Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da hukumar ICE a Minnesota

    Daruruwan ƴan kasuwa a jihar Minnesota sun rufe shagunansu ranar Juma'a kuma dubban masu zanga-zangar sun fito cikin tsananin sanyi don nuna adawa da ayyukan samame da hukumar shige-da fice ta Amurka (ICE) ke ci gaba da gudanarwa a jihar.

    Zanga-zangar ta ƙara zafi ne bayan masu shiryata sun ƙarfafa wa mazauna yankin gwiwa da su daina aiki ko makaranta domin su fito nuna adawa da hukumar ta ICE.

    Hukumar ICE dai ta shafe sama da makonni shida ta na gudanar da samame a jihar Minnesota a ƙarƙashin umarnin gwamnatin Donald Trump.

    Hukumar ta bayyana aikin a matsayin wani mataki na kare lafiyar jama'a da nufin korar masu aikata laifuka da suka shigo ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    Masu sukar wannan mataki sun yi iƙirarin cewa abin na sahfar ƴan cirani da ba su da wani laifi kuma ana hadawa da wasu ƴan Amurka ma yayin samamen.

    An tura dubban jami'an tsaro na tarayya zuwa Minnesota a matsayin wani ɓangare na aikin da aka yi wa laƙabi da "Operation Metro Surge".

  2. Kotu ta fara zaman yanke hukunci a shari'ar jagoran adawa a Afrika ta kudu

    Dubban magoya bayan ɗan siyasar Afirka ta Kudu Julius Malema ne suka hallara a gaban wata kotu a ranar Juma'a a daidai lokacin da kotun ta fara zaman sauraron bayanai gabanin yanke hukunci a shri'ar da ke masa bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba.

    Julius Malema, wanda ya shahara saboda irin nau'in siyasarsa, yana iya rasa kujerarsa a majalisar dokokin ƙasar idan har kotu ta yanke masa hukuncin ɗauri na fiye da watanni goma sha biyu.

    A watan Oktoban da ya gabata ne dai aka same shi da laifin harba bindiga bisa ka'ida ba yayin bikin cika shekaru biyar na EFF a shekarar 2018.

    Hukunci mafi tsauri da kotu za ta iya yanke masa shi ne zaman gidan yari na tsawon shekara 15.

  3. Malami ya zargi DSS da yi wa shari’arsa zagon ƙasa

    Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da wasu ayyuka da ya ce suna da nufin tauye masa haƙƙinsa na samun adalci a shari'ar da ake yi masa.

    A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka ya sanya wa hannu, Malami ya ce ana ci gaba da hana shi ganawa da lauyoyinsa lamarin da ke kawo masa cikas wurin kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa

    Ya bayyana abin da hukumar ta DSS ke yi a matsayin wani mataki na yi wa doka zagon ƙasa.

    Sanarwar ta ce "Waɗannan jerin abubuwan da ke faruwa suna nuni ne da wani tsari na kama mutum kafin ma a gudanar da bincike, inda ake neman tattara shaida bayan tsarewa, matakin da ya saɓa wa doka da kuma ƴancin da tsarin mulki ya ba shi," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa, kama shi da aka yi ya zo ne a daidai lokacin da ya ke buƙatar ya kare kansa a shari’arsa da hukumar EFCC gaban babbar kotun tarayya.

    Malami ya ƙara jaddada aniyarsa na kare kansa a gaban kotu.

  4. NNPP ta mayar wa Abba Kabir martani kan ficewa daga jam’iyyar

    Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam'iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.

    A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, jam’iyyar ta ce matakin da Gwamna Yusuf ya ɗauka tamkar cin amanar al’ummar jihar Kano ne, wanɗanda a cewarta, sun kaɗa masa ƙuri’a ne sakamakon daɗewar da ya yi yana tare da tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

    ''Muna matuƙar takaicin yadda Gwamna Abba, mutumin da al’ummar Jihar Kano suka damka wa al’ummar Jihar kan karfin biyayya da sadaukarwar da ya yi na tsawon shekaru da dama da ya yi wa tafiyar Kwankwasiyya, a yanzu ya zaɓii ya ci amanar da aka miƙa masa.'' in ji sanarwar

    Ta kuma ƙara da cewa ''Wannan mataki na iya mayar da jihar hannun waɗanda suka daɗe suna adawa da ci gabanta da muradun al’ummarta.''

