Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 21/01/2026

Wannan shafi ne da kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 21 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Mutum 39 sun mutu a Khartoum na Sudan sakamakon zazzaɓin Denge

    Likitoci a Sudan na ƙoƙarin yaƙi da yaɗuwar zazzaɓin Denge wanda sauro ke yaɗawa.

    A Khartoum, cutar ta kashe mutum 39 yayin da wasu ɗaruruwa suka kamu da ita.

    Asibitocin birnin da dama ba su aiki saboda yadda yaƙi tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan RSF ya ɗaiɗaita su.

    Ƙungiyar likitocin ƙasar ta ce mata da ƙananan yara na cikin waɗanda suka fi kamuwa da zazzaɓin na Denge a ƙasar.

  2. An yi jana'izar babban limamin Ilorin Imam Muhammad Bashir

    An gudanar da jana’izar marigayi Limamin Ilorin, Sheikh Muhammad Bashir Solih, wanda ya rasu a ranar Litinin, a unguwar Egbejila da ke jihar.

    Abin da ya fi ɗaukar hankali a jana’izar shi ne cewa an binne gawarsa a cikin wani ɗaki a gidansa.

    Bayan rasuwarsa, an kai gawarsa zuwa Muhammad Soliu Islamic Center, Egbejila, Ilorin, inda aka binne shi a gidansa na asali.

    Kafin jana’izar, mutane da dama sun taru a fadar Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, domin yin addu’o’i na ƙarshe da girmamawa ga marigayin.

    Limami Sheikh Abdullahi Abdulhameed ne ya jagoranci sallar jana’izar.

    An binne shi da misalin karfe 12 na rana yayin da kuma mutane suka je bakin kabarinsa suna masa addu’a.

    Jana’izar ta samu halartar dimbin mutane.

    An haifi marigayin a ranar 7 ga Yuli, 1951, kuma a ranar 15 ga Oktoba, 1983, aka naɗa shi limami na goma sha biyu na Ilorin.

  3. Sifaniya ta dakatar da jigilar jiragen ƙasa a Catalonia bayan mummunan hatsari

    Hukumomi a Sifaniya sun dakatar da duk wata jigilar jiragen ƙasa a yankin Catalonia, bayan mummunan hatsarin da ya sake aukuwa a jiya Talata.

    Hatsarin shi ne na biyu a cikin kwanaki uku a ƙasar, kuma hukumomi sun yi amanna cewa rashin yanayi mai kyau ke haifar da shi.

    Mutum 37 ne suka samu rauni, huɗu daga cikin su kuma suna cikin mawuyacin hali, yayin da direban jirgin ya mutu.

    Yankin Catalonia na cikin wuraren da gurɓatar yanayi ta yi ƙamari a Sifaniya a ƴan kwanakin nan.

  4. Trump na kan hanyar zuwa Switzerland bayan samun matsalar jirgi

    Shugaba Donald Trump na kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Switzerland domin halartar taron ƙoli na tattalin arziƙin duniya da ke gudana a birnin Davos, bayan ya samu jinkiri sakamakon wata matsala da ta taso a na’urar jirginsa na Air Force One.

    Lamarin ya saka Trump hawa wani jirgi na daban domin kammala tafiyarsa zuwa Davos.

    A bana, taron ya fi karkata ga muhawara kan ƙoƙarin shugaba Trump na ganin yankin Greenland ya koma wani ɓangare na Amurka, matakin da shugabannin Turai ke nuna adawa da shi.

    Yayin ganawarsa da manema labarai, an tambayi shugaba Trump game da shirinsa a kan Greenland, inda ya kaɗa baki ya ce: “Za ku sani nan gaba kaɗan.”

    A jiya Talata ne shugabannin Turai da ke halartar taron Davos suka sake jaddada matsayinsu na adawa da wannan buri na Amurka.

    Sai dai Trump ya nace cewa haɗa Greenland da Amurka zai taimaka wajen ƙarfafa tsaron ƙasashen yammacin duniya.

  5. An yanke wa mutumin da ya harbe tsohon firaiministan Japan ɗaurin rai-da-rai

    Wata kotu a Japan ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai kan Tesuya Yamagami, mutumin da ya harbi tsohon firaiministan ƙasar Shinzo Abe a wajen wani gangamin siyasa kusan shekaru huɗu da suka gabata.

    Yamagami ya amsa laifin yunƙurin kisan kai a watan Oktoban bara, lokacin da aka fara shari'ar, amma ya musanta wasu zarge-zargen da aka yi masa.

    Tsohon firaiminstan ya mutu bayan harbin da aka yi masa yana tsakiyar jawabi a lokacin taron.

    Masu gabatar da ƙara sun ce Yamagami ya daɗe yana riƙe da tsananin ƙiyayyar tsohon firaiministan, lamarin da ya sa ya harbe shi.

  6. Yadda ƴansanda suka yi amai suka lashe kan sace mutane a Kaduna

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta sanar da sauya matsayar da ta ɗauka a baya cewa ba a sace mutane ba a garin Kurmin Wali na ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, inda a yanzu rundunar ta tabbatar da garkuwa da mutanen.

    A ranar Litinin aka fara samun rahotannin cewa wasu mahara sun shiga ƙauyen na Kurmin Wali tare da sace mutane kimanin 170 a yankin mai fama da matsalar tsaro.

    Amma a ranar Litinin ɗin, sarkin Kurmin Wali, Ishaku Dan'azumi ya tabbatar wa BBC cewa maharan sun je ƙauyen ne a ranar Lahadi, inda suka sace mutane sama da 160.

    "Sun zo ranar Lahadi wurin karfe 9, lokacin muna coci, suka bazu a garin, suka sa mu a tsakiya.

    "Waɗanda suke a hannunsu yanzu 166," in ji Ɗan'azumi.

    Shi ma shugaban ƙungiyar CAN a arewacin Najeriya Jospeh Hayab ya tabbatar wa kafafen yaɗa labarai batun sace mutunan a ranar ta Litinin.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.