Alamu biyar da ke nuna cewa ɗan'adam na samun ci gaba a doron ƙasa

Lokacin karatu: Minti 6

A cikin shekarar da ta ƙunshi matsalolin yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen siyasa da matsin tattalin arziki tsakanin talakawa, ba abu ne mai sauƙi a iya cewa shekarar 2026 za ta faranta wa mutane rai ba.

To amma a yayin da ake tsaka da samun labarai da a bubuwa masu sosai rai, akwai dalilai da dama da ke nuna samun farin ciki a sabuwar shekarar.

A cikin wanna muƙala, mun zaƙulo wasu abubuwa biyar, da ke tuna mana irin nasarorin da muka samu cikin gomman shekaru a fannoni daban-daban.

Gagarumar raguwar yawan talakawa

Daga shekarar 1990 zuwa 2025, adadin mutanen da ke cikin matsanancin talauci a duniya ya ragu daga mutum biliyan 2.3 zuwa miliyan 831, kamar yadda alƙaluman Bankin Duniya suka nuna.

"Alƙaluman sun nuna cewa kimanain mutum biliyan ɗaya da miliyan 469, sun fice daga ƙangin matsanancin talauci, musamman tsakanin shekarun 1990 zuwa 2010, a lokacin da talauci ya ragu daga kashi 47% zuwa 10%," a cewar Farfesa José Manuel Corrales, masanin tattalin arziki da kasuwanci da dangantakar ƙasashe na Jami'ar Europe.

An samu raguwar talaucin ne sakamakon karuwar arziki a ƙasashen yankin gabashi da kudancin Asiya, musamman ƙasashen China da Indiya.

"Ƙaruwar samun ayyuka da zuba jari a fannonin ilimi da lafiya da tsaro sun taimaka wajen bunƙasar tattalin arziki da rage talaucin'', in ji Farfesa Corrales.

Sai dai duka da raguwar talaucin da aka gani, muna fatan ba za mu ɗauke idanunmu kan mutum miliyan 831 da ke rayuwa cikin tsananin talauci a duniya.

Akwai fatan fitar da sauran talakawa daga halin da suke?

"Ƙwarai, akwai alamun da ke ƙarfafa gwiwar hakan,'' a cewar Farfesa Corrales, yana mai kafa hujjar cewa fiye da rabin al'ummar duniya na samun wani nau'i na kariya ko tallafi, wani abu da ya ce zai taimaka wa miliyoyin mutane ficewa daga ƙangin na talauci.

Masana sun ƙara da cewa zuba jari a fannin ilimi da lafiya za su taiamka matuƙa wajen rage yawan talakawan a duniya.

Sai dai wasu bayanai na nuna cewa idan ba a yi da gaske ba raguwa za ta tsaya ko ma adadin talakawan su ƙaru a 2030.

2. Ci gaban kimiyya a yaƙi da cutar kansa

Cutar kansa na daga cikin manyan cutukan da ke kan gaba a haifar da mace-mace a duniya.

A 2020 kaɗai cutar ta yi sanadin mutuwar kimanin mutum miliyan 10, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana.

Duk da cewa akan iya magance wasu nau'ikan cutar idan aka gano da wuri, a yanzu sauran nau'ikan ma an gano hanyoyin rage musu raɗaɗi.

Asibitin Johns Hopkins da ke Amurka, wanda ke da ƙwararun cibiyoyin bincike da ya kwashe tsawon shekara 125 yana bincike game da cutar ya ce a yanzu cutar kansa ''ba ta cikin cutuka masu hatsari''.

Dr. Dani Skirrow, ɗaya daga cikin masu binciek a cibiyar nazarin cutar kansa ta Birtaniya da ta fara aiki tun 1902 ya yarda da wannan iƙirari.

"Akwai hanyoyi masu yawa na magance kansa, musamman idan an gano ta da wuri'', kamar yadda ya shaida wa BBC.

Duk da cewa wasu ɗabi'u na rayuwa na taimakawa - kamar guje wa shan taba, da cin lafiyayyen abinci, da motsa jiki da sauran su - akwai hanyoyin magance cutar da aka gano.

Alal mkisali, Skirrow ya ce akwai riga-kafin da aka samar domin bai wa mutanen da ake tunanin za su kamu da wani nau'i na cutar.

3. Rayuwar ƙananan yara da dama fiye da baya

Ɗaya daga cikin manyan ci gaban da aka samu a fannin lafiya a cikin gomman shekarun baya-bayan nan shi ne raguwar mace-macen ƙananan yara.

A shekara 2022, aka kafa tarihin yawan raguwar mace-macen ƙananan yara, inda adadin ya gaza miliyan biyar a wannan lokacin, adadin da ba a taɓa gani ba a baya, kamar yadda Asusun tallafa wa ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya,Unicef ya bayyana.

