Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 29 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed, Aisha Babangida da Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Da haka muka zo ƙarshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Sojoji sun jagoranci mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya gida daga Kamaru

    Sojoji

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Rundunar Sojin Najeriya a karkashin operation haɗin kai ta sanar da jagorantar dawowar ‘yan gudun hijirar Najeriya daga Jamhuriyar Kamaru zuwa Jihar Borno cikin tsaro.

    A cewar sanarwar da ta fitar, a ranar 27 ga Janairu, 2026, sojojin tare da hadin gwiwar dakarun ƴan sa kai ta CJTF da ‘yan banga na gari sun samar da cikakken tsaro yayin da ‘yan gudun hijirar ke ƙetare iyaka daga Kirawa zuwa garin Pulka a ƙaramar hukumar Gwoza.

    Wasu daga cikin wadanda suka dawo sun shafe sama da shekaru 11 a gudun hijira sakamakon rikicin ‘yan ta’adda.

    Aikin dawo da ‘yan gudun hijirar ya fara ne daga Minawawu a Kamaru zuwa Moruwa kafin shiga Kirawa a Najeriya.

    An gudanar da aikin bisa ƙa’idojin jin kai da tsaro, tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Kasa da gwamnatin jihar Borno da sauran hukumomin tsaro.

    Wata babbar tawaga daga gwamnatin jihar karkashin jagorancin Wakilbe, wakilin gwamna Babagana Umara Zulum, ta halarci taron tare da wakilan UNHCR da IOM.

    Kwamandan dakarun ƴan sa-kai ta CJTF, Birgediya Janar Nasiru Abdullahi ne ya tarbe su kafin a raka su zuwa cibiyar karɓar baƙi a Pulka.

    A can ne aka yi musu rijista inda aka raba musu tallafi da suka hada da kuɗade da tabarma da gado daga gwamnatin Borno da kayan abinci daga gwamnatin tarayya, da kuma tallafin kudi daga UNHCR.

    Rundunar Sojin ta tabbatar da cewa aikin ya gudana lafiya ba tare da wata matsala ba.

  3. Zazzaɓin Lassa ya hallaka mutum guda a Jigawa

    Lassa

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin lafiya a jihar Jigawa sun tabbatar da mutuwar wani mutum sanadiyar cutar zazzaɓin Lassa.

    An kuma killace tare da sa ido kan mutum fiye da 20 waɗanda suka yi mu’amala da marigayin, don daƙile yaɗuwar cutar.

    Masana sun bayyana cewa cutar ta samo asali ne daga wani nau’in ɓera wadda ke haɗa zazzaɓi mai zafi da amai da kuma fitar jini ta kafofin jikin mutum.

  4. Sojin Isra'ila sun ce an kashe Falasɗinawa 70,000 a yaƙin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafar yaɗa labarai na Isra'ila ta ruwaito cewa wata babbar majiya a fannin tsaron ƙasar ta ce rundunar sojin Isra'ila ta amince cewa an kashe Falasɗinawa kusan 70,000 a yaƙin Gaza.

    Tun da fari, Isra'ila ta ƙi amincewa da alƙaluman da ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin da Hamas ke jagoranta ta fitar.

    Majiyar ta shaida wa ƴan jarida cewa adadin da Hamas ta bayar na mutum fiye da 71,000 da suka mutu, ya kusa zuwa dai-dai da wanda Isra'ila ta samu.

    Sai dai, ta ce har yanzu rundunar sojin Isra'ilar ba ta tabbatar da su wanene mayaƙa ba, su wanene ne kuma yaƙin ya rutsa da su.

  5. Turai ta ayyana dakarun juyin-juya hali na Iran a matsayin ƴan ta'adda

    IRGC

    Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EP

    Ministocin harkokin wajen ƙasashen Turai sun amince da ayyana dakarun juyin-juya hali na Iran a matsayin ƙungiyar ƴan ta'adda, a matsayin martani ga yadda suka murkushe masu zanga-zangar da aka yi.

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta kuma sanya takunkumi kan wasu manyan shugabannin Iran, ciki har da ministan harkokin cikin gida da babban mai shigar da ƙara na ƙasar.

    Babbar jami'ar diflomasiyya ta ƙungiyar Tarayyar Turai, Kaja Kallas, ta ce duk wata gwamnati da za ta kashe dubban mutanen ta, tana kan hanyar ruguje wa.

