Ɗan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya ce shawarar da ɗansa Abba Atiku Abubakar ya yanke na barin jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki mataki ne na ƙashin kansa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Atiku ya ce a tsarin dimokuraɗiyya irin waɗannan lamuran ba sabon abu ba ne, ko da kuwa siyasa ta haɗu da alaƙar iyali.
Atiku ya ƙara da cewa "A matsayi na na ɗan dimokiraɗiyya, ba na tilasta wa ’ya’yan na ra’ayi a kan abubuwa da suka shafi irin wannan lamarin haka kuma bazan tilasta wa ’yan Najeriya ba."
Atiku ya jaddada cewa ra’ayin ɗansa ba zai sa shi canza manufarsa wajen aiki domin kawo ingantacciyar shugabanci ba.
Abba Atiku dai ya sanar da barinsa PDP zuwa APC a ranar Alhamis, yayin wata ziyara da ya kai ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ƙasa, Sanata Barau Jibril.
A jawabin nasa, Abba ya bayyana cewa dalilin sauya sheƙarsa shi ne sha’awarsa ga salon shugabanci da jajircewar Sanata Barau.
Abba Atiku ya ce zai yi aiki tare da Sanata Barau domin ganin an sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
“Don haka zan yi aiki da Sanata Barau domin tabbatar da nasarar sake zaɓen Shugaba Tinubu a karo na biyu,” in ji shi, kamar yadda Sanata Barau ya wallafa a shafinsa na X.
Atiku ya kuma ce abin da ya fi damunsa shi ne rashin kyakkyawan shugabanci na APC da kuma matsin tattalin arziki da zamantakewa da jam’iyyar ta jefa ’yan Najeriya a ciki inda ya ce zai ci gaba da aiki tare da masu kishin ƙasa domin samar da ingantacciyar shugabanci ga al’umma.