Yadda 'faɗuwar' Bola Tinubu a Turkiyya ke ruruta batun rashin lafiyarsa

Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 6

Duk da cewa fadar shugaban Najeriya ta fitar da bayani domin yayyafa ruwa kan muhawarar da ake tafkawa game da tuntuɓen da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi a ƙasar Turkiyya, lamarin na ci gaba da tayar da ƙura.

Tinubu mai shekara 73 ya yi tuntuɓe ne ya faɗi a daidai lokacin da ake masa bikin tarbar ban-girma a Ankara, babban birnin ƙasar Turkiyya.

Tun da farko, Tinubu ya ratsa ta tsakiyar sojoji da suka yi masa faretin girmamawa da kuma manyan jami'an gwamnati da suka tarbe shi.

Sai dai suna cikin tafiya ne tare da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, kwatsam sai ya yi tuntuɓe ya faɗi.

Bidiyon mai kimamin daƙiƙa 45 ya nuna mutane suna ƙoƙarin ɗaga shi, kafin daga bisani aka gan su tare da shugaban na Turkiya suna ci gaba da tafiya.

Tuni dai masu magana da yawun shugaban suka yi watsi da batun, inda suka nanata cewa lafiyarsa ƙalau, sannan suka ce tuntuɓe ne kawai, kuma tuni ya ci gaba da gudanar da abubuwan da suka kai shi ƙasar.

Babu dai wata alamar rauni da aka gani a tattare da Tinubun domin ya miƙe ya ci gaba da tafiya, sannan mai magana da yawunsa, Sunday Dare ya ce Tinubu ya ci gaba da tattaunawa da ƙulla yarjejeniyoyin da suka kai shi ƙasar.

"Abin da ya sa Tinubu ya faɗi"

Da yake bayani kan haƙiƙanin abin da ya faru, mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya taka wani ƙarfe da ke ƙasa a lokacin da yake tafiya.

"Wannan ƙarfen da ya taka ne ya sa ya ɗan yi tuntuɓen tafiya," in ji Bayo a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ƙara da cewa babu wata matsala, "sai dai masu neman abin magana ne a kusan kowane irin abin da ya faru. Kawai tuntuɓe ya yi ba wani abu ba, muna godiya ga Allah ba faɗuwa ya yi ba," in ji shi.

Sai dai duk da haka mutane sun ci gaba da muhawara kan batun a shafukan sada zumunta.

A nasa bayanin, Sanata Shehu Sani ya ce lamarin ya nuna cewa shugaban mutum ne kamar kowa.

Shi ma wani mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Sunday Dare, ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce Tinubu na cikin ƙoshin lafiya, kuma ya ci gaba da gudanar da aikace-aikacen da suka kai shi kamar yadda aka tsara.

"Bayan tarba ta musamman da aka yi masa a Ankara, ya samu damar tattaunawa da shugaban Turkiyya da sauran jami'an gwamnati na Najeriya da na ƙasar Turkiyya," in ji shi a sanarwar.

Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images

Ba yau farau ba

Da wannan ba ne karo na farko da shugaban na Najeriya ya yi irin wannan tuntuɓen, inda ya faɗi ko ya kusa faɗuwa.

A watan Yunin shekarar 2024, Tinubu ya yi tuntuɓe ya faɗi a wajen taron Ranar Dimokuraɗiyya ta Najeriya da aka yi dandalin taro na Eagle Square da ke babban birnin tarayya Abuja.

Ko lokacin, ƴan ƙasar da dama sun bayyana damuwarsu kan yanayin ƙarfin jikin shugaban, inda wasu ke ganin akwai alamar rashin isasshiyar lafiya a tattare da shi da ke rage masa kuzari.

Sai dai ko a wancan lokacin, masu magana da yawun shugaban sun yi watsi da maganganun, inda suka "kawai ya yi tuntuɓe ne," amma ba wata babbar matsala ba ce.

Shi da kansa ya mayar da lamarin abin ban dariya, inda ya bayyana daga baya cewa ya "ɗan rausaya ne" ne ba faɗuwa ba, inda ya ƙara da cewa rausayawa ce ta gaisuwar "dobale" da ƙabilar Yarbawa ke yi.

Tafiye-tafiye: Ziyara ko jinya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abu da ke ɗaukar hankalin ƴan Najeriya shi ne yadda shugaban yake yawan tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, lamarin da ya sa wasu ke zargin ko dai akwai wani abun daban da kai shi ƙasashen wajen.

