'Sun girke bindiga a kan titi suna ɓarin wuta': Abin da muka sani kan sace mutane a Mafara

Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomi a jihar Zamfara, mai fama da matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar da sace mutum 26 a wasu hare-hare da ƴan bindiga suka kai kan ƙauyuka biyu na ƙaramar hukumar Talatar Mafara a ƙarshen mako.

Talatar Mafara na daga cikin ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar, inda a shekarar 2021 ƴan bindiga suka sace ɗaliban makarantar mata ta Jangebe, kimanin 300.

A tattaunawa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara, Yahaya Yari Abubakar ya ce ƴan bindigar sun kai hare-hare biyu a cikin ƙarshen mako.

"Shekaran jiya an shiga wani ƙauye mai suna Matuna, inda suka ɗauki mutum uku suka kuma kashe mutum ɗaya," a cewar Yari Abubakar.

Ya ƙara da cewa "sai suka sake dawowa suka sake kai hari a wani ƙauye da ake ce wa Tashar Kuturu, suka ɗauki mutum 23 kuma suka harbi wani mutum a hannu da kafa, mun kai shi asibitin cikin garin Jangebe ana nema masa lafiya."

A ranar Litinin ne rahotanni suka ɓulla kan cewa wasu ƴan bindiga sun kai hari tare da sace mutane da dama waɗanda aba a ƙididdige yawansu ba.

Yadda aka kai hari a Tashar Kuturu

Bayanai sun nuna cewa maharan sun kai harin ne da tsakar dare, inda suka buɗe wuta domin firgita al'umma, kuma mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kwashe kimanin awa biyu suna addabar su.

A tattaunawar sa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Talatar Mafara Yahaya Yari Abubakar ya ce maharan "sun je da babura da manyan makamai, sun ajiye wata bindiga da suke kafawa a ƙasa mai ƙafa uku, suka ajiye ta a tsakiyar titi suka dinga harbawa saboda tsorata mutane, saboda duk abin da suka ce a ayi, a yi."

Ya bayyana cewa maharan sun kora mutane ne wasu a ƙasa wasu kuma a kan babura.

"Sun haɗa da maza da mata da ƙananan yara."

A baya-bayan nan ƴan bindiga sun matsa ƙaimi wajen kai hare-hare a jihohin arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashewa da kuma sace mutane domin karɓar kuɗin fansa.

A makon da ya gabata ne wasu ƴan bindiga sun kai hari a Kajuru da ke jihar Kaduna inda suka sace masu ibada kimanin 170 a ƙauyen Kurmin Wali, inda duk da cewa wasu sun tsero, amma har yanzu akwai mutum 160 waɗanda ba a san halin da suke ciki ba.

Haka nan a cikin watan Nuwamban 2025 wasu mahara suka kai hari kan Makarantar Sakandiren Ƴanmata da ke garin Maga a jihar Kebbi, inda suka kashe mai gadi da sace ɗalibai 25.

Jim kaɗan bayan haka wasu ƴan bindigan suka kai hari a wata makaranta da ke ƙauyen Papiri a jihar Neja inda suka sace ɗalibai da malamai kusan 200.

Hukumomi a Najeriya na cewa suna ƙoƙari wajen magance matsalar, sai dai har yanzu ƴan bindigar na ci gaba da kai irin wadannan hare-hare waɗanda ke janyo salwantar rayuka da dukiya.

Lamarin ya haifar da durkushewar ayyukan tattalin arziki a yankin, inda manoma da dama ke gudun hijira, wasu kuma ba su iya noma kamar yadda suka saba yi a baya.