    Da aka tambaye ta ko akwai yiwuwar Amurka ta kai wa Iran hari, Miss kallas ta ce yankin ba ya buƙatar wani yaƙin.

  6. NNPP ta soki masu kiran cewa mataimakin gwamnan Kano ya ajiye aiki

    Aminu da Abba

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

    Jam'iyyar NNPP ta yi Alla-wadai da kalaman kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, wanda ya buƙaci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye aikinsa.

    Wata sanarwa da kakakin jam'iyyar a jihar Kano, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce har yanzu kundin tsarin mulki ya bai wa mataimakin gwamnan ci gaba da riƙe mukaminsa.

    Kalaman kwamishinan yaɗa labaran na zuwa ne bayan da mataimakin gwamnan ya ki bin gwamna Abba Kabir Yusuf tare da wasu muƙarrabai sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC, inda NNPPn ta ce Abdussalam na da ikon ci gaba da gudanar da ayyukansa saboda sun yi takara tare gwamnan jihar.

    Jam'iyyar ta buƙaci ɓangaren zartaswa a jihar da ya daina shiga al'amuran siyasa, ya tsaya kan ayyukan da kundin mulki ya ba shi damar aiwatarwa.

    "Ci gaba da aikin mataimaikin gwamna yana da muhimmanci wajen ɗorewar shugabanci a jihar Kano," in ji sanarwar NNPP.

    Jam'iyyar ta ƙara da cewa kwamishinan yaɗa labaran ba ya nan lokacin da ake gwagwarmayar kafa gwamnati, don haka ya ja bakinsa ya yi shiru.

  7. Ministan wajen Iran zai tattauna da takwaransa na Turkiyya don shawo rikicinsu da Amurka

    Abbas Araqchi

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, zai gana da takwaransa na Turkiyya, Hakan Fidan a gobe Juma'a, bayan Turkiyyar ta ce za ta shiga tsakani domin shawo kan rikicin da ke tsakanin Tehran da Washington.

    Wata majiya a ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya ta ce Mista Fidan zai nanata matsayar ƙasar sa ta ƙin amincewa da duk wani harin soji a Iran, tare da gargaɗin cewa yin hakan zai kasance babbar barazana.

    Gwamnatin Rasha ma ta ce tana ganin har yanzu akwai damar hawa teburin tattaunawa, a yayin da ake samun rahotannin cewa jam'ian fannin tsaro da tattara bayanan sirri na Saudiyya da Isra'ila sun gana da takwarorinsu na Amurka a wannan makon.

    Shugaban sojin Iran ya yi alwashin mayar da martani ga duk wani hari da aka kai musu, bayan shugaba Trump ya yi gargaɗin cewa lokaci yana ƙure musu.

  8. 'Ya kamata mataimakin gwamnan Kano ya yi murabus'

    ...

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

    Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya shawarci mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, da ya yi murabus daga muƙaminsa sakamakon rashin bin gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa jam’iyyar APC.

    Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Alhamis, inda ya ce tafiyar da mulki na buƙatar cikakken aminci da fahimtar juna tsakanin shugabanni.

    Ya bayyana cewa "Ci gaba da halartar tarukan majalisar zartarwa daga wanda ba ya tare da gwamnati a siyasance na iya zama barazana ga sirrin gwamnati."

    “Ra'yinsa ne rashin bin gwamna Abba zuwa APC, amma babu yadda za a yi wanda ba ya tare da kai ya ci gaba da halartar tarukan majalisar zartarwa,” in ji kwamishinan.

    “Wa ya san wanda zai iya bayyanawa muhimman bayanan gwamnati? Mulki yana tafiya ne bisa amana, kuma ba za ka iya yarda da wanda ba ya tare da kai ba.”

    Waiya ya ƙara da cewa, a ganinsa, murabus shi ne mataki mafi dacewa kuma mai mutunci da mataimakin gwamnan zai ɗauka a irin wannan hali.

    “Da ni ne, da na yi murabus cikin da kaina,” in ji shi.

    Maganganun kwamishinan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun sauye-sauyen siyasa a Kano, ciki har da sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.