Wasu na ganin tafiye-tafiyen sun yi yawa, inda wasu kume ke zargin ko dai yana zuwa duba lafiyarsa ne ba tare da an bayyana ba.

A wata tattaunawa da tashar Channels mai zaman kanta a Abuja, Farfesa Jideofor Adibe na Jami'ar Jihar Nasarawa, ya ce bai ga dalilin wasu tafiye-tafiyen shugaban ba.

"Gaskiya tafiye-tafiyen sun yi yawa. Na san cewa akwai buƙatar inganta alaƙar diflomasiyya, amma bai kamata tafiye-tafiyen su yi yawa haka ba," in ji Adibe.

Ya ce babu dalilin da za a ce dole shugaban ƙasa ne zai yi ta tafiye-tafiyen, "akwai ministan harkokin waje, sannan akwai ofisoshin jakadanci, sannan ma wasu tattaunawar za a yi ta bidiyo ta intanet."

Sai dai Adibe ya ce ba Tinubu ne farau ba, domin a cewarsa, Obasanjo ne ya fara irin waɗannan tafiye-tafiye masu yawan, Buhari ya ɗaura, sannan shi ma Tinubu yanzu yake nasa.

Batun lafiyar Tinubu ta daɗe tana jan hankali, tun bayan da ya lashe zaɓe, inda tun kafin a rantsar da shi ƴan hamayya suka fara cewa ba shi da irin kuzarin da ya yi amfani da shi a lokacin da yake mulkin jihar Legas.

Dama dai tun lokacin da yake yaƙin neman zaɓe wasu ke tantama kan lafiyarsa, lamarin da masoyansa suke bayyanawa da adawar siyasa.

Bayan zaɓen wanda da ya doke Atiku Abubakar a shekarar 2023, Tinubu ya yi bulaguro zuwa ƙasar waje sau biyu, lamarin da ya ƙara janyo tambayoyi game da lafiyarsa.

A shekarar 2021, ya shafe watanni a London ana kula da lafiyarsa, duk da dai ba a bayyana cutar da ke damunsa ba a lokacin.

Sai dai a lokacin ya yi watsi da sukar da ake masa na ƙarfin jiki, inda ya ce aikin shugaban ƙasa ba ya buƙatar lafiya da ƙarfi kamar mai wasan tsere.

Ƴan Najeriya na ƙara sa ido kan lafiyar shugabanninsu ne tun bayan jinyar da Umaru Musa Yar'adua ya yi fama da ita kafin ya rasu a 2010.

Haka shi ma Muhammadu Buhari ya sha tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje domin a duba lafiyarsa, lamarin da wasu ke ganin yana jawo tsaiko a harkokin mulki.

Ko a watan Agustan 2025, sai da fadar shugaban Najeriya ta musanta zargin cewa Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje.

Raɗe-raɗin sun fara yawo ne ibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ta ruwaito daga wasu majiyoyinta cewa tawagar likitocin shugaban ƙasar suna shirye-shiryen fitar da shi zuwa asibiti a wata ƙasar.

A lokacin ne mai magana da yawun shugaba Tinubu, Abdu'aziz Abdul'aziz ya shaida wa BBC cewa rahotannin ba gaskiya ba ne.

Me ya kai Tinubu Turkiyya?

Tinubu ya ziyarci Turkiyya ne domin "inganta alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu," kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana kafin tafiyar ta ranar Litinin da ta gabata.

Bayan tattaunawar shugaban ƙasashen biyu, Turkiyya ta sanar da cewa ta ƙulla sabuwar alaƙar kasuwanci da tsaro da Najeriya.

Da yake jawabi a taron manema labarai, Erdogan ya ce ƙasashen biyu sun kuɗuri aninyar ƙara kasuwancin da ke tsakanin su zuwa dala biliyan 5, wato kimanin fam biliyan 3.5.

Haka kuma ƙasashen biyu sun saka hannu kan yarjejeninyar tsaro, inda ƙasar Turkiyya ta yi alƙawarin tallafa wa Najeriya a yaƙi da matsalolin tsaron da take fuskanta.

Haka kuma ƙasar ta ce za ta taimaka wa Najeriya wajen horar da jami'an tsaronta, sannan za su inganta alaƙar da ke tsakaninsu wajen tattara bayanan sirri da sauran su.

A nasa ɓangaren, Tinubu ya rubuta a shafinsa na X cewa, "Najeriya a shirye take ta ƙulla alaƙa da Turkiyya, kuma ƙofarmu a buɗe take wajen samun sababbin dabarori da zuba jari domin ɗaura ƙasarmu a hanya mai kyau."