Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan dokokin zaɓen da ake son yi wa gyara a Najeriya kafin 2027
Ƴan Najeriya na ci gaba da ta tsokaci kan wasu gyare-gyaren dokar zaɓe da ke jiran amincewar majalisar dokokin ƙasar.
Inda ma wasu ke sukar majalisar da jan ƙafa wajen amincewa da sabbin gyare-gyaren.
Daga cikin masu sukar har da jagoran adawar ƙasar, Atiku Abubakar, wanda ya zargi majalisar dattawa da “jan ƙafa da gangan, kan aikin gyaran dokar zaɓe” ta 2022.
Atiku Abubakar ya yi gargaɗin cewa ci gaba da jinkirin aikin gyaran dokar zaɓen zai iya shafar ingancin babban zaɓen kasar na shekarar 2027.
Wani saƙo da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya wallafa a shafinsa na X ya ce sassan da ke buƙatar gyara a dokar zaɓen ƙasar ta 2022, su ne ke hana masu ƙorafi kan sakamakon zaɓe damar iya kare abubuwan da suke ƙalubalanta a gaban kotu.
Dokar zaɓen ta 2022 da aka sanya wa hannu a cikin watan Feburerun 2022 ita ce ake amfani da ita wajen gudanar da zaɓuka yanzu haka a Najeriya.
Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la'akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023.
Wasu daga cikin gyare-gyaren da ake son yi
Akwai gyare-gyaren fuska da dama da aka yi wa dokokin zaɓen na 2022, domin inganta ayyukan hukumar INEC da jam'iyyu da kuma ƴantakara.
Cikin wannan muƙala mun duba wasu daga cikin muhimman gyare-gyaren fuskar da aka yi wa dokar zaɓen.
'Tilasta' bai wa INEC kuɗin zaɓe da wuri
Dokar zaɓen 2022 ta yi tanadin cewa gwamnati ta bai wa hukumar zaɓe kuɗin gudanar da zbuka aƙalla shekara guda kafin ranar zaɓe.
To amma sabuwar dokar ta yi tanadin cewa ''dole'' ne gwamnati ta yi hakan shekara guda kafin ranar zaɓen.
Dokar ta ce hakan zai taimaka wa INEC kammala shirye-shiryenta a kan lokaci tare da magance ƙorafe-ƙorafen da ke tasowa gabanin zaɓukan, musamman kan kammala shirye-shirye zaɓen.
A baya jam'iyyun siyasa sun sha ƙorafi kan rashin gudanar da wasu ayyukan INEC a kan lokaci gabanin zaɓe.
Bai wa fursunoni damar yin zaɓe
A karon farko a tarihin Najeriya, dokar na son bai wa ɗaurarru da fursunoni dmar kaɗa ƙuri'unsu a lokacin zaɓe.
Sabon ƙudurin ya yi tanadin bayar da damar yi wa ɗaurarrun rajistar zaɓe domin su zaɓi wanda suke so.
Hukunci mai tsauri ga masu maguɗin zaɓe
Sabuwar dokar ta tanadi hukunci mai tsauri ga waɗanda aka samu da laifin maguɗin zaɓe.
Haka kuma ta buƙaci a mayar da sayen ƙuri'a a matsayin babban laifin da za a tanadar masa tarar miliyan biyar ga wanda aka kama yana aikatawa.
A baya dai dokar zaɓe ta tanadi tarar naira 500,000 da ɗaurin shekara biyu, da kuma haramta wa mutum tsayawa takara na tsawon shekara 10.
Dokar ta kuma yi tanadin cewa duk wanda aka samu da laifin bayar da cin hanci na kuɗi ko wani abu domin jan ra'ayin daliget a lokacin zaɓen fitar da gwani ko mai kaɗa ƙuri'a a lokacin zaɓen gama-gari zai fuskanci hukuncin ɗaurin aƙalla shekara biyu a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba.
Soke takarar saboda ƙarya
Sabuwar dokar ta kuma yi tanadin cewa idan ɗan takara ya gabatar da bayanan ƙarya game da kansa , kuma kotu ta gano cewa karya ya yi, kotun za ta soke takararsa da kuma jam'iyyar da ya tsaya takarar.
''Duka jam'iyyar da ta tsayar da ɗan takarar da bai cancanta za ta fuskanci tarar aƙalla naira miliyan 10'', kamar yadda sabuwar dokar ta nuna.
