'Mozambique ta fuskanci ambaliya mafi muni a bana a shekara 25'
Hukumomi a Mozambique sun bayyana cewa ambaliyar ruwa mai tsanani da ta afka wa sassan ƙasar tun daga ranar 7 ga Janairu ita ce mafi muni a shekara 25.
Ambaliyar ta kashe aƙalla mutum 18, ta tilasta wa kimanin mutum 392,000 barin muhallansu, yayin da kusan mutum 780,000 ne ambaliyar ta shafa a faɗin ƙasar tun bayan fara damina a watan Oktoban 2025, a cewar gwamnati da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Jihohin Gaza da Maputo da Sofala ne ambaliyar ta fi shafa inda gidaje da makarantu da cibiyoyin lafiya da hanyoyi da wutar lantarki suka lalace matuƙa.
Hukumar kula da bala’o’i ta ƙasa (INGD) ta yi gargaɗin cewa adadin mutanen da ambaliyar ta shafa na iya kai wa miliyan 1.1, tana mai kiran lamarin mafi muni cikin shekaru fiye da ashirin.
Manyan koguna irin su Limpopo da Incomati da Save sun cika tam inda suka yi ambaliya, lamarin da ya katse al’umma da dama tare da haifar da ƙarancin abinci da man fetur.
Rahotanni sun nuna cewa fiye da gidaje 150,000 da cibiyoyin lafiya 242 da makarantu sama da 575 sun nutse, yayin da sama da hanyoyin kilomita 5,000 sun lalace, ciki har da rushewar wasu sassan babbar hanyar da ke haɗa arewa da kudu.
Shugaban ƙasar, Daniel Chapo, ya tura jami’an agaji da sojoji da motocin gwamnati domin kai ɗauki, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin jin ƙai.