Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    Amma kafin nan Abdullahi Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. 'Venezuela ta saki fursunonin siyasa 80 saboda matsin lambar Amurka'

    Ƙungiyar Kare Hakkin Yan Adam a Venezuela, ta ce gwamnati ta saki fursunonin siyasa akalla 80, sakamakon matsin lamba daga Amurka.

    Shugaban ƙungiyar Foro Penal - wata kungiya mai sa ido kan fursunonin siyasa - ta ce tana tantance sunayen waɗanda aka sako.

    Venezuela ta sanar da sakin fursunonin siyasa sama da 400 a watan Disamba.

    Sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ƴan Adam sun ce adadin bai kai haka ba.

  3. Wutar lantarki ta katse a wasu sassan Amurka saboda guguwa

    Aƙalla gidaje da shaguna 600 ne suka rasa wutar lantarki a Amurka sakamakon wata mummunar guguwa da ta auka wa ƙasar.

    Jihohin kudancin ƙasar, irin su Tennessee da Texas da Mississippi a kuma Louisiana ne lamarin ya fi ƙamari.

    Al'ummar ƙasar da dama ne suka fuskanci wannan guguwa, yayin da ake fama da tsananin sanyi inda a wasu biranen yake maki 20 ƙasa da sufuli a ma'aunin salshiyos.

    Hukumar kula da hasashen yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin samun mummunar iska da saukar dusar ƙanƙara mai yawa a wasu sassan New England.

  4. Gwamnatin Sokoto za ta haramta 'almubazzaranci' yayin aure a jihar

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ce gwamnatina za ta gabatar da dokokin haramta abin da ya kira almubazzaranci a lokacin aure a faɗin jihar.

    Ahmad Aliyu ya bayyana haka ne a lokacin ƙaddamar da masallaci da makamarantar zawiyyar Sheikh Aliyu Bunza da aka sabunta.

    ''Matakin ya zama wajibi saboda aydda ake samun ƙaruwar wahalhalun da ake ɗorawa mutanen da ke shirin yin aure ta hanyar tsara abubuwan da ba za zama wajibi ba, lamarin da ya sa matasa maza da mata da suka isa aure ke shan wahalar yin aure'', in ji gwamnan.

    Gwamnan ya ce waɗannan wahalhalu na taimaka wa wajen ƙaruwar yawan marasa aure maza da mata a jihar.

    ''Wanda kuma hakan ke taimakawa wajen ƙaruwar rashin tarbiyya tsakanin matasa, waɗanda suka gaza yin aure saboda tsadar buƙatun da ake gabatarwa gabanin auren'', in ji gwamnan.

    Matakin na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan wani bidiyon wata yarinya a jihar ya ɓulla da aka yi wa kayan lefe na gomman akwatina da motar hawa, lamarin da ya janye ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.

  5. Sojojin Isra'ila na binciken maƙabarta a Gaza don neman gawar ɗan ƙasarta

    Isra'ila ta ce tana bincike cikin wata maƙabarta a Gaza don neman Ran Gvili, mutum guda da ya rage cikin Isra'ilawan da Hamas ta yi garkuwa da su a 2023.

    Isra'ilar ta ce dakarunta za su yi binciken ne a wuraren da suke iko da su a Gaza.

    Ƙungiyar Hamas ta ce ta jima da bayar da bayanan inda za a samu Mista Gvili, kuma dakarun na Isra'ila na aiki ne bisa bayanan da Hamas ɗin ta bayar.

  6. Gwamnan Kano zai koma jam'iyyar APC ranar Litinin

    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf zai koma jam'iyyar APC, mai mulkin Najeriya a ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026.

    A ranar Juma'a ne gwamnan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyarsa ta NNPP, saboda abin da ya bayyana da rikicin cikin gida da ke addabar jam'iyyar, sai dai a lokacin bai bayyana jam'iyyar da zai shiga ba.

    Sai dai cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Lahadi, ya ce gwamna ya yanke shawarar komawa tsahowar jam'iyyarsa na APC bayan tuntuɓar abokan shawararsa na siyasa da sauran masu ruwa da tsaki.

    Gwamnan ya bayyana APC da jam'iyyar mai cikakken tsari wajen tafiyar da gwamnati.

    Abba Kabir Yusuf ya taɓa shiga APC a 2014 har ma ya tsaya takarar sanata, kodayake Kwankwaso ne ya yi takarar kujerar a lokacin.