Tantance alamomin jam'iyyu da sunaye a kan lokaci
Sabuwar dokar ta kuma yi tanadin cewa dole ne INEC ta bai wa jam'iyyu aƙalla kwana 60, domin ta rubuta wa kowace jam'iyya ta gayyato su tare da ƴantakararsu domin su duba sunayensu da alamomin jam'iyyunsu ko yadda aka rubuta sunayen jam'iyyun a akan takardun zaɓe.
Haka kuma sabuwar dokar ta ce jam'iyyun na da kwana biyu domin bai wa INEC amsa kan buƙatar dubawa.
A baya an sha samun matsaloin manta sunan jam'iyyu a kan takardun zaɓe, ko rubuta sunan wata a kusa da alamar wata jam'iyyar.
A dokar 2022 kwana 20 kawai INEC ke bai wa jam'iyyu domin zuwa su duba sunayen nasu, amma a sabuwar dokar an tanadi kwana 60.
Tura sakamakon zaɓen kowace rumfa ta na'ura
A yanzu manyan jami'an zaɓe a kowace rumfa za su ''tura'' sakamakon zaɓen kowace rumfa da adadin mutanen da aka tantance, zuwa cibiyar tattara sakamakon zaɓe ta gaba ta hanyar amfani da na'ura.
Wannan zai taƙaita yawan ƙorafin da ke samu daga jam'iyyu na kai sakamakon da ba shi aka samu a matakin rumfar zaɓe ba.
Dokar zaɓen 2022 ta yi tanadin kai sakamakon zaɓen a rubuce, bayan sanya hannun wakilan jam'iyyu da sauran masu ruwa da tsaki a matakin rumfar zaɓe.
Damar INEC ta sake nazarin sakamako kan sharaɗi biyu
Sabuwar dokar ta kuma bai wa INEC damar sake nazarin sakamakon zaɓe tare da soke shi cikin kwana bakwai, amma bisa sharaɗi guda biyu.
- INEC ta samu rahoto daga jami'inta sannan ta tabbatar cewa an bayar da sakamakon ne bisa ''tursasawa''.
- Aka tabbatar da cewa an saɓa ƙa'idojin tattara sakamakon zaɓe.
A baya kotu ce ke da alhakin dubawa tare da soke sakamakon da jami'in zaɓe ya bayar.
Rajistar jam'iyyu da kuma bayanan mambobi
Sabuwar dokarf ta yi tanadin cewa naira miliyan 50 ga duk jam'iyyar da ke son samun rajista daga INEC, kuma hukumar ce ke da alhakin saka kuɗin..
Haka kuma dokar ta tanadi cewa wajibi ne kowace jam'iyya ta ajiye rajistar mambobinta a na'ura da kuma takardu, inda za a samu sunan mambobin da jinsinsu da ranar haihuwarsu da adireshinsu da jiharsu da kuma ƙaramar hukumarsu.
Sauran bayanan sun haɗa da mazaɓunsu da rumfunan zaɓensu da lambarsu ta ɗan ƙasa, NIN da kuma hotonsu.
Haka kuma dokar ta ce duk wanda ya shiga jam'iyya to a ba shi katin rajistar jam'iyya.
Kuma dole ne kowace jam'iyya ta bai wa INEC rajistar mambobinta kwana 30 kafin zaɓukan fitar da gwani ko babban zaɓe, idan kuwa ta gaza yin hakan, ba za ta iya tsayar da ɗan takara ba.
Taƙaita kuɗin da ake kashewa da na tallafi
Sabuwar dokar ta buƙaci a taƙaita abin da jam'iyyu ke kashewa wajen yaƙin neman zaɓe.
Dokar ta ƙara kuɗin da za a iya kashewa a yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa daga naira biliyan 5 zuwa naira biliyan 10.
Ga masu neman kujerar gwamnan an ƙara kuɗin da za su iya kashewa a yaƙin neman zaɓe daga nira biliyan 1 zuwa naira biliyan 3.
Kujerun ɗan majalisar dattawa kuwa an ƙara kuɗin yaƙin neman zaɓensu daga naira miliyan 100 zuiwa naira miliyan 500, sai majalisar tarayya daga naira miliyan 70 zuwa naira miliyan 250.
Yayin da aka ƙara kuɗin yaƙin neman zaɓen ɗan majalisar jiha daga naira miliyan 30 zuwa naira miliyan 100, sai shugaban ƙaramar hukumar daga naira miliyan 30 zuwa naira miliyan 60.