Wace dabara ta rage wa Tinubu game da tsadar rayuwa a Najeriya?

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Bankin cigaban ƙasashen Afrika, a baya-bayan nan ya yi gargaɗin cewa tsadar rayuwa a wasu ƙasashen Afrika, ciki har da Najeriya na iya haifar da bore.

Bankin ya shawarci ƙasashen da su hanzarta ɗaukan matakin gaggawa domin kiyaye haɗarin da ke gabansu, ta yadda suma jama'a za su samu sassauci.

Wannan matsala ta tsadar rayuwa ta sa wasu yin zanga- zanga a kwanakin da suka gabata a wasu jihohin Najeriya har da Kano da Neja da Oyo da Legas.

Najeriya dai na fuskantar yanayi na matsin rayuwa sakamakon janye tallafin man fetur da kuma yadda darajar naira ke ƙara karyewa.

Ita ma gwamnatin a baya ta bijiro da wasu dabaru uku da ta ce za su kawo sauƙi ga 'yan ƙasar - fito da hatsi ton dubu arba'in domin sayarwa a kan farashi mai sauƙi sai tattaunawa da masu kamfanonin sarrafa shinkafa da kuma shigo da abinci daga wasu ƙasashen.

Duk da waɗan nan matakai, har yanzu al'umma na fuskantar tasku wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum.

Ita ma babbar jam'iyyar adawa a ƙasar - PDP ta nemi shugaba Tinubu ya sauka daga kan kujerarsa kan abin da ta kira gazawa wajen warware tarin ƙalubalen da 'yan Najeriya ke ciki sanadin cire tallafin man fetur da kuma karyewar darajar naira.

Farfesa Garba Ibrahim Sheka, masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce abubuwa a ƙasar sun jagule saboda "hauhawar farashi ta wuce wadda za a auna a wani sikeli, domin ana auna ta a wata zuwa wata ko sati zuwa sati, yanzu ta kai har a rana ɗaya ma sai ka samu farashi ya hau sau biyu ko sau uku.

Ya ce har yanzu hanyoyin samun kuɗi ba su bunƙasa ba - masu albashi ba a ƙara musu albashi ba, farashi kuma yana ta ninkawa, mutane sun talauce gaba ɗaya.

A cewarsa, "wanda ake cewa suna sama da layin fatara (poverty line), yanzu kusan kowa yana ciki "sai dai 'yan kaɗan".

A nasa bangaren, masani Abubakar Aliyu ya ce irin wannan bore da aka soma yi a wasu jihohin ƙasar alama ce ta cewa "ko ina zai amsa" inda kuma ya tunatar da shugaba Tinubu cewa "zanga-zanga kan ƙarin farashin burodi ne ya kifar da gwamnatin Al-bashir a Sudan."

Masanin ya ce rashin abinci babban tashin hankali ne ga ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma tunatar da shugaba Tinubu kan alƙawuran da ya yi kafin hawa kan mulki na inganta albashi da samar da ayyukan yi da kuma abinci saboda "babu wanda yake zaɓar gwamnati don gina gadoji."

A cewarsa, akwai dabaru biyu da suka kamata shugaba Tinubu ya yi amfani da su matuƙar ana son a samu zaman lafiya a Najeriya.

Buɗe boda da shigo da abinci

..

Asalin hoton, PIUS UTOMI EKPE

Masanin ya ce kamata ya yi Tinubu ya gaggauta fitowa ya "faɗa wa 'yan ƙasa cewa za a shigo da abinci a sa masa tallafi domin sayarwa mutane." Ya ce a irin wannan yanayin, ana iya yin tallafi ko kuma a raba wa mutane kyauta.

A nasa ɓangare, shi ma farfesa Garba Sheka ya ce matakin da aka ɗauka na hana shiga da shinkafa Najeriya ya ƙara ta'azzara matsalar abinci "kasancewar manoman Najeriya ba za su iya samar da shinkafar da za ta wadaci ƙasar ba."

Saboda haka ya ce wajibi ne gwamnati ta buɗe iyakokin ƙasar domin a samu damar shigo da kayan abinci, musamman shinkafa.

