Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 20 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Australia na shirin sayen bindigogi daga hannun jama’a bayan kisan Bondi

    Majalisar wakilan Australia ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da wani shirin ƙasa na sayen bindigogi daga hannun jama'a, da kuma fara sabon tsarin gudanar da bincike kafin bada izinin mallakar makami a ƙasar.

    An zartar da ƙudirin dokar ne bayan wakilai 96 suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da shi, yayin da 45 suka nemi a soke shi.

    Yanzu dai ƙudirin dokar zai ƙarasa majalisar dattawa, inda a can ma ake sa ran ya samu tsallakewa.

    Matakin na zuwa ne wata guda bayan mummunan harin gaɓar tekun Bondi, inda wasu mahara suka buɗe wuta kan Yahudawa masu biki a wajen, suka kuma kashe mutane 15.

  2. Bobi Wine ya yi kira ga ƴan Uganda su tashi tsaye kan mulkin Yoweri Museveni

    Jagoran ƴan adawan Uganda Bobi Wine, ya yi kira ga jama'ar ƙasar su tashi tsaye domin yin turjiya ga abin da ya kira mulkin kama-karya na shugaba Yoweri Museveni.

    A wata hira da BBC, Mista Wine ya ce zai ci gaba da ƙalubalantar Museveni duk da hatsarin da hakan ke da shi ga rayuwarsa.

    Ya ce: Mun ga yadda jama'ar Uganda ke ci gaba da yaƙi da abubuwan da ake masu, domin a zahiri ta ke mutane za su yi turjiya ga cin zarafi.

    Ya dai jaddada iƙirarin cewa jami'an tsaro a Uganda na son kama shi domin cutar da shi, amma gwamnatin ƙasar ta musanta wannan zargi.

  3. Trump ya sha alwashin lafta haraji kan ƙasashen da ke kare Greenland

    Shugaban Amurka Donald Trump ya sha alwashin aiwatar da barazanar da ya yi na lafta ƙarin haraji kan ƙasashen Turai da ke adawa da buƙatarsa ta karɓe ikon yankin Greenland.

    Ana sa ran shugabannin Turai za su tafka muhawara kan makomar yankin Greenland a wajen taron tattalin arzikin duniya da ke gudana a birnin Davos na Switzerland, duk da barazanar shugaban Amurka a kai.

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da shugabar hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, za su fara gabatar da jawabai a yau Talata, kwana ɗaya kafin isowar shugaba Trump Switzerland, inda taron ke gudana.

    Ƙasashen Turai sun bayyana aniyarsu ta haɗa kai domin fuskantar shugaban Amurka, inda suka sha alwashin mayar da martani kan duk wani yunƙurinsa na lafta musu ƙarin haraji.

    A jiya Litinin, shugaban Amurka ya ce a shirye yake ya sanya ƙarin haraji kan ƙasashen Turai da ke adawa da yunƙurinsa na mayar da Greenland a matsayin wani yanki na Amurka.

  4. Yadda za ku kare iyalanku daga kisan da ake yi wa mutane a gidajensu

    Batun kisan da aka yi wa wata mata tare da ƴaƴanta shida a jihar Kano na ci gaba da razana al'ummar ciki da wajen jihar.

    Wasu matasa ne dai ɗauke da makamai suka kutsa gidan matar da ke unguwar Dorayi Charanci da tsakar rana inda suka halaka ta tare da duka ƴaƴanta nata.

    Lamarin na zuwa ne ƙasa da watanni bayan da wasu matasan suka shiga wani gida a unguwar Tudun Yola da ke birnin na Kano suka kuma kashe matan gidan biyu tare da ƙona gawarwakinsu.

    Waɗannan kashe-kashe sun tayar da hankula tare da ƙara jefa tsoro da fargaba a zukatan al'ummar jihar - waɗanda ke ganin rayuwarsu na cikin barazana.

    Kan haka ne masana tsaro ke ci gaba da bayar da shawarwari na matakan da ya suka mutane su ɗauka domin kauce wa wannan matsala.

  5. Abin da muka sani kan 'sace mutum 160' a Kaduna

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce babu gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa na garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

    Rundunar ta ce wasu marasa kishi ne ke yaɗa wannan labari da nufin tayar da hankalin jama'a.

    A ranar Litinin jaridun Najeriya da dama sun bayar da rahoton sace mutane fiye da 100 a wuraren ibadah daban-daban na ƙauyen Kurmin Wali, inda suka ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 18 ga watan Janairu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya CAN, reshen jihar Kaduna Reberan Joseph John Hayab ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, in da ya ce: "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163,"

    Amma rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce har yanzu babu wasu bayanai da suka tabbatar da cewar an ɗauke mutanen.

  6. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.