  9. Kamfanin jirgin saman Ethiopia ya soke tashin jirage zuwa arewacin Tigray

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kamfanin jirgin sama na Ethiopian Airlines ya soke tashin jirage daga Addis Ababa zuwa filayen jiragen sama da dama a yankin arewacin Tigray, a yayin da aka soma samun tashe-tashen hankula.

    Rahotannin da aka samu a farkon makonnan na cewa an samu arangama tsakanin dakarun gwamnati da mayaƙan ƙungiyar Tigray.

    An cewa ma'aikatan filayen jiragen sama kar su zo aiki a yau, fasinjoji kuma an aika musu saƙonni kar ta kwana cewa an soke tashin jiragensu.

    Wani mazaunin babban birnin Tigray, Mekelle, ya ce ɗaruruwan mutane sun yi layi a yau suna ƙoƙarin cire kuɗi a banki, amma bankuna da dama ba su da takardun kuɗin.

  10. Majalisar dattijan Najeriya ta fara nazari kan gyaran dokar zaɓen ƙasar

    ...

    Asalin hoton, @NgrSenate

    Majalisar dattijan Najeriya ta fara nazari kan ƙudirin gyara dokar zaɓen ƙasar ta 2022 inda ta mayar da hankali kan wasu sassa da ake ganin suna buƙatar ƙarin gyara domin inganta zaɓe a ƙasar.

    Ƴan majalisar sun yi hakan ne ta hanyar fara nazarin wasu takardu da gyare-gyaren da shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Harkokin Zaɓe, Sanata Simon Lalong, ya gabatar, kafin a ci gaba da muhawara a bainar jama’a.

    Ƙudirin ya ƙunshi batutuwa kamar hana yin rajista a jam’iyyun siyasa fiye da ɗaya, daƙile sauya sheƙa bayan zaɓen fidda gwani, da kuma tanadin hukunci ga masu karya doka.

    A zaman majalisar, ‘yan majalisar sun amince da buƙatar janye wasu sassan ƙudirin da aka riga aka amince da su a watan Disambar 2025, domin a sake duba su.

    Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya jaddada muhimmancin yin nazari mai zurfi kan ƙudirin, duk da cewa Majalisar Wakilai ta riga ta amince da shi.

    Ya ce dokar na da matuƙar muhimmanci musamman yayin da ake shirin zaɓe, don haka dole ne a yi taka-tsantsan domin kauce wa rikice-rikicen shari’a bayan zaɓe.

    Kwamitin Majalisar Dattawa ya bayyana cewa aiwatar da dokar zai ƙarfafa gaskiya a tsarin zaɓe, da ƙara amincewar jama’a, tare da faɗaɗa damar masu kaɗa ƙuri’a da kuma ƙarfafa ƙarfin hukumar zaɓe ta INEC wajen hana maguɗin zaɓe.

  11. An tsaurara tsaro a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An tsaurara matakan tsaro a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, bayan shafe awa biyu ana harbe-harben bindiga a filin jirgin sama na birnin.

    Kawo yanzu gwamnatin mulkin sojin ƙasar ba ta ce uffan kan harin ba, amma ana ta yaɗa jita-jitar wataƙil an yi yunkurin juyin mulki ne, ko samame kan 'yan bindiga.

    Mazauna unguwannin da ke kusa da filin jirgin sun shaida wa manema labarai cewa wani ƙara mai ƙarfi ne ya tayar da su, sannan aka shafe tsawon lokaci ana ta harbe-harbe.

    Babu wanda aka bayyana cewa ya jikkata ko kuma hasarar rai, kuma babu wasu gine-gine ko dukiya da aka lalata.

    Filin jirgin dai shalkwatar sojojin haɗin gwiwa na kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso ne, waɗanda ke yaki da masu ikirarin jihadi.

  12. Sojoji sun lalata maɓoyar masu sace mutane tare da ceto wasu a Kaduna

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta na operation enduring peace sun lalata wata maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da ceto mutum takwas a dajin Badurum Kasa da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna

    Rundunar ta ce sojojin sun samu wannan nasarar ne a yayin wani samame da suka kai a wurin maɓoyar.

    Samamen ya gudana ne a ranar 28 ga Janairun 2026, bayan samun sahihin bayanan sirri kan inda masu laifin ke ɓoye.

    A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, sojojin sun kai samamennne cikin gaggawa tare da haɗin gwiwar rundunar ƴansandan Zango Kataf da dakarun sa kai ta CJTF da masu gadin daji da kuma mafarauta inda suka kutsa cikin dajin domin kama masu garkuwar.