    Gwamna Abba Kabir ya ce sake komawa APC zai ƙara ƙarfafa alaƙa mai ƙarfi tsakanin gamnatin jihar da ta tarayya, wani abu da sanarwar ta ce zai samar wa jihar ci gaba da ƙarfafa tsaro da inganta ci gaban jihar.

    ''Haka kuma matakin zai kawo masalaha kan rikicin siyasar jihar da haɗin kai tsakanin al'ummar Kano'',

    Sanarwar ta ƙara da cewa a ranar Litinin ɗin gwamnan zai karɓi katin jam'iyyar APC tare da wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22 ciki har da kakakin majalisar, da ƴanmajalisar tarayya takwas da shugabannin ƙananan hukumomi 44.

  7. Zanga-zangar mata ta ɓarke a Turkiya bayan samun gawar mace cikin shara

    Ɗaruruwan mata ne suka fantsama kan titunan Santanbul, babban birnin ƙasar Turkiyya domin nuna damuwarsu kan samun gawar wata mata da aka daddatsa zube cikin bola a birnin.

    Matar -wadda masu bincike suka ce ƴar asalin Uzbekistan ce - an daddatsa gawarta tare da sare ƙafafunta.

    Tuni ƴansanda suka tsare mutum uku bisa zarginsu da hannu a kisan matar ma shekara 37.

    Kawo yanzu ba a san dalilin kisan matar ba.

    Kodayake Turkiyya ba ta adana adadin kisan gillar da ake yi wa mata, ƙungiyoyin ƙare haƙƙi na cewa a shekarar da ta gabata kawai an kashe kusan mata 600 a ƙasar.

  8. An gurfanar da sojojin haya da ke da hannu a yaƙin Sudan

    Babban lauyan gwamnatin ƙasar Sudan ya fara shari'a kan wasu sojojin hayar ƙasashen waje sama da 120 da ke yaƙi tare da dakarun ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF).

    Intisar Ahmed Abdel Mutaal, wadda ke shugabantar kwamitin da ke bincike kan karya dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa, ta ce tuni aka yanke wa wasu sojojin hayar hukuncin kisa.

    Hukumomin Sudan na zargin ƙungiyar RSF da ɗaukar mayaƙan ƙasashen waje daga Chadi, da Sudan ta Kudu da Habasha da Colombia domin taya ta faɗa a mummunan yakin basasa da ake yi da sojoji.

    Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yaƙin da aka fara tun a shekarar 2023 a matsayin mafi girman matsalar jin ƙai a duniya.

  9. Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Kano ya ajiye muƙaminsa

    Kwamishin Kimiyya da Fasaha na jihar Kano, Dokta Yusuf Ibrahim Kofarmata ya sauka daga muƙaminsa sakamakon rikicin siyasar da jihar ta shiga.

    Cikin wata sanarwa da kwamishinan ya fitar a ranar Lahadi ya ce ya ɗauki matakin ne saboda gwamnatin da yake aiki a cikinta ta kauce wa tsarin siyasar da akayi gwagwarmayar kafata a doransa.

    ''Ina mai godiya ga Allah, ina godiya ga maigirma Jagoranmu, Sen. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, da maigirma Gwamnan Kano, Alhaji Abba K Yusuf, da kuma jama'a saboda gudunmawar da su ka bani a lokacin da na gudanar da aiki na hidimtawa al'ummar jaharmu ta Kano'', kamar yadda kwamishinan ya wallafa cikinn sanarwar tasa.

    Tun bayan ficewar Abba Kabir daga NNPP tare da barin Kwankwanso, masana siyasa da masu bibiyarta ke hasashen samun rabuwar kawuna tsakanin manyan ƙusoshin gwamnatin.

  10. Tsohon mataimakin shugaban Kenya ya zargi gwamnati da yunƙurin halaka shi

    Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Kenya Rigathi Gachagua ya ce yana cikin ƙoshin lafiya a gidansa da ke Wamunyoro, a gundumar Nyeri, a yankin tsakiyar ƙasar Kenya, bayan shafe sa'o'i na rashin tabbas kan inda yake sakamakon wani lamari da ya auku ranar Lahadi.

