Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne hukuncin wanda ya shiga azumi da ramuwar bara?
A yayin da aka shiga watan Sha’aban, wanda daga shi sai Ramadana, mai tsarki da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Musulunci, al’ummar Musulmin na shirye-shiryen zuwan watan, wanda a cikinsa ake kara azama wurin ibada.
Daga cikin shirye-shiryen da ake yi akwai ramakon bashin azumi na watan Ramadan na bara, ga waɗanda suka sha azumin kuma ba su samu damar ramawa ba tun tuni.
Azumi daya ne daga cikin ginshikan addinin Musulunci biyar, wanda hakan ya sa ibadar ta zama wajibi ga dukkan musulmin da ya cika sharuɗan aiwatar da ita..
A duk lokacin da azumin Ramadan ya zagayo haka, ana samun tambayoyi kan ramakon azumi, da abin da wanda ya kasa yin ramakon zai yi da sauran abubuwa da suka shafi watan.
Wannan ya sa muka tuntuɓi Sheikh Idris Yunus, limami kuma malamin da ke bayar da karatu a Masallacin da ke Wuse Zone 6 a babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce akwai matakan da ake dubawa game da ramakon azumi.
Ramako azumin baya
Shehin malamin ya ce "Allah ne ya umarci wanda yake da iko wato yake da lafiya sannan mazaunin gida ba matafiyi ba ya yi azumi. Shi ma matafiyin wajibi ne bayan ya koma gida ya rama bayan watan na Ramadan."
Malamin ya ƙara da cewa, "Idan mutum Allah ya ɗaura masa rashin lafiya, ko kuma yana cikin halin tafiya a cikin lokacin na azumi, to wannan Allah ya masa umarni ko kuma rangwamen da zai iya ajiye, sai ya rama a wasu lokutan bayan watan."
Sheikh Idris ya ce ba a iyakance lokacin ramakon ba, "sai dai akwai a cikin maganganun sahabbai da aikin da aka samu daga wajen Manzon Allah (SAW) cewa ana ramako ne kafin wani watan azumin ya shiga."
Ya ƙara da cewa akwai hadisin da ke nuna cewa matar Manzon Allah, Aisha (RTA) takan shagaltu da wasu ayyuka har ba ta samun damar rama azumin Ramadan sai a watan Sha'aban. Wato watan da ke dab da Ramadan.
Malamin ya ce idan aka samu sakaci mutum bai rama azumin ba, har wani watan azumin ya shigo, "malamai sun haɗu a kan cewa zai yi azumin watan Ramadan ɗin da ake ciki ne, ya bar wancan wanda yake kansa, ya sake zama ramako ke nan kuma."
Malamin ya hakaito daga mazhabobi, inda ya ce irin su Malikiyya da Shafi'iyya da sauran su, sun tafi a kan cewa irin wannan wanda sakaci ne ya hana shi ramakon, har wani watan na azumi ya shigo, to zai yi abubuwa uku ne kamar haka:
- Zai rama azumin
- Zai nemi tubar Allah saboda ya yi saɓo
- Zai ciyar
Malamin ya ce ba a samu fatawa kai-tsaye daga Manzon Allah ba, amma ya zo a aikin sahabbai, wanda ya ce ba a samu saɓani a ciki ba.
"Daga cikin sahabban da suka haɗu a wannan matsayar akwai Abdullahi bn Abbas da Abdullahi bn Umar da Abu Huraira da sauran su."
Sai dai malamin ya ƙara da cewa duk wanda yake da uzuri sahihi da ya hana shi rama azumin, "wanda wannan uzurin ne ya hana shi samun damar ramakon, har wani azumin ya zo, to wannan ramako kawai zai yi, babu istigfari kuma babu ciyarwa."
Sai dai ya ce akwai mazhabar Abu Hanifah da ke ganin ramakon kawai na isarwa ba tare da ciyarwa ba.
Ciyarwa maimakon azumi
A game da batun mutum ya ciyar maimakon ramako, malamin ya ce ba yadda ake tunani ba ne.
"Sahabi Abdullahi bn Abbas ne ya fassara ayar da take magana a kan zaɓin azumi ko ciyarwa. Asali akwai zaɓi, kafin daga bisani aka wajabta azumin Ramadan, aka soke hukuncin farko. Shi ne sai shi ya mayar da hukuncin kan tsofaffi."
Malamin ya ce hukuncin na kan waɗanda suke da abin da ya kira cutar da ba ta warkewa ne ke da wannan damar.
"Tsufa ita ce cutar da ba ta warkewa. Don haka idan mutum ya tsufa, to shari'a ta amince masa ya ciyar a madadin ramako."
Malamin ya ce game da masu shayarwa da masu ciki, ya ce "magana mafi inganci ita ce su ma an musu rangwame ne irin na matafiya. Wato ke nan bayan haihuwa da shayarwa su rama."