Na'urar ɗakile hare-haren makamai masu linzami da Trump zai ƙaddamar

Lokacin karatu: Minti 5

Donald Trump ya ce mallakar tsibirin Greenland yana da matuƙar muhimmanci ga ƙirƙirar garkuwar tsaronsa ta Golden Dome.

Da yake magana a taron tattalin arzikin duniya a Davos, ya ce, "muna da abin da muke so ne daga Denmark, don tsaron ƙasarmu da sauran ƙasashen duniya, da ma kiyaye kawunanmu daga ayyukan maƙiyanmu. Wannan na cikin dalilanmu na samar da na'urar tsaro ta Golden Dome."

A shekarar da ta gabata, Trump ya ce garkuwar za ta fara aiki gadan-gadan kafin ƙarshen wa'adinsa na shugaban ƙasa a shekarar 2029.

Bayan fitar da kasafin kuɗin farko na dala biliyan 23, shugaban ya ƙiyasta kuɗin da za a kashe kan shirin a dala biliyan 175, amma ofishin kasafin kuɗi na majalisar dokokin ƙasar ya ce kuɗin da shirin zai laƙume na iya ninka wannan adadin har ninki biyar a cikin shekaru ashirin.

Tsare-tsaren sun ƙunshi hanyar sadarwa ta fasahar zamani a cikin ƙasa, da teku da sararin samaniya - musamman ma na'urori da za a kafa a sararin samaniya waɗanda za su iya daƙile makamai masu linzami.

Tsarin Golden Dome zai faɗaɗa tare da inganta sauran tsare-tsaren da ake da su don ƙara samun kariya daga barazanar hare-hare ta sama daga ƙasashe kamar Rasha da China.

Ta ya ya Golden Dome zai yi aiki?

Shirin na Trump ya samo asali ne daga wani ɓangare na shirin Iron Dome na Isra'ila, wanda ke amfani da na'urorin kariyar don magance barazanar makamai masu linzami masu gajeren zango kuma ana amfani da shi tun 2011.

Amma shi Golden Dome, zai fi Iron Dome girma, kuma an tsara shi ne domin tunkarar barazana da dama.

Zai yi amfani da hanyoyin sadarwa da suka ƙunshi ɗaruruwan taurarin ɗan'adam, wani abu da a baya zai kasance mai tsadar gaske, amma wanda zai iya yiwuwa a wannan zamanin na yanzu.

"Ronald Reagan ya so ƙaddamar da wannan shirin shekaru da dama da suka gabata, amma fasahar ba ta samu ba a wannan lokacin," in ji Trump, yayin da yake magana kan tsarin kariya daga makami mai linzami, wanda aka fi sani da "Star Wars", wanda tsohon shugaban ƙasar ya gabatar a shekarun 1980.

Trump ya ƙara da cewa "Golden Dome" zai kasance "mai iya kakkaɓo makamai masu linzami da aka harba daga kowane wani ɓangare na duniya, ko kuma daga sararin samaniya," in ji Trump.

Za a samar da na'urar ne don ƙara kariya daga makamai masu linzami (ciki har da makamai masu linzami - waɗanda ke iya tafiya da sauri fiye da saurin sauti) da kuma tsarin bama-bamai na orbital - wanda ake kira Fobs - wanda zai iya harba makamai daga sararin samaniya.

Babban Daraktan Cibiyar ƙere-ƙere ta fasahar Intanet ta Amurka, Rear Admiral Mark Montgomery (mai ritaya), ya shaida wa BBC cewa Golden Dome zai dogara ne da "rukuni uku ko huɗu na tauraron ɗan'adam waɗanda suka haɗa da ɗaruruwan taurarin ɗan'adam".

"Kuna da taurarin ɗan'adam da ke ganowa, ɗaruruwa daga cikinsu, suna gano idan aka harba makamai. Sannan kuna da jerin taurarin da ke bin diddigi. Sannan kuna da taurarin ɗan'adam waɗanda ke dauke da makamai masu linzami ko duk abin da kuke amfani da su wajen harbo makaman da aka harbo," kamar yadda ya shaida wa shirin BBC na Newsday.

Za a iya ƙera Golden Dome cikin shekara uku?

Shashank Joshi, editan tsaro a jaridar The Economist, ya shaida wa BBC cewa sojojin Amurka za su ɗauki shirin da muhimmanci, amma bai kamata a yi tunanin za a kammala shi a cikin wa'adin mulkin Trump ba, kuma maƙudan kuɗaɗen da za a kashe za su janye wani kaso mai tsoka daga kasafin kuɗin tsaron Amurka.