    Tun da farko, Gachagua ya yi zargin cewa "wasu tawagar masu kisan gilla da ƴan sandan yankin ke marawa baya," suna aiki bisa umarnin shugaban ƙasar William Ruto, sun tarwatsa wani taron coci da shi da tawagarsa ke halarta.

    A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Gachagua ya ce, "Rundunar kisan gillar da ƴan sandan yankin ke marawa baya sun mamaye wuraren biyu, kuma ba mu san manufarsu ba bayan sun kasa kashe ni a cikin coci."

    Gachagua, ya kasance ɗaya dahga cikin masu sukar shugaba Ruto.

    Damuwa kan lafiyarsa ta bazu bayan rahotannin cewa jami'an tsaro da wasu da ba a san ko su wanene ba sun tayar da tarzoma a harbar cocin, lamarin da ya sa aka kwashe shi da tawagarsa cikin gaggawa.

    Hukumomin gwamnatin Kenya dai sun ce ana gudanar da bincike kan lamarin.

  11. Gwamnatin Jihar Anambra ta soke umarnin zaman gida ranar Litinin

    Gwamnatin jihar Anambra ta sanar da dakatar da batun zaman gida a ranar Litinin a jihar "cikin gaggawa".

    Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakatariyar hukumar kula da ilimi nma matakin farko ta jiha Mgbemena Loveline E, a madadin hukumar.

    Har ila yau, ta yi gargaɗin cewa ma’aikatan gwamnati, waɗanda suka bi umurnin zama a gida za su gani a kwarya a lokacin biyan albashi.

    “Wannan umarnin na nufin, duk wani ma’aikaci, mai koyarwa a aji ko mara koyarwa, wanda ya kasa zuwa makaranta ko ofis a ranar Litinin, ko dai zai karbi kashi 20 na albashinsa ko kuma ya yi asararsa baki daya,” in ji sanarwar.

    Manyan sassan jihar Anambra sun kwashe shekaru da dama suna gudanar da zaman gida na mako-mako a kowace ranar Litinin - lamarin da ke dakatar da harkokin kasuwanci da zamantakewa a faɗin jihar.

    Tun farko dai ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a yankin kudu maso gabashin ƙasar ne suka kafa wannan dokar, lamarin dai ya haifar da fargaba da rashin son gudanar da harkokin kasuwanci a tsakanin mazauna yankin, inda kasuwanni da makarantu da wuraren aiki suka kasance a garƙame a farkon kowanne mako.

    Ana kallon wannan umarnin na zama a gida a matsayin mai cutarwa ga rayuwar al'umma da kuma tattalin arzikin jihar.

  12. Ana ci gaba da zanga-zanga a sassan Amurka bayan jami'an tsaro sun harbe wani mutum

    Jami'an shige da fice na Amurka sun harbe wani mutum har lahira a Minneapolis, lamarin da ya haifar da zanga-zanga da kuma tofin Allah tsine daga sassa daban daban na ƙasar.

    Ɗaruruwan masu zanga-zangar ne suka fito cikin sanyi don nuna adawa da harbin Alex Pretti, wanda danginsa suka bayyana a matsayin ma’aikacin jinya mai shekaru 37 da haihuwa, yayin wata arangama da aka yi da safiyar Asabar.

    Bidiyo da yawa daga wurin da abin ya faru sun nuna hatsaniya tsakanin jami'an shige da fice na tarayya da Pretti.

    Hukumomin tarayya da na jiha sun ba da rahotanni masu cin karo da juna kan yadda lamarin ya auku, wanda ya zo kasan makonni uku bayan wani jami'in hukumar shige da fice (ICE) ya kashe wata mata mai suna Renee Good a cikin motarta a birnin Minneapolis.

  13. Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta kan aibata Kwankwaso

    Gwamnatin Kano ta gargaɗi masu amfani da shafukan sada zumunta game da aibata jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwanso.

    Gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ne ya yi gargaɗi kwana guda bayan raba gari da jam'iyyar NNPP da Sanata Kwankwaso ke jagoranta.

    Yayin wani jawabi da ya gabatar a taron bayar da kyaututtuka da gwamnatinsa ta shirya wa masu amfani da shafukan sada zumunta ranar Asabar a jihar, Gwamna Abba ya bayyana Kwankwaso a matsayin shugaban da ya cancanci girmamawa saboda sauye-sauyen da ya samar wa Kano.

