Abin da muka sani kan 'sace mutum 160' a Kaduna

Lokacin karatu: Minti 3

Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce babu gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa na garkuwa da sama da mutane 160 a wasu coci-coci da ke ƙauyen Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

Hakan na zuwa ne bayan bayanai sun fita a ranar Litinin cewa wasu mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170, a yankin, mai fama da matsalar tsaro.

A ranar Litinin, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan'azumi ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun je ƙauyen ne a ranar Lahadi, inda suka sace mutane sama da 160.

"Sun zo ranar Lahadi wurin karfe 9, lokacin muna coci, suka bazu a garin, suka sa mu a tsakiya.

"Waɗanda suke a hannunsu yanzu 166," in ji Ɗan'azumi.

Haka nan ma shugaban ƙungiyar CAN a arewacin Najeriya Jospeh Hayab ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai batun sace mutunan a ranar ta Litinin.

Ya ce, "duk da cewa ban cika son ambata adadi ba, amma bayanan da na samu daga yankin na nuna cewa ƴanbindiga sun sace kusan mutum 172, amma guda 9 sun tsere sun koma gida, amma har yanzu ana neman mutum 163," in ji shi.

Sai dai daga bisani, BBC ta sake tuntuɓar shi da yamma, amma ya ce ba zai ce komai ba, sai dai ya ce abinda ya faɗa wa manema labarai gaskiya ne.

Ba a sace mutane a Kajuru ba - Ƴansanda

Sai dai a yammacin ranar ta Litinin rundunar ƴansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta musanata batun garkuwa da mutanen a Kajuru.

Rundunar yansandan ta ce a iyakar binciken da ta gudunar a garin da tuntuɓar shugaban ƙaramar hukumar yankin, babu ƙamshin gaskiya a batun.

Mai magana da yawun rundunar a jihar Kaduna DSP Mansir Hassan ya shaida wa BBC cewa tun bayan samun labarin, kwamishinan ƴansandan jihar CP Rabiu Muhammad ya bayar da umarnin gaggauta kai ɗauki a wajen da aka ce lamarin ya faru.

Ya ce ''Bayan zuwan da DPO ya yi, daga baya jami'anmu suka ƙara zuwa tare da shugaban ƙaramar hukumar da hukumomin tsaro, kama daga soja da ƴan sa kai. Aka je wannan waje aka yi tambayoyi.''

''Har zuwa yanzu ba mu samu wani abu da zai yi nuni da cewa wannan satar mutane da aka ce ya tabbata ba,'' in ji DSP Hassan.

Ko da BBC ta ja hankalin kakakin rundunar ƴansandan kan cewa sarkin yankin ya tabbatar da cewa akwai mutanen da aka sace, sai ya ce ''E to, ka ga mu dai mun je kuma mun samu shi wannan sarkin, mun je har waɗannan coci-coci da aka ce an kai wannan hari amma ba mu samu wani bayani da zai gamsar da mu cewa wannan abu ya faru ba.''

Sai dai kakakin rundunar ƴansandan ya amsa cewa dama can yankin yana fama da ƙalubalen tsaro, amma ya jaddada matsayar su cewa rahoton satar mutanen ba gaskiya ba ne.

''Idan an ɗauki yaran nan su waye iyayensu? idan an ɗauki waɗannan mutanen su waye ƴan'uwansu? Idan an ɗauki waɗannan mutanen ina sunansu? Babu yadda za a ce a ɗauki mutum tsawon kusan sa'a 40 amma har zuwa yanzu ba mu samu amsar waɗannan tambayoyi da muke ba.'' in ji DSP Mansir Hassan.

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce ƙofarta a buɗe ta ke ga duk wanda ke da bayani game da lamarin domin gabatar da hujjoji da za su taimaka wajen gudanar da aikin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar jama'a.

Kaduna na cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro, musamman ayyukan ƴanbindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma masu kai hare-hare tare da kashe mutane a ƙauyuka.

Ko a shekara ta 2024 wasu ƴan bindiga sun shiga yankin na Kajuru inda suka sace gwamman mutane.

Haka nana a watan Maris ɗin shekarar ta 2024 'yan bindiga suka tasa keyar dalibai kusan 300 daga wata makarantar firamare da sakandare a jihar ta Kaduna.

Daga bisani gwamnatin jihar ta sanar cewa dalibai 28 daga cikin wadanda 'yan bindigar suka sace sun tsere daga hannunsu.

Sai dai a ranar Lahadi 24 ga watan Mayu gwamnatin jihar ta sanar da kuɓutar da ɗaliban, makonni biyu bayan sace su.