Muhimman yarjeniyoyin da Najeriya da Turkiyya suka kulla

Asalin hoton, @aonanuga1956/X
Turkiyya ta sanar da sabbin yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a fannin tattalin arziki, kasuwanci da tsaro da Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan ziyarar aiki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai zuwa Turkiyya.
A wani taron manema labarai da suka yi tare da shugaba Tinubu a ranar Talata, 27 ga watan Janairu, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa, ƙasashen biyu ba su amince da cimma yarjejeniya cinikayya da ta kai dala biliyan biya.r
Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da shugaba Tinubu ya cimma a Turkiyya.
Yaƙi da ta'addanci

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayyana cewa ƙasarsa za ta taimakawa Najeriya wajen yaƙi da ta'addanci.
A taron manema labarai na haɗin gwiwa da sgugabannin biyu suka yi, ya bayyana shirin zurfafa kai a fannin horas da sojoji da kuma leƙen asiri.
Shugaban na Turkiyya ya ce "Muna tare da abokanmu na Najeriya don yaƙi da ta'addanci. Muna kimanta damarmakin da za a samu na haɗin gwiwa, musamman a fannin horas da sojoji da leƙen asiri," in ji shugaban na Turkiyya.
Ya ƙara da cewa, Turkiyya a shirye ta ke ta ba da amfani da gogewar da ta ke ita a fannin tsaro sakamakon yaƙin da ita ma ta yi da ta'addanci, wuirn taimakawa gwamnatin Najeriya.
Shugaban na Turkiyya ya ce ƙungiyoyin ƴan ta'adda da ke sassan Afrika musamman a yankin Sahel na yin barazana ga zaman lafiyar nahiyar baki ɗaya.
Jami'an Najeriya sun kuma gana da manyan kamfanoni ta ke taka rawa a fannin tsaro a Turkiyya yayin ziyarar tare da bayyana ƙwarin gwiwar cewa tattaunawatr za ta haifar da sakamako mai kyau.
Shugaba Tinubu ya ce taimakon sojin da za a samu zai zarce Najeriya zuwa sauran ƙasashen da ke yankin, waɗanda ke fuskantar ƙalubalen tsaro daban-daban.
Najeriya dai na fuskantar matsalolin tsaro da dama, waɗanda suka haɗa da hare-hare daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi da ƴan fashin daji masu sace mutane don neman kuɗin fansa , da kuma tashe-tashen hankula da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu aikata laifuka da kuma ƴan aware.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Kulla hulɗar kasuwanci ta dala biliyan 5

