Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da suka kamata ka yi lokacin tashi daga bacci
Ɗaya daga cikin abubuwan da ake daɗe ana tattaunawa game da lafiyar al'umma shi ne ainihin abin da ya kamata mutum bayan ya tashi daga bacci, musamman baccin safe.
An sha samun labarin wanda ya farka daga bacci da safe, amma da zarar ya yunƙura zai tashi, sai jiri ya kwashe, inda wasu suke faɗi, lamarin da yakan jefa su cikin wata matsalar daban.
Dokta Khadija Mormoni, likita ce a sashen kula da lafiyar al'umma da ke asibitin koyarwa na Jami'ar Jihar Kaduna, wato Barau Dikko, wadda ta ce abu mafi muhimmanci bayan tashi daga bacci shi ne natsuwa.
A cewar Dr Khadija, "Daga cikin abubuwan da ake so mutum ya yi idan ya tashi daga bacci shi ne samun lokaci a kwance na wani ɗan lokaci. Mutum zai kasance yana ɗan nazarin rayuwa ko dai addu'a ko tsara abin da zai yi a ranar ko wani nazarin daban," in ji ta.
Ta ce wannan lokacin da mutum zai ɗauka yana kwance yana da matuƙar muhimmanci, "domin zai taimaka masa wajen tattara tunaninsa waje ɗaya, kuma ƙwaƙwalwarsa za ta fara aiki da kyau a ranar, sannan komai nasa zai tafi a tsare cikin natsuwa."
Abu na biyu da likitar ta ce yana da muhimmanci bayan tashi daga bacci shi ne shan ruwan ɗumi.
"Yana da kyau a sha ruwa mai ɗumi, ko dai a saka lemun tsami a ciki, ko kuma a sha ruwan ɗumin zalla. Ruwan ne zai taimaka wajen wanke hanji da ma cikin baki ɗaya. Sai ya fitar da sauran abincin da mutum ya ci jiya kafin a fara cin wani abincin sabo," in ji ta.
Ta ce haɗuwar sauran abincin da ya kwana a ciki, da sabon zai iya haifar da illi, inda a cewarta yakan jawo kumburin ciki.
Likitar ta ƙara da cewa ana buƙatar mutum ya motsa jiki kafin ya fara sauran abubuwan, sannan ya yi wanka, sai kuma ya ci abinci.
"Amma ba a cika so mutum ya ci abinci mai ɗauke da sinadarin sukari sosai ba, kuma an fi son abinci mai ɗumi."
Jiri bayan tashi daga bacci
A game da abubuwan da ba a so mutum ya aikata da zarar ya tashi daga bacci, Dr Khadija ta ce a yanzu da aka saba da amfani da wayar hannu, akwai buƙatar a guji ɗauko waya da zarar an tashi, inda ta ce "hasken yana rage kuzari da natsuwa."
Wani abu da aka daɗe ana tambaya shi ne da abin da yake jawo ganin jiri ko faɗuwa ko suma idan mutum ya miƙe bayan tashi daga bacci, Dr Khadija ta ce rashin isar jini da sauri ne.
"Yawan jini ne da ke shiga ƙwaƙwalwa ya yi jinkiri. Ƙwaƙwalwar ce ke kula ayyukan da sassan jiki ke yi, to idan aka samu jinkirin jinin, sai mutum ya fara ganin jiri ko ya faɗi, ko suma ko ma mutuwa idan ba a yi sa'a ba."
Likitar ta ce ana so ne a ɗan samu lokacin da ake buƙata domin jini ya gudana ya ƙarasa duk inda ake buƙata daga zuciya, "wannan ya sa jinkirin gudanar jinin ke janyo tsaiko a jiki."
Ta ce daga cikin abubuwan da ke jawo faruwar haka akwai tsufa da cututtuka irin su ciwon zuciya da daɗewa a kwance da juna biyu da daɗewa ana shan wani na'in magani.
Sai dai ta ce idan mutum ba ya ɗaya daga cikin waɗanda ta lissafa, "kuma yana ganin jiri ko da kuwa a hankali ya tashi, to akwai buƙatar ya je ya ga likita domin a duba shi," in ji ta.
Amma ta ƙara da cewa idan mutum yana da shekaru sosai ko mai juna biyu ɗin, "to idan ya farka yana da kyau ya ɗan kasance a kwance, sai ya ɗan juya kaɗan kafin ya tashi ya zauna. Bayan ya ɗan zauna ne sai ya miƙ a hankali ba zabura ba," in ji Dr Khadija.