Dusar ƙanƙara ta mamaye Amurka ta katse wutar lantarki
Ana ci gaba da fuskantar tsananin sanyi da zubar dusar kankanra a sassan Amurka inda aka samu daukewar wutar lantarki a wurare da dama da kuma soke tashi da saukar jirage dubu 11.
Kusan gidaje da wuraren kasuwanci miliyan guda basu da wutar lantarki.
Yanayin tsananin sanyi ya faro ne daga New Mexico zuwa Maine inda aƙalla a yanzu jihohin kasar 23 sun ayyana dokar ta baci.
Jihohin da ke kudu maso gabashin ƙasar na shirin fuskantar mummunan yanayi na sanyi inda aka yi hasashen zubar dusar kankara mai yawan gaske a wasu yankuna na jihohin.
Masu hasashen yanayi sun ce za a shafe kwanaki ana fuskantar tsananin sanyin sannan kuma zai haddasa asara da dama.