An gano gidajen yarin sirri na Daular Larabawa a Syria

    • Marubuci, Nawal Al-Maghafi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior international investigations correspondent
    • Aiko rahoto daga, Yemen
  • Lokacin karatu: Minti 7

BBC ta samu damar shiga wuraren da ake tsare mutane wanda ya kasance tsohon sansanonin soji na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a Yemen, abin da ya ƙara tabbatar da zargin da ake yi cewa UAE da sojojinta na ƙawance na tafiyar da wani gidajen yarin cikin sirri a Yemen.

Wani da aka taɓa tsarewa ya faɗa wa BBC cewa an lakaɗa masa duka da kuma cin zarafinsa a ɗaya daga cikin wuraren.

Mun ga gidajen yari biyu a kudancin ƙasar, ciki har da kwantenoni ɗauke da sunaye - waɗanda ake tsare mutane - har da ranakun wata a jiki.

UAE ba ta ce uffan ba lokacin da muka nemi martaninta, sai dai ta sha musanta irin waɗannan zarge-zarge.

Gwamnatin Yemen, wadda ke samun goyon bayan Saudiyya, na haɗin gwiwa da UAE wajen yaƙar ƴan tawayen Houthi da ke iko da arewa maso yammacin ƙasar, inda sai a baya bayan-nan ne al'amura suka sauya.

Sai dai alaƙar Yemen da ƙasashen biyu ya ruguje. Dakarun UAE sun fice daga Yemen a farkon watan Janairu sannan sojojin gwamnatin Yemen da ƙungiyoyi da ke alaƙa sun sake karɓe iko na wasu yankuna da dama da ke kudancin ƙasar a hannun ƴan aware da ke samun goyon bayar UAE.

Yankunan sun haɗa da tashar jirgin ruwa ta Mukalla, inda muka sauka daga jirgin soji mallakin Saudiyya sannan aka ɗauke mu zuwa ziyara tsoffin sansanonin soji na UAE da ke yankin Al-Dhaba.

Yana da matukar wahala ƴan jarida daga ƙasashen waje su samu bizar bayar da rahotanni daga Yemen a shekarun baya bayan-nan, sai dai gwamnatin ƙasar ta gayyaci ƴan jarida su je su ga wuraren biyu, tar da rakiyar ministan yaɗa labarai Moammar al-Eryani.

'Babu wurin kwanciya'

A ɗaya daga cikin wuraren, akwai kwantenoni 10, sannan an yi wa cikinsu bakin fanti.

Sakonnin da ke bangonsu na ɗauke da rubutun kwanan wata na lokacin da aka kai waɗanda ake tsare, ko kuma ƙirga kwanakin da suka shafe a tsare.

Ranakun watan ya nuna cewa an tsare mutane da dama a watan Disamban 2025.

A wani sansanin soji, an nuna wa BBC wuraren tsare mutane guda takwas waɗanda aka gina da sumunti, ciki har da waɗanda tsawonsu bai fi mita ɗaya ba da mita biyu, wanda Eryani ya ce ana amfani da su wajen tsare mutane ɗaya-ɗaya.

Ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun naɗi bayanan mutane da suka kwatanta yadda wuraren suke a tsawon shekaru.

Wata lauya a Yemen Huda al-Sarari ta shafe lokaci tana tattara bayanai.

BBC ta halarci wani taro da ta shirya, inda mutum 70 da suka je taron suka ce an tsare su a Mukalla, da kuma wasu iyalai 30 da suka ce har yanzu ana tsare da ƴan uwansu.

Tsoffin mutane da aka tsare da dama sun faɗa mana cewa kowane kwantena ɗaya zai ɗauki maza kusan 60 a lokaci guda.

Sun ce an rufe wa fursunoni fuska, da ɗaure musu kwankwaso sannan a tilasta musu zama na tsawon lokaci.

"Babu wurin kwanciya," kamar yadda wanda aka taɓa tsarewa ya faɗa wa BBC. "Idan mutum ya faɗi, sauran mutane ne ke ƙoƙarin riƙe shi."

'Babu irin uƙubar da ba a yi'

Mutumin ya faɗa wa BBC cewa an yi ta lakaɗa masa duka har na tsawon kwanaki uku bayan kama shi, inda masu bincike suka buƙaci ya amsa cewa shi mamban al-Qaeda ne.

"Sun faɗamin cewa idan ban amsa ba, za a tura ni 'Guantanamo'," in ji shi, inda yake magana gidan yarin Gauntanamo Bay a Cuba.

"Ban san me suke nufi da Guantanamo ba har sai da suka kai ni gidan yarinsu. Kafin nan na fahimta."

Ya ce an tsare shi a wurin na tsawon shekara ɗaya da rabi, babu abin da ake yi masa sai duka a kowace rana da kuma cin zarafi.

"Ba su ba mu isasshen abinci," in ji shi. "Idan kana son zuwa bahaya, sau ɗaya za a kai ka. Wasu lokutan ma a jikinka za ka yi bahaya idan ka matsu."

Ya ce waɗanda suka kama shi sun hada da sojonin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma mayaƙan Yemen: "Babu irin uƙubar da ba a yi mana - abin ya fi muni idan ana yi mana tambayoyi. Har ta kai suna mana cin zarafi na lalata sannan sai su kawo wani likita.

"Wannan likita ɗan ƙasar UAE ne. Yana mana duka sannan ya faɗa wa sojojin Yemen su ma su lakaɗa mana duka. Na yi koƙarin kashe kaina sau da dama domin kawo karshen lamarin."