Za ka fahimci haka idan ka duba shekartar 1990 inda yaro guda cikin 11 ne ke mutuwa kafin ya kai shekara biyar, saɓanin 2023 da yaro 1 cikin 27 ke mutuwa kafin kai wa shekara biyar.

A watan Maris na shekarar da ta gabata, UNICEF ya ce adadin ƙananan yaran da ke mutuwa a faɗin duniya kafin su kai shekara biyar a yanzu ba ya ɗaga wa duniya hankali.

Tun shekarar 2000 adadin ƙananan yaran da ke mutuwa kafin su kai shekara biyar ya ragu da kashi 52 cikin 100.

A ƙasashen Cambodia da Malawi da Mongolia da kuma Rwanda, raguwar ta kai kashi 75 cikin 100.

A 2022, an ƙiyasta samun mutuwar ƙananan yara - ƴan ƙasa da shekara biyar - 152,000 a ƙasashen yankin Latin da Karebiyan, wani abu da ke nuna raguwar matsalar da kashi 60 cikin 100, tun daga shekarar 2000.

An ɗauki matakai da dama don tabbatar da wannan nasara. ɗaya daga cikin matakan a cewar UNICEF da masana shi ne - samar da riga-kafi.

Haka kuma akwai inganta kiwon lafiyar mata masu juna biyu da kula da jarirai da ake yi bayan haihuwarsu.

4. Samun makamashin da baya gurɓata muhalli

"Makamashin da ba ya gurɓata muhalli na samun gagrumin ci gaba a faɗin duniya," a cewar rahoton Hukumar Kula da Makamashi ta Duniya (IEA) na 2025.

Wannan kyakkyawan labari ne ga ƙoƙarin duniya na rage iskar da ke gurɓata muhalli, wani muhimmin al'amari a yaƙin da ake yi da ɗumamar yanayi ta duniya, wanda a shekarun baya-bayan nan hatsarinsa ke cutar da miliyoyin mutane a faɗin duniya.

A duniya da ke cike da "ƙishirwar makamashi'', ana samar da sabbin fasahohi a fannin cikin sauri.

"Makamashin da ba ya gurɓata muhalli ya kafa sabon tarihi a 2024, bayan cika shekara 23 da kafuwa,'' a cewar rahoton.

An jima ana ƙarafaf duniya gwiwar samar da mafani da makamshin da ba ya gyur bata muhallai.

Gwamnatocin duniya da ƙungiyoyi da kamfanoni da dama sun ɓullo da hanyoyin samar wa kansu makamashin da ba ya gurɓata muhalli.

A tsakiyar shekarar 2025, aka inganta hanyar amfani da iska da hasken rana a matsayin hanyar samar da lantarki.

Duk da cewa hanyoyin da ake amfani da su sun bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, sabbin hanyoyin kamar amfani da hasken rana ''ya fi kowane hanya bunƙasa cikin sauri,,' a cewar hukumar IEA.

5. Zuwa makaranta ga yara mata

"A faɗin suniya, ƴara mata sun zarta maza yawan shiga makaranta da waɗanda ke fita daga makarantun,'' kamar yadda rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan jinsi na 'Panorama 2025' ya nuna.

A shekarar 2024 Bankin Duniya ya ce yana ƙirgi ci gaban ilimi cikin manyan nasarorin da duniya ta samu cikin shekara 50 da suka gabata.

"Yara mata, wadnada a baya ba su samun ilimi ko suke samun arancin ilimi saanin maza, a yanzu na samun ilimi mai sufi fiye da kowane lokaci a baya'', in ji rahoton.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma ce a shekarun baya-bayan nanan samu gagarumin ci gaba a sanya yara mata makarantun furamare da sakandire.

"Kodayake an kawar da bambancin shiga makarantu tsakanin jinsi a matakan asa, har yanzu akwai bambancin a makarantun gaba da sakandire musamman a yankunan uku cikin takwas na duniya."

A cewar UNICEF, yanzu haka akwai yara mata miliyan 119.3 da ba sa zuwa makaranta a duniya, kimanin ragin miliyan 124.7 idan aka kwatantan da shekarar 2015.

Yayin da ake samun nasarar kammala makarantun furamare da sakandire ga yaran mata, UNICEF ta kuma yi gargaɗin cewa bambancin da ake samu a makarantun gaba na zama barazana ga matan.

Asusun ya kuma bayar da misalin wani rahoton bincikensa a cikinwanda ya nuna cewa a 65 daga cikin wadannan ƙasashe matan kan zama malaman makarantun furamare da sakandire maimakon zama manyan malamai a jami'o'i.