Admiral Montgomery ya yi amanna da wannan fahimtar.

"Wannan aiki ne da ke buƙatar shekara biyar zuwa bakwai zuwa 10.

"Shin akwai abubuwan da za a samu nan da shekara uku da za su inganta tsaron mu? Ƙwarai da gaske," in ji shi, amma ya ƙara da cewa "ba zai yiwu a samu tsarin tsaro da ke da inganci 100 bisa 100 ba" kuma a ce kafin ƙarshen wa'adin shugaban ƙasa na yanzu.

Waye zai ƙera Golden Dome?

Janar Michael Guetlein shi ne mutumin da aka ɗora wa alhakin jagorantar aikin Golden Dome na biliyoyin daloli.

Guetlein, babban hafsan soji ne a Amurka wanda Shugaba Trump ya bayyana a matsayin "mutum mai hazaƙa", wanda yake da gogewa kan abubuwan da suka shafi sararin samaniya.

A baya ya kasance shugaban Space Systems Command kuma daraktan na'urorin gano makamai masu linzami daga wurare masu nisa.

An haife shi kuma ya girma a jihar Oklahoma ta Amurka, Guetlein ya shiga rundunar sojojin saman Amurka a shekarar 1991 bayan ya kammala karatunsa a jami'ar jihar Oklahoma.

Me Rasha da China ke cewa kan Golden Dome?

Na'urar tsaro ta Golden Dome tun farko an ƙirƙire ta ne don kakkaɓo makamai masu linzami da aka harba daga Rasha da China.

Wani daftarin bayani da sashen leƙen asirin ma'aikatar tsaro ta fitar ya nuna cewa barazanar makami mai linzami "za ta faɗaɗa," tare da zargin ƙasashen biyu da bijiro da tsare-tsaren da za su iya samun galaba kan matakan tsaron Amurka.

Ƙasashen China da Rasha duk sun soki wannan ra'ayi.

Sabon tsarin tsaro "ya ba da damar ƙarfafa ɓangaren kayan yaƙin da za a iya amfani da su a sararin samaniya," in ji sanarwar Kremlin da aka buga bayan tattaunawa tsakanin Rasha da China a watan Mayun 2025.

Sai dai daga baya mai magana da yawun Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana shirin a matsayin "al'amari ne mai cin gashin kansa" ga Amurka, kuma ya yi nuni da cewa hakan na iya haifar da sake komawa tattaunawa kan batun makaman nukiliya.

A ɗaya ɓangaren kuma, ƙasar China ta bayyana cewa, shirin zai kawo cikas ga tsaron ƙasa da ƙasa, ta yadda za a ƙara rura wutar yunƙurin samar da makamai da kuma ƙara ƙarfin soja a sararin samaniya.

Golden Dome "ya fito fili ya tallata batun shirin ɗaura ɗamarar yaƙi a sararin samaniya... kuma yana da ɓangarori masu matuƙar tayar da hankali, waɗanda suka saɓawa yarjejeniyar sararin samaniya," in ji mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar a watan Mayu, sannan ya buƙaci Amurka ta yi watsi da shirin.

Ko Canada za ta shiga shirin Golden Dome?

Zuwa yanzu dai babu tabbas kan ko Canada za ta shiga shirin tsaron ba saboda ana takun-saƙa tsakanin ƙasashen da ke maƙwabtaka da juna, kan harajin da Trump ya sanya.

A Davos, Sakataren Baitulmali Scott Bessent ya ce an gayyaci Ottawa. Trump ya kuma ce ya kamata Canada ta yi godiya ga ''kan abubuwan kyauta da ta ke samu daga Amurka kuma tsarin zai kare Kanada .

A watan Mayun 2025, ofishin Firaministan Canada Mark Carney ya ce shi da ministocinsa suna tattaunawa da takwarorinsu na Amurka game da sabuwar dangantakar tsaro da tattalin arziki.

"Waɗannan tattaunawa a zahiri sun haɗa da ƙarfafa NORAD (Cibiyar tsaron sararin samaniya ta Arewacin Amurka) da kuma abubuwan da suka danganci hakan kamar Golden Dome," in ji ta.

A bara, Ministan Tsaro na Canada a lokacin Bill Blair shi ma ya yarda cewa Canada na da sha'awar shiga cikin shirin, yana mai cewa "yana da ma'ana" kuma abu ne da ya shafi "ci gaban ƙasa".