UAE na jagorantar wani shiri na yaƙi da mayaƙa a kudancin Yemen, sai dai ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam sun ce an tsare dubban mutane a lokacin da aka yi kame kan masu gwagwarmaya da masu suka.

Wata mahaifiya ta faɗa mana cewa an tsare ɗanta tun yana karami inda ya shafe shekara tara a tsare.

"Ɗana ɗan wasan tsere ne," in ji ta. "Bai daɗe da dawowa daga gasa a kasar waje ba. Ranar ya fita zuwa motsa jiki daga nan bai sake dawowa ba."

"Ban ji daga gare shi ba na tsawon watanni bakwai," in ji mahaifiyar.

"Sun ba ni damar ganinsa na minti goma. Na ga jikinsa da raunuka daban-daban saboda azaba."

Ta yi zargin cewa an saka wa ɗanta lantarki a gidan yarin da UAE ke gudanarwa, da zuba masa ruwan ƙanƙara har ma da cin zarafin lalata sau da dama.

Ta ce ta halarci wata shari'a inda waɗanda ke zargin ɗanta suka saka wata muryar yaron yana magana.

"Za ka ji ana yi masa duka da kuma faɗa masa abin da zai ce," in ji mahaifiyar.

"Yarona ba ɗan ta'adda bane. Kun cuce shi ta hanyar ɓata masa shekarunsa a tsare."

Zarge-zarge

A tsawon shekaru goma da suka wuce, ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam da kafafen yaɗa labaru - ciki har da BBC da AP - sun naɗi zarge-zarge na tsare mutane ba tare da laifi ba, ɓatar da mutane da kuma cin zarafin mutane a cibiyoyin tsarewa wanda UAE da ƙawayenta ke tafiyarwa.

Human Rights Watch ta ce a 2017 ta tattara bayanai na waɗanda aka tsare ba tare da aikata laifi ba, inda aka gana musu azaba, ciki har da saka musu wutar lantarki a jiki da kuma duk na'ukan cin zarafi.

UAE ta musanta waɗannan zarge-zarge.

BBC ta aika wa gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa waɗannan zarge-zarge na mallakar cibiyoyin tsare mutane da muka kai ziyara, sai dai babu wani martani.

An zargi dukkan ɓangarori da take hakkin ɗan'adam a yaƙin basasar Yemen, wanda ya ɗaiɗaita mutane da janyo ƙaruwar bukatar jin-ƙai a ƙasar.

Tambayoyin iyalai

Iyalan waɗanda aka tsare sun faɗa wa BBC cewa sun sha faɗa wa hukumomin Yemen halin da ake ciki.

Sun yi imanin cewa yana da wuya UAE da ƙawayenta su tafiyar da wurin tsare mutane ba tare da gwmanatin Yemen ko Saudiyya sun sani ba.

Ministan yaɗa labaru, Eryani, ya ce: "Ba mu samu damar gano wuraren da UAE ke iko da su ba sai yanzu.

"Lokacin da aka saki mutanen mun gano waɗannan gidajen yari... mutanen da lamarin ya shafa da dama sun faɗa mana cewa gidajen yarin sun daɗe sai dai ba mu amince cewa da hakan ba."

Matakin da gwamnatin Yemen ɗin ta ɗauka na barin kafafen yaɗa labaru na ketare su shiga ƙasar na zuwa ne yayin da saɓani tsakanin Saudiyya da UAE ke ƙara wanzuwa.

Tsamin dangantakarsu ta ƙara lalacewa ne a watan Disamba lokacin da ƴan awaren kudanci waɗanda ke samun goyon bayan UAE, suka ƙwace iko da yankin da ke hannun dakarun gwamnati a wasu larduna biyu.

Saudiyya ta kai hare-hare kan abin da ta kira yunkurin shigar da makamai daga UAE zuwa Yemen, sannan ta goyi bayan buƙatar shugaban ƙasar Yemen na ganin sojojin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun fice daga ƙasar cikin gaggawa.

UAE ta janye kuma a cikin kwanaki kalilan dakarun gwamnati da ƙawayenta suka sake karɓe iko da larduna da ke yammaci da kuma na kudanci.

Sai dai, ƴan awaren da suka rage sun yi barazanar tumɓuke gwamnati a wuraren da suke, ciki har da tashar jiragen ruwa na Aden.

UAE dai ta musanta cewa akwai makamai a cikin kayakin da ta kai Yemen.

Har yanzu mutane na 'tsare'

A ranar 12 ga watan Janairun 2026, shugaban majalisar gwamnatin Yemen, wanda ke duba ayyukan gwamnati, Rashad al-Alimi, ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen yarin da ba sa kan ka'ida da ke kudancin ƙasar, da buƙatar sakin duk waɗanda aka tsare nan take.

Ministan yaɗa labarun ya ce an gano wasu daga cikin mutane da aka tsare a gidajen yarin, sai dai bai ba da alkaluma ko karin bayani ba.

Wasu ƴan uwa - ciki har da mahaifiyar ɗan wasan tsere - sun faɗa wa BBC cewa tuni aka sauya wa waɗanda ake tsare da su wuri zuwa gidajen yarin da ke karkashin ikon gwamnati.

Hukumomin Yemen sun ce sauya wa fursunoni wuri zuwa tsarin shari'a da aka amince da shi yana da tsarkakiya, yayin da ƙungiyoyin kare hakkin ɗan'adam suka yi gargaɗin cewa za a ci gaba da tsare mutanen da ba su aikata laifi ba ta wata hanyar daban.

"Ƴan ta'adda na can suna yawo kan tituna," in ji mahaifiyar ɗan wasan tsere.

"Ƴaƴanmu ba ƴan ta'adda ba ne."