    Sojojin sun yi arangama da masu garkuwa da mutanen inda wasu suka tsere suka bar waɗanda suka sace a baya lamarin da ya sa sojojin suka yi nasarar ceto mutane takwas.

    An haɗa mutanen da aka ceto su da iyalansu.

  13. ECOWAS ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Guinea

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika wato ECOWAS ta amince da ɗage dukkan sauran takunkuman da ta ƙaƙaba wa ƙasar Guinea bayan kammala miƙa mulki, lamarin da ke nuna cikakken dawowar ƙasar cikin harkokin ƙungiyar yankin.

    An cimma wannan matsaya ne a yayin taron shugabannin ƙasashe da gwamnatocin ECOWAS da aka gudanar a ƙasar Saliyo, bayan kammala miƙa mulkin siyasa a ƙasar, kamar yadda gidan jaridar Africaguinee mai zaman kanta ta ruwaito.

    ECOWAS ta bayyana cewa an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a ranar 28 ga Disamba, 2025, kuma an miƙa mulki bisa doka ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mamadi Doumbouya.

    A cewar rahoton, shugabannin yankin sun lura cewa wannan miƙa mulki ya samar da yanayi mai kyau na dawo da dimokuraɗiyya da mutunta doka da oda a Guinea.

    ECOWAS ta taɓa dakatar da Guinea tare da ƙaƙaba mata takunkumi ne bayan juyin mulkin da aka yi a 2021, wanda Mamadi Doumbouya, a wancan lokaci soji, ya jagoranta, inda aka kifar da tsohon shugaban ƙasa Alpha Condé.

  14. ’Yansanda sun bankaɗo masu satar katin waya ta intanet

    ...

    Asalin hoton, NPF

    Rundunar ƴansandan Najeriya tare da haɗin gwiwar cibiyar yaƙi da laifukan intanet ta ƙasa (NPF–NCCC) ta bayyana cewa ta bankaɗo wata babbar ƙungiyar masu satar katin waya ta intanet da ta haddasa asarar kuɗi da ta haura naira biliyan 7.7.

    ’Yan sandan sun ce ƙungiyar na karkatar da katin waya da bayanan intanet na wani kamfanin sadarwa ta haramtacciyar hanya.

    Rundunar ce ta sanar da hakan a shafinta na X.

    Hakan ya biyo bayan ƙorafin da wani kamfanin sadarwa a Najeriya ya shigar, inda ya lura da wasu ayyuka na zamba da ba a amince da su ba a tsarin biyan kuɗaɗe da lissafin kamfanin.

    Binciken ’yansanda ya nuna cewa an sace bayanan wasu ma’aikatan kamfanin ne lamarin da ya bai wa masu laifin damar shiga muhimman tsarin kamfanin ba tare da izini ba.

    Bayan makonni na shiri da bincike, ’yansanda sun gudanar da samamen kama mutane a jihohin Kano da Katsina a watan Oktoban 2025, tare da wani kama ƙarin wasu da ake zargi a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

    A yayin wannan aiki, an kama mutum shida da ake zargi.

    Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun waɗanda ake zargin sun haɗa da gidaje biyu a Kano, ƙananan kantuna biyu, shagunan sayar da wayoyi da kwamfutoci da ke ɗauke da sama da kwamfutoci 400 da wayoyi 1,000.

    Haka kuma, an gano kuɗaɗe masu yawa a asusun bankin waɗanda ake zargin wanda ƴansanda suka kyautata zaton cewa kuɗaɗe an same su ne ta hanyar aikata laifin.

    ’Yan sanda sun ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

  15. Sojojin Sudan ta Kudu sun kai farmaki a yankunan da ke hannun ƴan adawa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babbar ƙungiyar da ke adawa da gwamnati a Sudan ta Kudu, SPLM-IO, ta ce sojojin gwamnati sun kai farmaki a yankunan da ƙungiyar ke iko da su a jihar Jonglei da ke gabashin ƙasar, lamarin da ya haddasa mummunan faɗa tsakanin ɓangarorin biyu.

    Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa rikicin na iya yin tasiri mai girma ga faɗace-faɗacen da za su biyo baya a nan gaba, tana mai cewa artabun da ake yi a halin yanzu na iya zama shi ne zai yanke wannan hukuncin.

