Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mece ce cutar Nipah mai kisan mutane kuma yaya take?
Hukumomi na ta ƙoƙarin yaƙi da yaɗuwar cutar Nipah bayan ɓarkewar annobar a wasu garuruwa da ke jihar West Bengal na ƙasar India.
Tuni aka killace kusan mutum 110 bayan masu ɗauke da cutar guda biyu sun yi jinya a asibitocin jihar a farkon wannan watan na Janairu.
Yawanci sun haɗu da waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, amma bayan gwaji, sai aka ga ba sa ɗauke da ita.
Cutar, wadda take da matuƙar haɗari, tana yaɗuwa ne daga dabbobi zuwa ga mutane, kuma zuwa yanzu ba ta da takamaiman magani, ballantana riga-kari.
Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ayyana cutar, tare da Ebola da Zika da Covid-19 a matsayin cututtuka da suke buƙatar bincike na musamman domin kare duniya shiga wata annoba.
Ya haɗarin cutar, kuma mene ne alamominta?
Yaya ake yaɗa cutar Nipah?
Nipah cuta ce mai saurin yaɗuwa, kuma tana cikin cututtukan da ke yaɗuwa tsakanin dabbobi zuwa ga mutane.
Jemage da aladu na cikin dabbobin da suke yaɗa cutar ga mutane, kamar yadda ƙungiyar lafiya ta duniya wato WHO ta bayyana.
Haka kuma za a iya yaɗa cutar ta cikin gurɓataccen abinci, sannan wanda ya kamu da ita zai iya yaɗa ta zuwa ga wani.
Yawanci ana samu ɓarkewar cutar ne kusan duk shekara a yankin Asia, musamman a ƙasashen Bangladesh da India.
Sannan kuma sha ko cin kayan lambu da fitsari ko yawun mai cutar ya taɓa zai iya yaɗa cutar, amma dai jemage ce dabbar da ta fi yaɗa ƙwayar cutar.
Mene ne alamomin cutar?
Akwai waɗanda ba sa nuna alamar cutar, akwai waɗanda ake ganin alamu kaɗan, kamar zazzaɓi, da kuma waɗanda suke girgiza sosai kamar kumburin jiki da fuska.
Da farko dai waɗanda suka kamu da cutar, suna fara fuskantar zazzaɓi da ciwon kai da raɗaɗin jiki da amai da bushewar maƙogoro.
Daga nan kuma sai rashin kuzari da shiga ruɗu da sauransu.
Wasu kuma cutar na janyo musu matsalolin numfashi kamar wanda ke ɗauke da cutar sarƙewar numfashi ta pneumonia da kumburin ƙwaƙwalwa, sannan a kan samu farfaɗiya, wanda kan jawo dogon suma a cikin kwana ɗaya zuwa biyu.
Kwanakin da cutar ke ɗauka kafin a fara ganin alamominta suna kai tsakanin kwana 1 zuwa kwana 14.
Amma an taɓa samun lokacin da cutar ba ta bayyana ba sai bayan kwana 45.
Cutar tana kashe kusan kashi 75 na waɗanda suka kamu da ita.
Shin akwai riga-kafi?
Har yanzu babu riga-kafi ko magani. Ana mayar da hankali ne wajen magance alamomin cutar da suka fito.
Wuraren da aka samu ɓarkewar cutar a baya
Ɓullar cutar ta farko ta yi ajalin sama da mutum 100 a Malaysia, wanda hakan ya sa aka kashe aladu kusan miliyan 1 domin taƙaita yaɗutar cutar.
An sanya wa cutar sunan ƙauyen da ta fara ɓulla ne a shekarar 1999.
Daga baya ta ɓulla a Singapore, inda aka samu mutum 11 da suka kamu, sannan mutum 1 ya rasu a cikin wasu ma'aikatan wata mayanka da suka yi aikin gyara naman aladu a Malaysia.
Amma dai Bangladesh ta fi shiga matsala a baya-bayan nan, inda sama da mutum 100 suka mutu a Nipah daga 2011 zuwa yanzu.
Haka kuma an samu ɓullar cutar a India.
An samu ɓullar cutar a jihar Kerala ta kudancin India a 2018 da 2023.
Sauran ƙasashen da ke fuskantar barazanar ɓullar cutar sun haɗa da Cambodia da Ghana da Indonesia da Madagascar da Philippines da Thailand, kamar WHO ta bayyana.