Yadda cire manyan janar-janar ɗin China ya jefa sojojin ƙasar cikin ruɗani

Zhang Youxia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zhang Youxia, mai shekara 75, shi ne mataimakin babbar cibiyar manyan hafsoshin China
    • Marubuci, Stephen McDonell
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, China correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 3

Sojoji masu manyan mukamai a rundunar sojin ƙasar China na cikin wani hali.

Cire babban janar ɗin soji Zhang Youxia a karshen mako da kuma wani babban jami'in soji, janar Liu Zhenli, ya janyo tambayoyi kan abin da ya haddasa tirka-tirkar iko da ke afkuwa a ƙasar - kuma abin da hakan ke nufi ga shirin yaƙi da China ke ciki, watakila wani yunkuri ne na karɓe ikon Taiwan da ƙarfin tuwo ko kuma ta shiga wani babban rikici ne na yanki.

Zhang, mai shekara 75, shi ne mataimakin kwamandan babbar cibiyar manyan hafsoshin China (CMC) - na ɓangaren jam'iyyar Communist wanda shugaban ƙasar Xi Jingping ke jagoranta, kuma shi ne yake kula da dukkan sojoji.

Cibiyar, wadda ta kunshi mutum bakwai, yanzu sun ragu zuwa mambobi biyu kaɗai - Xi da kuma janar Zhang Shengmin.

Cibiyar ta manyan hafsoshin sojin ƙasar ita ce ke da ikon kula da miliyoyin jami'an soji. Tana da ƙarfin da ya kai zama shugaban cibiyar ita ce mukami ɗaya tilo da Deng Xiaoping ya riƙe a matsayin jagora a China.

Abu ne da ba a taɓa gani ba cewa shugaba Xi da janar ɗaya ne kaɗai suka rage a cibiyar, a cewar Lyle Morris daga cibiyar tsare-tsare ta Asiya.

"Cibiyar na cikin rarrabuwa," kamar yadda ya faɗa wa BBC, inda ya ƙara da cewa a yanzu babu komai a rundunar sojin China".

Da aka tambaye shi kan abin da ya sa ake sauke janar-janar da dama, Morris ya ce: "Akwai jita-jita da yawa da ke yawo. Ba mu sani ba, mene gaskiya ko kuma ba gaskiya ba zuwa yanzu... sai dai abu ne mara kyau ga Xi Jingping, kan jagorancinsa da kuma iko a cibiyar."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani farfesa, Chong Ja Ian daga wata jami'a a Singapore, ya ce ba ya da masaniya kan abin da ya janyo faɗuwar janar Zhang, amma akwai jita-jita da yawa kan batun.

"Akwai maganganu da yawa kan fitar da bayanan sirri kan nukiliya ga Amurka da yunkurin juyin mulki da kuma rikici na ɓangarori. Akwai jita-jitar buɗe wuta a Beijing," in ji shi.

"Sai dai faɗuwar Zhang da Liu da kuma waɗannan jita-jita suna nuni ne kan abubuwa biyu: Cewa ba za a iya far wa Xi ba kuma babu bayanai sosai na abubuwan da ke faruwa a Beijing, abin da ya ingiza rashin tabbas."

Sanarwar da aka fitar cewa ana binciken janar Zhang da Liu, ta ce ana zargin su da "babban laifin saɓa wa doka", wato zargin cin hanci.

Zarge-zargen da ake yi wa dukkan waɗannan janar-janar ba su fito ga jama'a ba kuma ba za su taɓa fito wa ba. Sai dai, bayyana cewa suna karkashin bincike na nufin cewa akwai yiwuwar yanke musu hukuncin zaman gidan yari na ɗan lokaci.

Za a iya cewa an sauke janar-janar ɗin sojojin ne kan zargin cin hanci, sai dai akwai yiwuwar cewa akwai rikicin siyasa, ganin yadda aka kori sojojin a baya bayan-nan.

China ta kasance tana fama da matsalar cin hanci da rashawa lokacin da XI Jinping ya zo kan mulki, inda ya girke wata tawagar sa ido mara tsoro, domin kakkaɓe ƴan adawar siyasa ko kuma waɗanda ke cikin gwamnati da ba su yin mubaya'a.

Wannan ya bai wa Xi ikon da babu mai kalubalantarsa, abin da ba sake gani ba tun lokacin ɗan siyasa Mao Zedong.

Duk da haka wannan irin jagoranci yana rashin alfanu shi ma. Alal misali, zargi kaɗan a rundunar soji zai iya janyo taka tsantsan, har ma da ɗaukar matakan da ba su dace ba.

Mahaifin Zhang Youxia ya kasance mai son kawo sauyi. Janar ɗin ya kasance yana da alaƙa mai ƙarfi da Xi kafin saɓani na baya baya-nan ya janyo taɓarɓarewar abubuwa, saboda imanin cewa babu wanda za a iya bari.

Yana ɗaya daga cikin manyan jami'an soji da suke da ƙwarewar yaƙi, abin da ya sa rashinsa ya kasance babban giɓi da rundunar sojin China.

Cire shi zai janyo matsaloli na tsawon lokaci ga Xi Jinping, a cewar Morris.

Za a iya cewa Xi ya sake daɓɓaka ikonsa, sai dai abin da ke faruwa na nufin cewa akwai zaman tankiya, in ji shi.

"Yanayi ne mara kyau ga Xi kuma ina tunanin akwai ruɗani a rundunar sojin ƙasar, daga wajen Xi da jagororinsa - musamman waɗanda ke cikin rundunar - a tsawon shekaru.

Cire manyan janar-janar ɗin ya janyo ana son ganin waye ne abin zai sake shafa, ganin abin da ya faru da waɗanda aka cire, zai sa waɗanda za su iya samun mukamai shiga ɗar-ɗar, inda batun yaƙi da cin hanci na Xi zai iya dirar kan mutum kowane lokaci.

Duka wannan ya zo ne a daidai lokacin da Beijing ke ƙara matsin lamba kan Taiwan har da barazana, da kuma yunkurin son ƙwace yankin mai cin gashin kansa ta ƙarfin tuwo.

Masu sharhi na ganin cewa cire waɗannan janar-janar na soji ya ɗan yi nakasu ga batun karɓe Taiwan - duk da cewa wasu na tunanin hakan ba zai yi wani illa ba kan burin Beijing.