Yadda 'Isra'ila ke ƙara cin wasu yankuna a Gaza' duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

    • Marubuci, Benedict Garman
    • Marubuci, Emma Pengelly
    • Marubuci, Matt Murphy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 6

Isra'ila ta ƙara matsar da shingenta - da aka amince da ta tsaya a lokacin yarjejeniyar tsagaita wuta a matsayin wurin da take iko da shi - zuwa cikin Gaza, wani abu da ya ƙara haifar da fargaba tsakanin Falasɗinawa.

Hotunan tauraron ɗan'adam da sashen tantance labarai na BBC Verify ya gani, sun nuna cewa a cikin aƙalla wurare uku, Isra'ila ta ƙara matsar da shigayen zuwa cikin Zirin Gaza.

A cikin yarjejeniyar - wadda Amurka ta samar kuma Hamas da Isra'ila suka amince da ita - Isra'ila ta amince ta janye sojojinta zuwa bayan wani layi mai launin ruwan ɗorawa da aka shata ta hanyar amfani da wasu bulo na siminti.

A cikin watan Oktoban shekarar da ta gabata, Ministan tsaron tsaron Isra'ila, Israel Katz ya yi gargaɗin cewa duk sojojinsa za su ''harbi duk wanda'' ya ƙetare layin.

Tun bayan kalaman ministan tsaron an riƙa samun rahotonnin kashe-kashe a kusa da layin.

A Beit Lahia da Jabalia da kuma al-Tuffah dakarun Isra'ila sun saka bulo masu yawa a kan iyakar da aka shatan, daga baya kuma suka sake matsar da su zuwa cikin Gaza.

A duka faɗin yankin an matsar da iyakar a wurare 16.

A unguwar-Tuffah da ke Birnin Gaza, hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna dakarun IDF sun matsar da bulon tsakanin ranar 27 ga watan Nuwamba da 25 ga watan Disamba.

An matsar da iyakar da kusan mita 295, ƙwatanƙwacin ƙafa 968 zuwa cikin Gaza.

Game da bulon da aka matsar, BBC Verify ta lura da taswirar wasu iyakoki 205. Kuma ta fahimci cewa fieye da rabinsu an matsar da su sosai zuwa cikin Zirin Gaza, fiye da yadda suke a baya a kan taswirar.

Kakakin IDF ya ce rundunarsa ta yi watsi da ''duka iƙirarin da ke cewa sojojoji sun matsar da iyakokin ko hanyoyin shiga Gazar''.

''IDF ta saka layin inda kowa zai gan shi, kamar yadda sharaɗin yarjejeniyar ya tanada,'' in ji shi.

Bayanan da aka gani daga wasu hoyunan tauraron ɗan'adam ya zuwa ranar 11 ga watan Janairu sun nuna cewa wasu ɓangarori da iyakar mai launin ruwan ɗorawa - da Shugaban sojin Isra'ila ya bayyana da ''sabuwar iyaka'' - ba a yi masa fenti ba, fiye da wata uku bayan yarjejeniyar tsagaita wutar.

Sabbin Hotunan tauraron ɗan'adam da BBC Verify ta yi nazarinsu sun nuna cewa ba a sanya shinge a kusan kilomita 10 (mil shida) na yanki ba - lamarin da ya sa wasu mutane a Gaza ke kokawa game da sanin inda farkon abin da IDF ke kira "yankin mai hatsari".

A watan da ya gabata, wani mutum mai shekara 23 a kusa da Khan Younis - wanda BBC ta ɓoye sunansa don kariya - ya ce sojojin Isra'ila suka matsar da bulon gaba da gidansa, lamarin da ya sa ya nan take ya zama ya ''maƙale''

"A yanzu muna zaune a gaban layin, amma bayan dulon da suka sake sakawa, ba tare da sanin makomarmu ba,'' kamar yadda ya bayyana.

"Mukan shiga yanayin tashin hankali cikin dare. Mukan ji ƙarar harsashi da fshewar abubuwa da nausawar sojoji da ƙarar bindigogi, tare da shawagin jirage marasa matuƙa."

Farfesa, Andreas Krieg masanin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya daga Jami'ar King College da ke Landan ya yi kira matsar da iyakar da ''aikin kanikancin iyaka''.

"Matsar da kan iyakar bayan kuma akwai iyakar da aka amince da ita, Ira'ila na nuna cewa tana da ikon matsar da inda ƴan Gaza za su zauna, su yi yawo su je gona ba tare da ayyana sauya iyakar a hukumance ba,'' in ji shi.

Amma Efraim Inbar - shugaban Cibiyar Dabaru da Tsaro na Birnin Ƙudus - ya ba da shawarar cewa layin da aka zayyana ba zai iya yin la'akari da shingen da alamomi ba kuma injiniyoyin IDF na iya sanya shingen inda suka sami ''sauƙin sanyawa''.

