Da gangan majalisa ke jan ƙafa kan gyaran dokar zaɓe - Atiku

Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma jigon hamayyar siyasar kasar, Atiku Abubakar ya zargi majalisar dattawa da jan ƙafa da gangan, kan aikin gyaran dokar zaɓe ta 2022.

Atiku Abubakar ya yi gargadi cewa ci gaba da jinkirin aikin gyaran dokar zaɓen zai iya shafar ingancin zaɓen 2027.

Dokar zaɓen ta 2022 da aka sanya wa hannu a cikin watan Feburerun 2022 ita ce ake amfani da ita wajen gudanar da zaɓuka yanzu haka a Najeriya.

Yanzu haka wannan doka tana a gaban majalisar dokokin ƙasar, inda ake nazari da muhawara a kai da nufin gyara sassan da aka gano cewa suna da matsala ta la'akari da abubuwan da suka faru a lokacin babban zaɓen Najeriya na 2023. Kuma wannan wani mataki ne na shirya fuskantar zaɓen 2027 a Najeriya.

Amma yayin da ƴan Najeriya ke jiran kammala wannan aiki a zauren majalisar, tsohon mataimakin shugaba ƙasar ya ce rashin gyaran dokar zaɓen ƙasar ne ya janyo kurakuren da aka tafka a zaɓen 2023 a Najeriya.

Wani saƙo da tsohon mataimakin shugaban Najeriyan ya wallafa a shafinsa na X ya ce sassan da ke buƙatar gyara a dokar zaɓen ƙasar ta 2022, su ne suke hana masu ƙorafi kan sakamakon zaɓe damar iya kare abubuwan da suke ƙalubalanta a gaban kotu.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, wanda ya yi wa jam'iyyar PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a Najeriya, ya yi zargin cewa da gangan majalisar dattawan ke hana a aiwatar da kundin dokar zaɓen.

A hirarsa da BBC, AbdurRashid Shehu Uba, mataimaki na musamman ga Atiku Abubakar kan kafafen yada labarai ya yi bayanin cewa "wannan a bayyane suke ga dukkan waɗanda suke bibiyar abubuwan da suke wakana wajen tabbatar da an yi gyare-gyare. Tun daga shekarar 2022, kafin zaɓen 2023 akwai muhimman gyare-gyare da ya kamata a ce ita majalisa ta mayar da hankali a kai wajen tabbatar da su, wanda har aka yi wannan zaɓe ba a yi nasarar gyara su ba."

Daga cikin sassan da aka shirye gyarawa a dokar zaɓen ta Najeriya, waɗanda Atiku Abubakar ke fatan su tabbata harda "Tura sakamakon zaɓe ta na'ura mai ƙwaƙwalwa, da kuma batun samar da kotu mai zaman kanta da za ta saurari ƙarar waɗanda suka aikata laifunkan zaɓen" in ji AbdurRashid Shehu Uba.

Ya ce a bisa nazarin su, a bayyane take cewa majalisar ba ta da aniyar kammala wannan aiki domin inganta tsarin gudanar da zaɓe a Najeriya.

Ya yi nuni da cewa idan har aka tafi a haka, to ita kanta hukumar Zaɓe ta Najeriya za ta fuskanci matsala wajen gudanar da zaɓen 2027.

Atiku ya jaddada buƙatar majalisa ta mayar da hankali wajen kammala aikin gyaran dokokin zaɓen domin kaucewa duk wani abu da zai kawo nakasu ga zaɓukan Najeriya, musamman zaɓen 2027 da ke ƙaratowa.