Samar da tallafi a wasu ɓangarorin

Masani kan tattalin arziƙi Abubakar Aliyu ya ce a maimakon ƙoƙarin cire tallafi da gwamnati ke yi a wasu ɓangarori na tattalin arziƙi, kamata ya yi ta sanya tallafin a cikin su a wannan lokaci har sai an samu lafawar al’amura.

A kwanakin baya ne dai gwamnatin ta bayyana cewa ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗin tallafi da take biya a ɓangaren wutar lantarki ba kasancewar hakan wani babban nauyi ne a kanta.

Sai dai Aliyu ya ce idan har ana son a samu sauƙi ya kamata a ci gaba da bayar da tallafin wutar lantarki, da samar da tallafi a ɓangaren abinci da kuma rage kuɗaɗen haraji da masu shigo da kaya ke biyan hukumar hana-fasa-ƙwauri, wato kwastam.

Rage kashe kuɗin tafiyar da lamurran gwamnati

Dakta Shamsudden Muhammad na jami’ar Bayero da ke Kano ya ce wani matakin da dole a ɗauka in dai da gaske ne gwamnati na son rage wahalhalun da ƴan ƙasa ke ciki shi ne rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati.

A cewar sa “ba zai yiwu talaka na cikin halin wahala su kuma ƴan siyasa na tafiya da jerin gwanon motocin gwamnati masu tsada ba.

Nawa ake kashewa wajen kula da motoci kuma nawa ake kashewa wajen zuba musu man fetur, ba ƙananan kuɗi ba ne.” In ji shi.

..

Asalin hoton, Getty Images

'Ta inda aka hau ta nan za a sauka'

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dr Shamsudden Muhammad, ya ce "ta inda aka hau ta nan ya kamata a sauka."

A cewarsa an san cewa duk wasu manufofin gwamnati da suka jefa Najeriya cikin wannan hali ba su wuce batun cire tallafin man fetur da kuma sakin takardar naira sakaka a kasuwa ba.

Ya ce idan ana son samun sauƙi na halin da ake ciki dole ne sai an warware waɗannan manufofi.

Ya ƙara da cewa “Matukar aka ce za a kyale kasuwa ta tantance darajar naira to kuwa darajar nairar ba za ta taɓa daidatuwa ba.”

In da ya ce babu wani wuri a duniya da ake amfani da naira in ban da cikin Najeriya da kuma wasu garuruwa na ƙasashe masu maƙwaftaka, saboda haka nan buƙatar dala za ta ci gaba da ƙaruwa sannan darajar naira za ta ci gaba da tangal-tangal.

Masani Abubakar Aliyu ya bayyana cewa a yanzu gwamnati za ta iya yin waiwaye domin da alama manufofin da ta ɓullo da su ba su haifar da ci gaban da ake buƙata ba.

Ya bayar da misali da cewa idan gwamnati ta mayar da tallafin man fetur wanda a cewarsa, shi ne silar tsadar rayuwa, to hakan zai taimaka wajen rage wahalhalun da jama'a ke fuskanta.

Shin zai yiwu a mayar da tallafin man fetur?

Dakta Shamsudden ya ce "idan ina cewa a mayar da tallafi wasu na ganin kamar tastuniya ce nake yi, sukan ce ina kuɗin suke da za a mayar?"

To amma a cewar sa "babu wani abu da zai yi saurin kawo sauƙi a halin da ake ciki face mayar da tallafin man fetur ɗin da aka cire."

A nasa ɓangaren, farfesa sheka ya bayyana cewa duk da cewa sake mayar da tallafin man fetur tamkar "gwamnati ta lashe aman da ta yi ne, amma da alama idan aka mayar ɗin zai samar da sauƙi ga talaka."

Shi kuma Abubakar Aliyu ya ce "ba lallai ne sai an mayar da tallafin man fetur dindindin ba, amma za a iya mayarwa na wani ɗan lokaci,"

Yaƙara da cewa "za a iya mayarwa koda na wata shidda ne ko kuma shekara ɗaya, daga baya sai a janye a hankali."

Sai dai a cewar Dakta Shamsudden mayar da tallafin kuɗi ba abu ne mai sauƙi ba sanadiyyar matsin da gwamnati ke fuskanta daga hukumomi kamar na IMF da kuma Bankin Duniya.

Ya ce idan har gwamnati za ta biye wa shawarwarin IMF da Bankin duniya to da alama mutane za su ci gaba da kasancewa cikin ƙunci.