    Kakakin SPLM-IO, Pal Mai Deng, ya shaida wa BBC cewa sojojin gwamnati ne suka fara kai farmaki, inda ake fafatawa da ƙarfi a Yuai, hedikwatar ƙaramar hukumar Uror.

    Ya ce faɗan ya fara ne tun ranar Laraba, yana mai bayyana shi a matsayin “mummunan artabu na soji”.

    Deng ya ƙara da cewa sakamakon wannan faɗa na iya tantance makomar rikice-rikicen da za su biyo baya tsakanin ɓangarorin.

    Sai dai rundunar sojin Sudan ta Kudu ta yi watsi da wannan iƙirari, tana mai cewa faɗar ba za ta yanke hukuncin makomar rikicin ba.

    Kakakin rundunar sojin, Manjo Janar Lul Ruai Koang, ya ce sojoji na ci gaba da ayyukansu domin sake ƙwato dukkan yankunan da ’yan adawa ke riƙe da su, inda ya ƙara da cewa an riga an sake ƙwato wasu ƙauyuka.

    Ya kuma ce an kwashe fararen hula da rikicin ya rutsa da su zuwa wuraren da ke da kariya, tare da ba su kayan abinci kamar garin masara da man girki.

  16. 'Mozambique ta fuskanci ambaliya mafi muni a bana a shekara 25'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Mozambique sun bayyana cewa ambaliyar ruwa mai tsanani da ta afka wa sassan ƙasar tun daga ranar 7 ga Janairu ita ce mafi muni a shekara 25.

    Ambaliyar ta kashe aƙalla mutum 18, ta tilasta wa kimanin mutum 392,000 barin muhallansu, yayin da kusan mutum 780,000 ne ambaliyar ta shafa a faɗin ƙasar tun bayan fara damina a watan Oktoban 2025, a cewar gwamnati da Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Jihohin Gaza da Maputo da Sofala ne ambaliyar ta fi shafa inda gidaje da makarantu da cibiyoyin lafiya da hanyoyi da wutar lantarki suka lalace matuƙa.

    Hukumar kula da bala’o’i ta ƙasa (INGD) ta yi gargaɗin cewa adadin mutanen da ambaliyar ta shafa na iya kai wa miliyan 1.1, tana mai kiran lamarin mafi muni cikin shekaru fiye da ashirin.

    Manyan koguna irin su Limpopo da Incomati da Save sun cika tam inda suka yi ambaliya, lamarin da ya katse al’umma da dama tare da haifar da ƙarancin abinci da man fetur.

    Rahotanni sun nuna cewa fiye da gidaje 150,000 da cibiyoyin lafiya 242 da makarantu sama da 575 sun nutse, yayin da sama da hanyoyin kilomita 5,000 sun lalace, ciki har da rushewar wasu sassan babbar hanyar da ke haɗa arewa da kudu.

    Shugaban ƙasar, Daniel Chapo, ya tura jami’an agaji da sojoji da motocin gwamnati domin kai ɗauki, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin jin ƙai.

  17. Ba a nemi izinin majalisa ba kafin kai harin Amurka a Najeriya - Sanata Ningi

    ...

    Asalin hoton, Abdul Ahmed Ningi/Facebook

    Sanata Abdul Ahmed Ningi, mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya, ya bayyana damuwa kan yadda Amurka ta kai hare-haren sama kan wuraren ‘yan ta’adda a Jihar Sokoto ba tare da neman izini ko tuntuɓar majalisar dokokin ƙasar ba kafin ta kai harin.

    Sanatan ya ce "hakan ya saɓa wa ikon ƙasar tare da karya tsarin sa ido na majalisa kan al’amuran tsaro."

    Sanata Ningi ya tayar da batun ne a zauren majalisar dattawa inda ya ce "majalisar dokoki na da rawar da doka ta tanada a harkokin tsaro da kuma shigar sojojin ƙasashen waje, amma ba a nemi ra’ayinta ba kafin kai harin."

    Ya gargaɗi cewa "barin ɓangaren zartarwa ya yanke irin wannan hukunci shi kaɗai na iya buɗe ƙofa ga wasu ƙasashe su ma su ɗauki mataki makamancin haka nan gaba."

    Biyo bayan wannan ƙorafi ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Majalisar ta shirya gudanar da zama domin tattaunawa da yan majalisa kan lamarin.