    Jam’iyyar NNPP ta buƙaci magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, su kuma yi taka-tsan-tsan kan duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma a siyasance ko kuma ta da zaune tsaye.

  5. Rasha ta kai hari kan Ukraine yayin da tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin ke gudana

    Rasha ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Ukraine cikin dare, inda ta kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu 23 duk da cewa ta shiga tattaunawa da Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

    Magajin garin Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine ya ce mutum ɗaya ya mutu, huɗu kuma sun jikkata sakamakon wani ƙazamin harin da Rasha ta kai, yayin da magajin garin Kharkiv ya ba da rahoton cewa mutane 19 ne suka jikkata a wani hari da aka kai a birnin.

    Tawagogin Rasha da Ukraine da Amurka sun yi taro a Abu Dhabi a tattaunawar farko ta ɓangarorin uku tun bayan da Kremlin ta ƙaddamar da mamaye makwabciyarta a shekarar 2022.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa an samu ci gaba a tattaunawar amma har yanzu ba a warware muhimmin batu da ya shafi mallakar yankuna ba.

    Rasha ta mamaye kusan kashi 20% na yankunan Ukraine, gami da sassan yankin gabashin Donbas.

    Kremlin na son ta cib gaba da riƙe wadannan yankuna har ma da ƙarin wasu, amma Ukraine ta dage kan cewa hakan ba zai yiwu ba.

  6. Manoman Zimbabwe sun nemi taimakon Trump wurin karɓar diyya daga gwamnatin ƙasarsu

    Tsofaffin manoma fararen fata na Zimbabwe suna neman gwamnatin Amurka ta taimaka musu domin samun diyya daga gwamnatin ƙasar kan gonakin da aka ƙwace a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasar Robert Mugabe.

    Wata ƙaramar ƙungiyar manoma ta tabbatar da cewa ta rubutawa wani kamfani da ke da alaƙa da Shugaba Trump wasiƙa domin ya matsawa Washington lamba don neman a gaggauta biyansu diyyar fiye da dala biliyan uku da suke bin gwamnatin Zimbabwe.

    Wakilin ƙungiyar manoma Bud Whitaker ya shaida wa BBC cewa da yawa daga cikin mambobin yanzu sun tsufa kuma suna neman masu sayen hannayen jari da suka samu daga gwamnati a matsayin diyya.

    Gwamnatin Zimbabwe ta ƙwace gonakin fararen fata sama da dubu huɗu, daga shekara ta 2000 a matsayin wani ɓangare na manufofin gyara abubuwan da suka faru a zamanin mulkin mallaka.

  7. Shugaban Ivory Coast ya ƙaddamar da sabuwar majalisar ministoci

    Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya sanar da sabuwar majalisar ministocin ƙasar inda babu wasu manyan sauye-sauye baya ga ficewa daga gwamnatin ministan noma Kobenan Kouassi Adjoumani, wanda ke da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da shugaba Ouattara.

    Téné Birahima Ouattara, ɗan'uwan Shugaba Alassane Ouattara, wanda a baya shi ne ministan tsaro, ya zama mataimakin firaminista gami da matsayinsa na baya.

    Robert Beugré Mambé, mai shekaru 72, wanda aka sake naɗawa a matsayin Firaministan Ivory Coast a farkon wannan makon, ya jaddada cewa sabuwar majalisar za ta ba da fifiko kan muradun jama'a da hadin kan ƙasa da kuma ci gaban tattalin arziki.

    Sabuwar majalisar ministocin ƙasar za ta iya dogaro da goyon bayan sabuwar majalisar dokokin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Patrick Achi, tsohon firaminista.

    Jam'iyya mai mulki, Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP), ita ke riƙe da sama da kashi 75% na kujerun majalisar dokokin.

  8. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da mu ke wallafawa.