    A ranar Juma'a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP da ake zaɓe shi matsayin gwamna a cikinta a 2023.

    A ranar Asabar ma wasu ƴan majalisar dokokin jihar 22 ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar jihar, Hon. Jibril Ismail Falgore, suka sanar da bin sahun gwamnan wajen barin jam'iyyar NNPP.

  14. An fara kaɗa ƙuri'a a zagayen ƙarshe na zaɓen Myanmar

    An fara kaɗa ƙuri'a a zagaye na uku kuma na ƙarshe na zaɓe a yankuna da dama na ƙasar Myanmar wadanda ba sa ƙarƙashin ikon ƴan tawaye.

    A cewar wata tawagar BBC da ta ziyarci rumfunan zaɓe da dama yayin da aka gudanar da zaɓen, akwai yanayi na fargaba, inda mutane da dama ke jin an matsa musu su fito.

    Ƴan jarida sun ce jami'an leƙen asiri na soji na biye da su yayin da suke ƙoƙarin yaɗa labaran yaƙin neman zaɓe.

    Ana sa ran jam'iyyar da ke goyon bayan sojoji za ta samu gagarumin rinjaye, a zaɓen da Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama suka bayyana a matsayin mara adlaci ko daidaito.

    Ƙasar Myanmar dai ta faƊa cikin rikicin cikin gida tun bayan da sojoji suka hamƁarar da gwamnatin farar hula kusan shekaru biyar da suka gabata.

  15. Sassan Amurka na fuskantar yanayin hunturu mai tsanani

    Mummunar iska mai ƙanƙara ta haifar da ruwan sama a jihohin New Mexico da kuma Texas a yayin da kuma ta ke ci gaba da yaɗuwa zuwa sassan da ke arewa maso gabashin ƙasar.

    Mutane miliyan ɗari biyu iskar za ta iya shafa, sannan kuma masu hasashen yanayi sun yi gargaɗin cewa za a iya samun sanyin da zai kai ƙasa da maki ɗaya a ma'aunin celcius.

    Tuni aka ɗauke wutar lantarki musamman a Texas da Louisiana sannan kuma mutane fiye da dubu 100 na zaune a cikin duhu.

    An dai sauke tashi da saukar jirage kusan dubu 13 a faɗin ƙasar.

  16. Sojoji sun kama matar da ake zargin tana kai wa ƴan Boko Haram wiwi

    Dakarun rundunar ɗguiwa ta arewa maso gabas, Operation HADIN KAI, sun kama wata mata mai shekaru 65 da haihuwa, bisa zarginta da safarar miyagun ƙwayoyi ga ƴan ƙungiyar Boko Haram da ke kai hare-hare a sassan jihar Borno.

    Wata sanarwa da jami'in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanar Sani Uba ya fitar ta ce an kama wanda ake zargin ne a karamar hukumar Askira uba da ke jihar Borno, a ranar 23 ga watan Junairu, 2026, yayin wani samame da rundunar ta kai sakamakon bayanan sirri da ta tattara.

    Sanarwar ta ƙara da cewa ana zargin matar ne da zama babbar mai samar da tabar wiwi ga ƴan Boko Haram da ke aiki a faɗin yankin da ya haɗa da Askira Uba da Rumirgo da Gwahi da Wamdiyo, da Uvu da kuma Gaya.

    Binciken farko dai ya nuna cewa wadda ake zargin ta samo tabar wiwin ne daga ƙaramar hukumar Sarti Baruwa ta jihar Taraba kuma an kama ta da ƙunshin ganyen wiwi guda 14 mai nauyin kimanin kilogiram 30.

    ''A halin yanzu dai wadda ake zargin ta na tsare yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, don ganowa tare da wargaza hanyoyin da ake amfani da su wajen safara da rarraba miyagun ƙwayoyin''. In ji sanarwar

  17. Wani mutum ya hau gidan bene mai hawa 101 ta bango

    Wani ɗan ƙasar Amurka mai hawa dutse Alex Honnold ya yi nasarar hawa wani dogon bene a Taiwan ba tare da igiya ko wani kayan kariya ba.

    Ginin mai suna Taipei 101 wanda aka yi masa laƙabi saboda yawan hawan da ya ke da su, ya kai tsawon mita 508.