    Ya ce an shirya yin bayanin tun da farko amma aka ɗage shi domin girmama marigayi Sanata Godiya Akwashiki.

    Akpabio ya jaddada cewa batun tsaro ne mai matuƙar muhimmanci wanda bai dace a tattauna a bainar jama’a ba, yana mai tabbatar da cewa za a shirya zama nan ba da jimawa ba domin yi wa sanatoci bayani kan hare-haren da Amurka ta kai a ranar 25 ga Disamba 2025, wanda AFRICOM ta ce an aiwatar da shi tare da haɗin gwiwar hukumomin Najeriya domin kai farmaki kan sansanonin ‘yan ISIS.

  18. Komawar Abba APC: Wa ke da riba wa ke da asara?

    ...

    Asalin hoton, Social media

    Komawar Gwamnan jihar Kabo, Abba Kabir Yusuf jam'iyyar APC na ci gaba da ɗaukar hankali a siyasar arewacin Najeriya.

    Yayin da wasu ke ci gaba da murna wasu kuma takaici matakin ya janyo musu, sakamakon abin da matakin gwamnan ya janyo musu.

    Gwamnan dai ya ce ya zaɓi komawa APC ne saboda ci gaban al'ummar Kano.

    Yayin da yake jawabi a wurin taron komawar tasa, Abba Kabir ya ce ya ɗauki matakin ne domin jihar Kanio ta amfana da manyan ayyukan gwmanatin tarayya.

    Matakin gwamnan zai sauya abubuwa masu yawa a fagen siyasar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.

    Yayin da matakin zai yi wa wasu da dama daɗi, wasu kuwa akasin hakan ne, saboda ba yadda suka so ba.

    BBC ta yi nazarin ɓangarorin siyasa da za su ƙirga riba ko asara saboda matakin an gwamnan Kano.

  19. An ji harbe-harbe da fashe-fashe a kusa babban filin jirgin Nijar

    Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    A daren jiya ne aka ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da kusa da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Diori Hamari da ke babban birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

    Kafar LSI Africa ce ta ruwaito labarin daga wasu shaidun gani da ido, inda suka ce an fara jin ƙarar ne da misalin ƙarfe 12 na dare, sannan ya ɗan ɗauki lokaci ana yi.

    Wasu faye-fayen bidiyo da suka karaɗe kafofin sada zumunta a ƙasar sun nuna yadda haske ya yi sama daga daidai yankin da ake jin harbe-harben.

    Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton dai hukumomi a ƙasar ba su ce komai ba kan aukuwar lamarin, musamman kan musabbin harbe-harbe da fashe-fashen ko asarar da aka yi, da kuma ko an rasa rai.

    Sai dai akwai rahotannin da ba a tabbatar ba da ke zargin wataƙila mayaƙa masu iƙirarin jihadi ne suka yi yunƙurin kai hari a filin jirgin.

    Sai dai wasu na zargin ganin yanayin ƙarar wataƙila akwai yiwuwar wata matsala ce ta cikin gida da ba za ta rasa nasaba da boren sojoji ba, kamar yadda rahoton ya ƙara.

    Nijar dai na fama da matsalolin rashin tsaro a cikin ƴan shekarun nan duk da cewa tana ƙarƙashin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya karɓi mulki bayan juyin mulkin watan Yulin 2023.

  20. Jirgin ruwan sojin Amurka na tunkarar Iran - Trump

    Iran

    Asalin hoton, Reuters / Getty Images

    Shugaba Trump ya sake yi wa Iran barazanar ɗaukar matakin soja, inda yake matsa wa ƙasar lamba don ta tattauna kan yarjejeniyar makaman nukiliya.

    Mista Trump ya ce wani babban jirgin rundunar sojin Amurka na tunkarar ƙasar, yana mai barazanar cewa harin da zai kai mata nan gaba zai nunka irin wanda ya kai mata a watan Yuni.

    Iran ta dage cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne, tana mai gargaɗin cewa duk wani hari da Amurka ta kai mata na iya jefa rayukan dukkan dakarunta da ke gabas ta tsakiya cikin haɗari.

    A Majalisar Dinkin Duniya, China ta yi gargadi game da barazanar ta Amurka. Wannan na faurwa ne bayan zargin kisan dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati da aka yi a Iran.