Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwa 7 game da tshon fitaccen mawaƙi Fela Anikulapo Kuti
Labarin Fela Anikulapo Kuti ya sake zama sabon labari kusan shekaru 30 bayan mutuwarsa ba kuma a lokacin bikin tunawa da shi ba.
Bayan shekaru da dama, taurari a mawaƙan Najeriya da suka yi ƙaura daga ƙasar na amfani da irin salon waƙoƙinsa bayan ya mutu.
Tamkar gado, waƙokin Fela sun zama waɗanda mawaƙa ke kwaikwayo a faɗin duniya kamar misalin Kendrick Lamar wanda ya yi waƙar Mortal Man da Tiwa Savage wadda ta yi waƙar 49-99 da kuma Wizkid da waƙarsa mai suna Jaiye Jaiye.
A ƙarshen shekara ta 2025, an yi gagarumin taron tunawa da shi da kuma irin waƙokinsa da ake kira Afrobeat rebellion.
Ko me za ka iya sani game da rayuwarsa duk da cewar an shafe sama da shekaru 50 ana tunawa da shi?
Fela mai hannun rubutu
Yayin bikin tunawa da shi an bayyana cewar bayan amfani da waƙoƙi wajen jan hankalin gwamnati, Fela Kuti yana sayen shafuka a jaridu don ya caccaki gwamnati kan abinda yake gani ba daidai ba ne.
Yana rubutun ne da turancin pidgin sannan yana farawa da ''Chief Priest Says'' watau ''babban boka ya ce''.
Batutuwansa sun ƙunshi sukar gwamnati kan abinda suka yi ba daidai ba, ko kuma ya tona asirin irin zagon ƙasan da ƙasashen waje suke yi ko ya caccaki Amurka game da sabon salon mulkin mallaka da take amfani da shi, a wasu lokutan kuma ya na sanar da lokacin da zai yi waƙoƙi ne kawai.
Auren mata 27 a rana ɗaya
A ranar 20 ga watan Fabrairu shekara ta 1978 ne ya auri mata 27 daga cikin matan da suka yi dandanzo don shi.
Lamarin dai ya fusata wasu mutane to amma Fela ya ce al'adar Afirka ce don haka ko a jikinsa.
Sai dai da dama daga cikin matan 27 da ya aura ba su jima tare da shi ba.
Zauren rawar banjo na Afrika Shrine
Fela ya fara ƙaddamar da zauren al'adun gargajiya mai suna Fela Shrine a farkon shekara ta 1970 a matsayin dandalin kaɗe-kaɗe da raye-raye da daddare.
Inda yake cashewa da sabuwar ƙungiyar sa ta Africa 70 a wasu ranakun mako ya kan shafe mintuna 30 yana rera doguwar waƙa.
An manna hotunan shugabannin Afirka da suka yi fafutika irinsu Kwame Nkurumah da Malcom X da mahaifiyarsa Funmilayo Anikulapo Kuti da kuma hotunan wasu abubuwan da Yarabawa ke bautawa.
Ransom-Kuti zuwa Anikulapo Kuti
A farkon 1970 ne Fela ya sauya sunansa daga Ransome inda ya ce sunan bayi ne daga nan ya koma Anikulapo Kuti wanda ke nufin "mutumin da ya sanya mutuwa a cikin aljihu".
Ba suna kawai ya sauya ba, Ronsome-Kuti ya kasance kakansa ne kuma attajiri sannan limamin Coci ne, cikakken sunansa shi ne Reverend Josiah Jesse Ransome-Kuti wanda ya fara yin waƙar da aka naɗa a Najeriya.
Fela ya fice daga Addinin Kirista.
Abin da ya sa yake sanya kamfai a gida
A cikin kalakuta wadda Fela ya bayyana a matsayin ƙaramar jamhuriyarsa, ya na yawo da kamfai har ma akwai hotunansa da dama sanye da kamfai kawai a jikinsa.
Ya ce abinda ya sa ya ke zama da kamfai shi ne, don ya nuna ba shi da ƙiba watau akwai banbanci tsakaninsa da masu hannu da shuni a Najeriya.
Sannan ya na nuna tabon dukan da aka yi masa ya yin da ya yiwa ƴansanda turjiya a lokutan da suke amfani da ƙarfi kan jama'a.
Duk da haka ya na riƙe da al'adar fafutuka wadda ya gada a wurin mahaifiyarsa.
Tsugunar da marassa muhalli
Fela Anikulapo Kuti ya kira wurin da ya ke zaune da suna Kalakuta, wadda ya sanyawa sunan ɗaya daga cikin gidajen kurkukun da ya taɓa zama.
A cikin Jamhuriyar Kalakuta akwai cibiyar kula da marassa lafiya, akwai kuma matsugunin mutanen da basu da muhalli sannan mafaka ce ta masu fafutukar siyasa.
Shan ɗauri a kurkuku
Gabaɗaya jikin Fela a cike yake ta tabo, jikinsa da ruhinsa kuwa sun yi fama da kamu, inda aka tsare shi sau 200. Kamar yadda," Rikki Stein ya shaidawa BBC'' ya yin bikin kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa.
An taɓa kama shi ranar 4 ga watan Satumba shekara ta 1984 ya yin da zai shiga jirgi don tafiya ƙasar waje inda zai yi waƙoƙi.
An kama shi bisa zarginsa da safarar kuɗaɗen ƙasar waje da yawansu ya kai fan £1600 cikin jakarsa an kuma yanke masa hukunci zaman gidan kurkuku na shekaru 5.
Afrobeat Rebellion ta ce jama'a sun yi ta sukar gwamnati tare da Allah wadai da ɗaurin da aka yi masa har sai da aka sako shi bayan kwanaki 532 da ɗaure shi.
A ranar 23 ga watan Afrilun shekara ta 1986 aka sake shi bayan Alkali ya ce gwamnati ce ta matsa masa lamba ya saki Fela.
Stein ya ce ya yi imani ba batun kuɗi ba ne, sojoji ne suke ganin ya zamar musu ƙalubale don haka suke son rufe masa baki.
To amma ɗaurin da aka yi masa a gidan kurkuku ya fusata al'umma a duniya har Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ƴan Adam Amnesty International ta ce an zalunce shi.
Waƙokinsa sun karaɗe duniya gidajen rediyo sun riƙa sanya waƙoƙinsa.