanifa, wata ƙaramar yarinya da aka kaske bayan garkuwa da ita a 2021.
Da kuma kisan fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Ja'afar Adam da aka yi lokacin da yake tsaka da jagorantar sallar asuba a shekarar 2007.