Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sauye-sauye biyar da INEC ke son a yi a dokokin zaɓen Najeriya
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta sabunta kira domin a yi gyara a kundin tsarin mulkin ƙasar don ɓullo da wasu sauye-sauye a tsarin zaɓen ƙasar.
Kakakin hukumar Zaɓen, Hajiya Zainab Aminu ta shaida wa BBC cewa dama hukumar ta saba ɓullo da wasu sauye-sauye a tsarin zaɓen ƙasar, kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba ta dama.
''In ba a manta ba a 2020, an yi makamancin haka, inda aka yi zama tsakanin INEC ta majalisun dattawa da wakilai, wajen yi wa dokokin zaɓen ƙasar kwaskwarima'', a cewarta.
Ta ƙara da cewa a wannan zama ne aka sabunta dokokin zaɓen na shekarar 2010, wanda aka mayar da shi dokokin zaɓe na 2022, da ake aiki da shi a yanzu a ƙasar.
Sabuwar buƙatar hukumar zaɓen ta ƙunshi yin gyare-gyare a kundin dokokin zaɓen domin fito da wasu hanyoyi a tsarin zaɓen ƙasar.
Kan haka ne muka yi nazarin sauye-sauyen biyar da hukumar ke son a ɓullo da su a yanzu.
Zaɓen wuri (Early Voting)
Ɗaya daga cikin manya-manyan sauye-sauye da hukumar zaɓen Najeriyar ke so ɓullowa da shi, shi ne zaɓen wuri.
''A wannan zaɓen ne za a bai wa masu ayyuka na musamman, kamar ma'aikatan zaɓen da jami'ar tsaro da ƴan jarida da likitoci da sauran masu muhimman ayyuka damar gudanar da zaɓensu tun kafin ranar da za a yi zaɓe'', a cewar Hajiya Zainab Aminu.
Tuni dai dama wasu ƙasashe ciki har da Ghana ke amfani da wannan tsari na zaɓen wuri domin bai wa masu muhimman ayyuka damar kaɗa ƙuri'a.
Zaɓen mazauna ƙasashen waje (Diaspora Voting)
Wani sauyin da INEC ke son ɓullo da shi a tsarin zaɓen Najeriya, shi ne bai wa ƴan ƙasar mazauna ƙetare damar kaɗa ƙuri'unsu a zaɓukan ƙasar.
''Muna so a riƙa bai wa ƴan Najeriya mazauna ƙetare damar gudanar da zaɓe'', in ji Hajiya Zainab.
Hukumar zaɓen ta ce hakan za taimaka wajen damawa da kowane ɗan Najeriya a ko'ina yake zaune a faɗin duniya.
Gyara amfani da katin zaɓe na dindindin
Cikin shirin gyare-gyaren da INEC ke son a ɓullo da shi har da batun daina taƙaita amfani da katin zaɓen na dindindin domin kaɗa ƙuri'a.
''Sabon sauyin zai buƙaci, duk wanda ke da wani katin shaida na Najeriya da INEC ta amince da shi, ya samu damar kaɗa ƙuri'arsa'', a cewar Muhammad Kuna mashawarcin shugaban INEC a lokacin da yake jawabi a zaman kwamitin zaɓe na haɗin gwiwar majalisar dokokin ƙasar .
A yanzu dai sai wanda ke da katin zaɓe na dindindin ne ke da damar kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙasar.
Mutane da dama kan yi rajistar katin zaɓensu ba tare da sun karɓa ba, ko kuma su karɓa su tafi wasu garuruwan, wani abu da ke kange su daga yin zaɓen.
Bai wa INEC damar naɗa shugabannin zaɓe na jihohi
Haka kuma hukumar na son a ba ta damar na ɗa shugabannin hukumar zaɓe na jihohi da birnin tarayya, waɗanda za su yi aiki a matsayin daraktocin hukumar.
INEC ta ce hakan zai taimaka wajen ƙarfafa mata gwiwa don gudanar da zaɓukan a matakan gwamnati uku da ake da su a Najeriya.
Samar da hukumomin sasanta rikicin zaɓe
Hukumar INEC ɗin na son kafa wasu hukumomi biyu, Hukumar kula da laifukan zaɓe , wadda za ta riƙa bincika tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifukan zaɓe.
Da kuma hukumar kula da jam'iyyun siyasa, wadda za ta riƙa kula da harkokin jam'iyyun siyasa domin tabbatar da suna biyayya ga tsarin dokokin hukumar.