Mece ce makomar NNPP bayan ficewar Gwamna Abba Kabir?

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a hukumance, wadda a karkashinta ne aka zabe shi a matsayin gwamna.

Gwamnan - wanda ɗaya ne daga cikin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da tsohon gwamnan jihar Rabi'u kwankwaso ya assasa - ya ce ya fice daga NNPP ne saboda rikicin cikin-gida da ya dabaibaye jam'iyyar, wanda a cewarsa ya fita ne domin fifita buƙatun al'ummar Kano.

A shekarar 2023 ne aka zaɓi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar Kano ƙarƙahsin Jam'iyyar NNPP bayan da ya kayar da babban abokin hamayyarsa Nasiru Yusuf Garo na jam'iyyar APC mai mulkin jihar a lokacin.

Dama an kwana biyu ana rade-radin fitar gwamnan daga jam’iyyar tasa, lamarin da ya haifar da rudani a lamurran siyasar jihar.

Ficewar Gwamna Abba daga NNPP na nufin cewa ya raba gari da tafiyar Kwankwasiyya ta ubangidan siyasarsa.

Ana tunanin gwamnan zai tafi da manyan jiga-jigan gwamnatin, waɗanda su ma ƙusoshi ne a tafiyar Kwankwasiyyar.

Wannan ne ya sa mutane da dama ke tambayar ina makomar tafiyar Kwankwasiyyar a jihar, wadda siyasarta ke ɗaukar hankali a Najeriya.

Giɓi a Kwankwasiyya

Kabiru Sufi, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya ce tafiyar Kwankwasiyya ta yi babban rashi.

"A halin yanzu Kwankwasiyya da ma jam'iyyar NNPP a gwamnatance ta rasa jiha guda ɗaya da take tunƙaho da ita," in ji shi a lokacin da yake nuna irin giɓin da tafiyar ta samu.

Masanin harkokin siyasar ya ƙara da cewa giɓin ya ƙara faɗi ne kasancewar ba gwamnan ba ne kaɗai zai fice daga jam'iyyar.

"Akwai muƙarrabansa da ƴan majalisa na tarayya da na jiha da dama da za su bi shi, waɗanda kuma duk ƴan jam'iyyar da tafiyar ne. Kasancewar masu riƙe da madafun iko a jam'iyya na taimaka mata sosai."

Sai dai Sufi ya ce an san Kwankwasiyya da ƙoƙari da juriyar hamayya, "amma duk da haka, samun masu riƙe da mulki suna taimakawa wajen ciyar da tafiyar da harkokinta domin ƙara mata tagomashi."

Masanin ya ce za a samu matsala wajen tantancewa ne kasancewar Kwankwaso ya bai wa magoya bayansa izinin cewa za su iya tafiya tare da gwamnati.

"Wannan sanarwar ta Kwankwaso za ta haifar da ruɗani, inda za a yi wahalar tantance waɗanda suka fice da gaske da kuma waɗanda suka bi umarnin Kwankwaso wajen bin gwamnan."

Me ya kamata Kwankwaso ya yi?

Sai dai duk da ficewar gwamnan, da kuma wasu jiga-jigan jam'iyyar da ake tunanin za su fita, masanin ya ce tafiyar Kwankwasiyya za ta iya tsayawa da ƙarfinta idan jagororinta sun yi abin da ya dace.

"Makomarta za ta danganta ne da irin matakin da jagororinta, musamman ma shi Kwankwaso ya ɗauka musamman a ɓangaren fitar da sabon shugabancin tafiyar," in ji shi.

Sufi ya ce idan aka yi gaggawar fitar da sabon tsari, suka kuma ɗora daga inda aka tsaya, za a samu sauƙin matsala.

"Idan ba a tsaya jimami mai tsawo ba, aka ɗauki mataki cikin sauri domin cigaba da harkoki, to wataƙila raunin ba zai zama mai yawa ba. Amma idan aka yi jinkiri, aka tsaya jan ƙafa, lallai lamarin zai taɓa tafiyar sosai," in ji shi.

Darewar Kwankwasiyya

A watan Disamban shekarar 2025 ne dai aka fara maganar cewa Gwamna Abba Kabir zai bar uban gidansa na siyasa, Rabiu Musa Kwanwaso domin komawa APC.

Ana cikin muhawara kan batun rahotanni suka bayyana cewa mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam ba zai bi gwamnan ba, lamarin da ya ƙara fito da alamar ɓarakar fili.

A yanzu dai gwamna Abba ya fice daga jam'iyyar ta NNPP, kuma tuni lamarin ya haifar da ruɗanin siyasa a jihar, inda a cikin Kwansiyya yanzu aka samu waɗanda ake kira da "a ci daɗi lafiya" domin kwatanta masu bin gwamna, da kuma "ƴan wahala ba ta kisa" domin kwatanta masu bin Kwankwaso.

A halin yanzu za a iya cewa kai ya rabu sannan mabiya na cikin ruɗu dangane da wane ɓangaren za su bi, Abba ko Kwankwaso?

Rikicin ya ƙarra ta'azzara ne a jam'iyyar NNPP a mazaɓar Gargari da ke ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta sanar da korar Hashim Dungurawa daga jam'iyyar, duk da cewa na hannun daman Rabiu Kwankwaso ne kuma shugaban jam'iyyar a jiha.

Sai dai ba a daɗe ba da wannan matakin uwar jam'iyyar ta sanar da rushe shugabancin jam'iyyar a jihar baki ɗaya.