Kashe-kashen da aka samu a kusa da iyakar

Tun bayan gargaɗin Katz na watan Oktoba, sojojin Isra'ila sun kashe mutanen da suka tsallak iyakar sau aƙalla 69, kamar yadda bayanan jerin sanarwa da IDF ke fitarwa a shafinta na Telegram da waɗanda take aike wa BBC suka nuna.

A ranar 19 ga watan Disamba IDF sun ƙaddamar da wani hari kan wata makaranta ke zaman mafaka ga ƴangudun hijira a unguwar al-Tuffah a Birnin Gaza, mai tazarar mita 330 daga kan iyakar, kamar yadda taswirar IDF ta nuna, amma ƴan mitoci daga shingen da suka matsar.

Shaidu sun ce an ƙaddamar da harin ne a daidai lokacin da ake ɗaura aure a sansanin. Mutum biyar ne ciki har da ƙananan yara suka mutu a lokacin harin, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza.

A cikin wata sanarwa da IDF ta fitar game da harin, ta ce ta kai shi ne kan wasu ''mutane da take zargi'' a yamma da shingen, inda ta ce tana ci gaba da nazarin harin, kuma tana ''kaico kan cutar da mutanen da ba ta hara ba''.

A wani mummunan lamarin, an kashe wani matashi mai suna Zaher Nasser Shamiya mai shekara 17 a kusa da bulon a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza.

Mahaifinsa ya ce dakarun IDF ne suka harbe shi kafin su bi ta kansa da tankar yaƙi a ranar 10 ga watan Disamba.

"Tankar ta ragargaje gawarsa filla-filla bayan da ta zo har inda aka amince mutane su yi walwalarsu,'' in ji shi

Haka a watan Nuwamba wata kafar yaɗa labaran yankin ta bayar da rahoton cewa sojojin Isra'ila sun kashe wasu yara biyu asu shekara 8 da 10 ko 11.

Baffansu ya ce an kashe yaran ne a lokacin da suke nemo wa mahaifinsa itacen girki wanda nakasasshe ne.

Yayin da take fitar da sanarwar game da lamarin, IDF ta ce ta kashe wasu mutum biyu da takje zargi, waɗanda suka tsallaki layi, suna aikata wasu abubuwan zargi a ƙasa, sannan suka doshi inda IDF suke.

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayanin yadda ta gano yaran waɗanda ake zargi ba ne.

Kakakin IDF ya zargi mayaƙan Hamas da buɗe sojojin Isra'ila wuta har sau shida a ''bayan layin'' cikin makon da ya wuce, kamar yadda ta aike wa BBC Verify wata sanarwa.

Rusa gine-gine da ƙwace wasu

Yayin da Isra'ila ta amince da janye dakarunta zuwa bayan layin da aka shata, ƙarƙashin yarjejeniyar ta watan Oktoba, bidiyoyi da hotunan tauraron ɗan'adam da BBC Verify ta gani sun rika nuna motocin IDF na ayyukansu a gaban layin da aka shatan.

Wasu bidiyoyi da BBC ta tantance sahihancinsu sun nuna wasu motocin yaƙi da na buldoza da tazarar mita 400 bayan layin a shataletalen Bani Suhailat da ke Khan Younis.

Haka ma wasu bidiyoyin tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 25 ga watan Disamba ya nuna wata tankar yai da motar rusau da wasu motocin IDF na tsaye a tazarar mita 260 bayan layin a yankin Beit Lahia.

A wasu wuraren ma IDF na matsar da shingen tare da rusa wasu gine-ginen da ke kusa.

A sassan gabashin Birnin Gaza, hotunan tauraron ɗan'adam sun nuna ɗaruruwan gine-gine an daidaita su da shingen ko ma an mayar da su bayan shingen, daga nan kuma aka ruguza su.

Sannan a kusa da Jabaliya, Sojojin Isra'ila sun rusa wasu gine-ginen makarantu, masu tazarar mita 150 daga kan iyakar.

A wasu wuraren da aka rua gine-ginen, ɓaraguzai kan ɓoye layin da aka shatan.

Kakakin IDF ya ce sojojin Isra'ilar na lalata hanyoyin arƙashin ƙasa na Hamas, waɗanda ta ce sun bi ta ƙarƙashin gine-gine a kan layin da ma bayansa, yana mai cewa lalata hanyoyin ƙarƙashin ƙasan ''ka iya haifar da rushewar gine-gine a duka ɓangarorin.

A ranar Laraba ne Amurka ta ce za a fara aiki da kashi na biyu na yarjejeniyar tsagaita wutar.

Wanda a ƙarƙashinsa ake sa ran sojojin Isra'ila za su ƙara janyewa daga wasu sassan Zirin Gazan.

To sai dai ba a bayyana lokacin janyewar ba, wadda ke da alaƙa da ''ajiye makaman'' Hamas, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Ƙarin rahoto daga Maha El Gaml.