    Honnold ya shahara bayan da ya kasance mutum na farko da ya hau El Capitan, dutse mai ɗan karen tsawo da ke gandun dajin Yosemite da ke California - kuma ba tare da igiya ko kayan tsaro ba.

    Tun da farko dai an shirya hawan ginin ne a ranar Asabar amma aka jinkirta sakamakon ruwan sama.

    Wannan bajinta na shi dai a watsa shi kai-tsaye a dandalin Netflix.

    Honnold ya kammala hawa ginin ne a cikin awa ɗaya da minti 31.

  18. An haramtawa ƴan jarida shiga zaman kwamitin bincike kan rikicin bayan zaɓe a Tanzania

    An hana ƴan jarida a Tanzaniya halartar zaman kwamitin bincike kan rikicin da ya biyo bayan zaɓen shugaban ƙasa, yayin da waɗanda rikicin ya rutsa da su ke bayar da shaida.

    Kwamitin da shugaba Samia Suluhu ta kafa, na gudanar da bincike a kan rikicin da nufin gano musabbabin sa da kuma ba da shawarar hanyoyin da za a bi wajen samar da sulhu a ƙasar.

    An buɗe zaman farko ga manema labarai, kuma duka kafafen yaɗa labarai na gida da na waje sun ba da rahoto kan shaidar waɗanda abin ya shafa.

    Sai dai kuma ƴan jarida da wasu kafafen yaɗa labarai sun ce ba a ba su damar halartar tarukan da suka biyo biyo baya ba ranar Asabar.

    A ranar Juma'ar da ta gabata, kafofin yaɗa labarai na cikin gida ne aka bai wa damar shiga zaman kwamitin a birnin Dar es Salaam.

    Wata sanarwa da wata jarida mai zaman kanta 'The Citizen' ta wallafa a shafukan sada zumunta ta ce an ba wa ƴan jarida damar yaɗa labaran zaman da aka yi ranar Juma’a, inda waɗanda abin ya shafa suka bayyana yadda al'amura suka gudana lokacin rikicin.

    Har yanzu ba a tabbatar da ko za a mai do da damar kafofin watsa labarai na shiga zama na gaba ba.

  19. An dawo da Intanet a sassan ƙasar Iran

    Wata kafar yaɗa labaran Iran ta rawaito cewa gwamnatin ƙasar dawo da intanet din data ɗauke a sassan ƙasar.

    Gwamnatin ta katse intanet ɗin ne a lokacin da aka fara zanga zangar nuna adawa da matakan gwamnati a faɗin ƙasar a ƙarshen watan da ya gabata.

    Jami'ai sun ce za a ɗauki tsawon lokaci kafin duka harkokin Intanet su daidai ta saboda wasu matsaloli na na'ura.

    Ɗaukewar intanet ɗin ya sa an gaza tabbatar da adadin mutanen da aka kashe a lokacin zanga zangar.

    Wata ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam da ke Amurka ta ce an kashe fiye da mutane dubu huɗu.

  20. Jami'an tsaron Amurka sun harbe wani mai zanga-zanga a Minnesota

    Jami’an tsaro na gwamnatin tarayya a Amurka sun bindige wani mutum mai zanga-zanga a birnin Minneapolis ranar Asabar.

    Wannan dai shi ne mutum na biyu da aka kashe a birnin tun lokacin da gwamnatin Trump ta ƙaddamar da wani yaƙi na musammman kan ƴan cirani a jihar ta Minnesota.

    Jami’an yankin sun bayyana sunan mutumin a matsayin Alex Pretti mai shekaru 37, ɗan ƙasar Amurka ne kuma ma'aikacin jinya da ke zaune a Minneapolis.

    Bidiyo da aka wallafa a shafukan intanet sun nuna yadda aka yi taho-mu-gama tsakanin jami'an tsaron kan iyaka da kuma mutumin.

    Ma’aikatar tsaron cikin gida (DHS) ta ce jami’an sun yi harbi ne domin kariyar kai bayan Pretti, wanda suka ce yana da riƙe da bindiga, ya bijirewa yunƙurinsu na ƙwace masa makamai.

    Lamarin, wanda ya zo makonni biyu bayan harbe Renee Nicole Good da wani jami’in shige-da-fice ya yi, ya haifar da ci gaban zanga-zanga tare da kiraye kiraye da shugabannin yankin cewa jami'an tsaron gwamnatin tarayya su fice daga birnin.