Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyoyin Saudiyya na son Salah da Vinicius, Man U na shirin tattaunawa da Mainoo
Dan wasan gaban Liverpool da Masar Mohamed Salah, mai shekara 33, da dan wasan Real Madrid da Brazil Vinicius Jr, mai shekara 25, za su kasance manyan 'yan wasa biyu da kungiyoyin Saudiyya ke zawarcinsu a bana.(Telegraph - subscription required)
A wani labarin kuma kungiyoyin Saudiyyan sun yi ammanar cewa ,Salah zai bar Liverpool a wannan bazara . (i Paper - subscription required)
Golan Tottenham da kuma Italiya Guglielmo Vicario, mai shekara 29, na jan hankalin Inter Milan yayin da suke shirin maye gurbin dan wasan Switzerland Yann Sommer, mai shekara 37. (Gazzetta - in Italian)
Crystal Palace ta tattauna da Wolves a kan ko za ta sayar da dan wasan gaban Norway Jorgen Strand Larsen mai shekaa 25. (Talksport)
Manchester United ta soma shirin tattaunawa da dan wasan tsakiyar Ingila Kobbie Mainoo mai shekaru 20 a duniya.(Sky Sports)
Chelsea na son a bata aron dan wasan tsakiyar Brazil, Douglas Luiz mai shekara 27 wanda a halin yanzu yana Nothingham Forest a matsayin aro daga Juventus har karshen kakar wasa (Athletic - subscription required)
Kungiyar Charlotte FC ta kasar Amurka na sha'awar dan wasan Ingila a tawagar masu shekaru kasa da 21 Harvey Elliott, mai shekara 22, wanda Liverpool ta bada shi aro ga Aston Villa . (Sky Sports)
Leeds da Sunderland za su rasa dan wasa mai kai hari na Norwich City Josh Sargent. Dan wasan Amurka mai shekara na son ya koma Major League Soccer kuma ya fi son kungiyar Toronto FC. (Teamtalk)
Arsenal na zawarcin dan wasan Corinthians Machado mai shekara 16. (Globo - in Portuguese)
Kawo yanzu Roma da wasu kungiyoyi na sha'awar dan wasan Manchester United da Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24. (Florian Plettenberg)