Man City na son Alexander-Arnold, Liverpool ta tuntuɓi Alonso

Lokacin karatu: Minti 1

Manchester City na zawarcin ɗanwasan baya na Ingila Trent Alexander-Arnold yayin da ake ci gaba da samun rashin tabbas kan makomar danwasan mai shekara 27 a Real Madrid. (Teamtalk)

Liverpool ta tuntuɓi wakilan tsohon kocin Real Madrid Xabi Alonso yayin da rahotanni suka ce tsohon ɗanwasan ƙungiyar mai shekara 44 ya nuna haske ga buƙatar aikin. (AS - in Spanish)

Chelsea ta kira ɗanwasanta na Argentina Aaron Anselmino da ke taka leda a matsayin aro a Borussia Dortmund. (Athletic - subscription required)

Bournemouth na dab da kammala yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Vasco da Gama da Brazil Rayan, mai shekara 19. (Athletic - subscription required)

Lazio ta tura tayin fam miliyan 15 kan ɗanwasan tsakiya na Everton mai shekara 22 Tim Iroegbunam. (Football Insider)

Chelsea da Manchester United na sa ido kan ɗanwasan gaba na Rennes mai shekara 18 Mohamed Kader Meite. (Caughtoffside)

A ɗaya ɓangaren kuma Rennes ta yi watsi da tayin Chelsea a Janairu kan ɗanwasan baya Jeremy Jacquet. (Fabrizio Romano)

Golan Borussia Monchengladbach da Switzerland Jonas Omlin, mai shekara 32, da Sunderland ke nema ya koma Bayer Leverkusen a matsayin aro har zuwa ƙarshen kaka. (Florian Plettenberg, Sky Germany)