Asalin hoton, Bola Tinubu/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A yayin taron manema labaran, shugaba Erdogan ya kuma bayyana wasu sabbin yarjejeniyoyin tattalin arziki da kasuwanci da ƙasarsa ta ƙulla da Najeriya.
Ya ce Turkiyya na shirin sanya hannun jarin dalar Amurka biliyan 5 wanda ya haɗa da hada-hadar kasuwanci da Najeriya inda ya ce an fara tattaunawa domin tabbatar da hakan.
"Muna ganin cewa muna ba da muhimmiyar dama ta fannonin ciniki da zuba jari. A yayin tarukanmu na yau, mun sake jaddada aniyarmu ta cimma yarjejeniyar cinikin dala biliyan biyar da kuma tattauna matakan da za mu ɗauka domin tabbatar da hakan," in ji shi.
Duk da haka, har yanzu ba a fayyace cikakken tsarin manufar cinikin da kuma wa'adin lokacin da aka ɗiba domin cimmasa ba.
A halin yanzu, yawan ciniki tsakanin ƙasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan biyu. Turkiyya na fitar da jiragen sama da jirage masu saukar ungulu da injuna, da kuma karafa, da kayayyakin sinadarai zuwa Najeriya. Yayin da Najeriya ke fitar da ɗanyen mai da kayayyakin noma zuwa ƙasar Turkiyya, kamar yadda mai magana da yawun shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, ya yi bayani.
Shugaba Erdogan ya ce kafa kwamitin haɗin gwiwa na tattalin arziki da kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu zai samar da damammaki na faɗaɗa zuba jarin Turkiyya a Najeriya domin cimma burinsu.
Haɗin gwiwa a fannin ilimi
A ɓangaren ilimi kuwa, shugaban na Turkiyya ya ce bayan fara ayyukan gidauniyar Maarif a Najeriya, Tukikiyya za ta iya samar da ƙarin gudummawa ga al'ummar Najeriya.
Shugaba Erdoğan ya ƙara da cewa, "Yayin da muka rattaba hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin ilimi a yau, za mu ci gaba da ƙarfafa tsarin haɗin gwiwarmu."
Tuntuɓe da faɗuwar shugaba Tinubu
Ɗaya daga cikin masu taimakawa shugaba Tinubu ya ce, Shugaban na Najeriya "yana cikin ƙoshin lafiya" bayan da ya yi tuntuɓe faɗi a yayin da ya ke halartar liyafar maraba da aka yi ma sa aTurkiyya.
Shugaba Erdigan ya tarbi shugaba Tinubu, mai shekaru 73, a wani biki da aka yi a babban birnin ƙasar, Ankara, inda ya yi tuntuɓe.
Bayan ya wuce wani layin sojoji da manyan mutane, wani bidiyo da aka wallafa a shafin shugaban Turkiyya na dandalin X ya nuna daidai lokacin da shugab Tinubu ya yi tuntuɓe ya faɗi yayin da yake tafiya.
Bidiyon ya nuna lokacin da mutane suka taru domin taimakawa shugaban ƙasar kafinn daga baya aka yanke ya fara nuna Tinubu da Erdogan suna tsaye a kusa da juna.
Tinubu bai ji rauni ba kuma daya daga cikin masu taimaka masa Sunday Dare, ya ce zai iya ci gaba da ganawar tasu.
Hotunan bidiyo na lamarin sun bazu a shafukan sada zumunta.
Wani mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, daga baya ya ce Tinubu ya taka wani ƙarfe ne ''da ke ƙasa, wanda ya taɗiye shi".
"Ba wani babban abu ba ne, sai dai kawai akwai mutanen da ke son tayar da zaune tsaye kan wani abu da bai ya kawo ba. Tuntube ne kawai, Allah Ya kiyaye bai faɗi ba" in ji shi.
Karon farko da shugaban ƙasar ya faɗi a bainar jama'a, a watan Yuni 2024 ne, inda ya mayar da abun na raha inda ya ce rawa ya yi ba faɗuwa ba.
A halin yanzu, ɗaya daga cikin mataimakansa ya bayyana lamarin a matsayin "tuntuɓe," kuma mutane da dama sun jajantawa Tinubu, ciki har da babban ɗan siyasar adawa Atiku Abubakar, wanda ya bayyana abin a matsayin "abin takaici".
Najeriya da Turkiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyoyi guda tara
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce a ƙarshen taron ƙasashen biyu, shugabannin biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi tara a fannin tsaro, ilimi, yada labarai, manufofin ƙasashen waje, kasuwanci, ci gaban zamantakewa, da hadin gwiwar hukumomi tsakanin ma'aikatun ƙasashen waje na ƙasashen biyu.
Yarjejeniyoyin sun haɗa da:
- Yarjejeniyar haɗin gwiwa a fagen harkokin ƙasashen waje tsakanin Jamhuriyar Turkiyya, Ma'aikatar Al'adu da Yawon buɗe ido, Fadar Shugaban ƙasa ta Turkawa da ke ƙasashen waje, hukumar hukumar kula da ƴan Najeriya da ke ƙasashen ƙatare.
- Yarjejeniyar haɗin kai kan harkokin watsa Labarai da sadarwa tsakanin gwamnatin Turkiyya da gwamnatin Tarayyar Najeriya.
- Haɗin gwiwa a fannin Ilimi mai zurfi tsakanin gwamnatoci ƙasar Turkiyya da na tarayyar Najeriya.
- Sanarwar Kafa Kwamitin haɗin gwiwar tattalin arziki da kasuwanci; da yarjejeniya a ɓangaren Ingantattun Kayayyakin Halal.
- Hadin kai tsakanin Jamhuriyar Turkiyya, da Ma'aikatar harkokin waje, da Kwalejin nazarin Diflomasiyya da gwamnatin Najeriya, da Ma'aikatar harkokin wajenta, Kwalejin da kuma kwalejin nazarin harkokin ƙasshen waje.
- Yarjejeniyar haɗin kai tsakanin jamhuriyar Turkiyya, da ma'aikatar Jin daɗin Jama'a da Tarayyar Najeriya, Ma'aikatar harkokin mata da ci gaban zamantakewa.
- Yarjejeniyar haɗin Kai a fannin tsaro tsakanin Jamhuriyar Turkiyya da Tarayyar Najeriya.
Najeriya da Turkiyya na ci gaba da ƙara danƙon alaƙar diflomasiyya ta ƙut da ƙut da ke tsakaninsu na tsawon shekaru.
Shugaba Erdoğan ya ziyarci Najeriya a shekarar 2021.
Dukansu sun kasance mambobin ƙungiyar haɗin kan Musulunci (OIC) da D-8, ƙungiyar haɗin gwiwa da ta haɗa da Bangladesh da Masar da Indonesia da Iran, da Malaysia da kuma Pakistan.
Turkiyya na ƙara faɗaɗa tasirinta a faɗin Afirka a cikin ƴan shekarun nan, tare da ƙarfafa tasirin ta hanyar haɗin gwiwar soji da fasahar jirage da ilimi da ayyukan jin kai da al'adu. Ta tabbatar da matsayinta a matsayin wadda za ta maye gurbin ƙasashen yammacin duniya a nahiyar.











