Babu tabbas kan makomar Maguire a United, Juventus za ta yi gagarumin cefane

 Harry Maguire

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto, Harry Maguire
Lokacin karatu: Minti 2

Juventus na ƙara himma wajen ɗaukar ɗan wasan gaban Faransa mai shekaru 27 Randal Kolo Muani, wanda ke zaman aro a Tottenham daga Paris St-Germain, kuma Spurs na iya neman maye gurbinsa da ɗan wasan gaba na Crystal Palace Jean-Philippe Mateta, mai shekaru 28, idan ya tafi. (Mail)

Shima dan wasan gaban Holland Joshua Zirkzee na cikin yan wasan da Juventus ke tunanin dauka, inda Manchester United ta ba wa dan wasan mai shekara 24 damar barin su a matsayin aro. (Gazzetta dello Sport)

Manchester United na tunanin yadda za ta yi da ɗan wasan Ingila Harry Maguire. Ƙungiyar ba ta yi wata tattaunawa mai mahimmanci da ɗan wasan bayan mai shekaru 32 wanda kwantaraginsa zai kare a ƙarshen kakar wasan nan ba. Ƙungiyoyi a Italiya da Turkiyya sun tuntuɓi wakilinsa. (Athletic)

PSG ta fara tattaunawa don tsawaita kwantaragin kocinta Luis Enrique, wanda wa'adinsa ke shirin karewa a 2027. (Le Parisien)

Ana alakanta dan wasan tsakiya na Turkiyya Kenan Yildiz, mai shekaru 20 da wasu ƙungiyoyin Premier League, ko da yake bayanai na cewa daf yake da da tsawaita zamansa a Juventus. (Sky Sports Germany)

Atletico Madrid na son ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Jamus Leon Goretzka, wanda kwangilarsa za ta ƙare a Bayern Munich a lokacin bazara (Sky Sports Germany)

Jesse Lingard, mai shekaru 33, yana tattaunawa da kungiyoyin Ingila da Italiya. Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United, bai da wata kungiya a yanzu, tun bayan barin FC Seoul a watan Disamba. (Mail)

River Plate ta amince da yarjejeniyar siyan dan wasan tsakiya na Chelsea da Ecuador mai shekaru 18, Kendry Paez, wanda ya shafe rabin wannan kakar a Strasbourg a matsayin aro. (Fabrizio Romano)

AC Milan na neman mai tsaron baya kuma za su iya neman Radu Dragusin na Tottenham. Dan wasan na Romania mai shekaru 23 yana sha'awar Roma da Napoli. (Calciomercato)