Yadda farashin kayan masarufi ya tashi a lokacin mulkin Tinubu

Asalin hoton, fb/Bola Tinubu
- Marubuci, Khalifa Dokaji
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
A Najeriya al'umma na kokawa kan tsadar rayuwa da tashin farashin kayan abinci, tun bayan da shugaban ƙasar Bola Ahemd Tinubu ya hau mulki watanni takwas da suka gabata.
Lamarin dai ya yi ƙamarin da ya sa wasu daga cikin al'ummar ƙasar suka fara gudanar da zanga-zanga a wasu daga cikin jihohin kasar.
A ranar litinin, al'umma sun hau kan titunan birnin Minna na jihar Neja da ke arewa maso tsakiyar ƙasar suna zanga-zanga kan matsin rayuwa.
Ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ta shaida wa BBC cewar: "Ba mu iya cin rabin abin da muke ci a baya, komai ya yi tsada, maza na tserewa (su bar iyalai) ba a sake ganin su...aure na mutuwa saboda rashin abinci."
An dai zaɓi shugaba Tinubu ne da tunanin samun sauƙi kan wahalhalun da al'ummar ƙasar suka faɗa ciki tun a lokacin tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Mutane da dama sun kyautata wa Tinubu zato, ganin cewa ya mulki jihar Legas, cibiyar kasuwanci da tattalin arziƙin ƙasar tsawon shekara takwas a matsayin gwamna.
Kuma har gobe shugaban ƙasar na bugun ƙirjin cewa shi ne ya ɗora jihar kan turbar bunƙasar tattalin arziƙi da take cin gajiya a yanzu.
Sai dai watanni da dama bayan hawan sa kan mulki, mutane da dama sun fara karaya ganin cewa abubuwa na ƙara taɓarɓarewa game da halin rayuwa.
Alƙaluman da Hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar a watan Janairu sun nuna cewa an samu tashin farashi mafi muni a ƙasar cikin shekara 27.
Hukumar ta ce tashin farashi ya ƙaru da kashi 28.92% a watan Disamban 2023, lamarin da ke nuna cewa an kwashe shekara guda ana samun tashin farashi a jere a ƙasar.
Wani abu da ke ƙara jefa mutanen ƙasar cikin damuwa shi ne hali na rashin tabbas kan lokacin da abubuwa za su daidaita.
BBC ta kwatanta farashin wasu kayan masarufi a lokacin da Tinubu ya karɓi mulki da kuma farashinsu a yanzu:
Kayan abinci

Shinkafa na daga cikin kayan masarufin da aka fi amfani da su a Najeriya, wanda ƴan ƙasar suka sha kokawa dangane da yadda farashinta ya yi tashin gauron zabi, duk da shirin bunƙasa nomanta da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ta samar.
Mun tuntuɓi shugaban kasuwar kayan abinci ta kasa da kasa ta Dawanau da ke Kano, Alhaji Muttaka Isa da Alhaji Musa Nabanki - Shugaban haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƴan kasuwa ta jihar Kano (AMATA) da kuma Alhaji Bashir Sule Dantsoho - Shugaban masu sayar da dabobi na jihar Kano, waɗanda dukkaninsu suka ce an samu hauhawar farashin kayan abinci babu ƙaƙƙautawa a ƙasar.
Sukari (Kwano ɗaya)
Farashin baya: Naira 2,300
Farashin yanzu: Naira 5,200 - 5,300
Nama (Kilo ɗaya):
Farashin baya: Naira 2,800 - 3,000
Farashin yanzu: 3,800 - 4,200
Majiya:
Sufuri
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bangaren sufuri na daga cikin bangarorin da shi ma aka samu tsefewar farashinsa tun bayan janye tallafin man fetur a Najeriya.
Inda gabanin cire tallafin motocin haya na masu zaman kasu a cewar Mallam Lawwali Dan Ada daya daga cikin shugabanin kungiyar direbobi motocin haya, a Najeriya reshen tashar Jabi da ke Abuja, ya ce:
Abuja zuwa Sokoto ya tashi daga naira 8,000 yanzu ya koma 16, 000.
Abuja zuwa Kano ya tashi daga naira 5,000 ya koma 10,000.
Abuja zuwa Kaduna ya tashi daga naira 3,000 ya koma 5,500.
Abuja zuwa Katsina ya tashi daga naira 6,000 ya koma 10, 000.
Sai dai a cewar Ɗan'ada tafiya a motocin safa na gwamnati ya fi rahusa, amma duk da haka nan an samu ƙari kamar yadda aka samu a motocin haya masu zaman kansu.
Misali:
Abuja zuwa Maiduguri ya tashi daga naira 6,500 ya koma 10, 000 a motar gwamnati.
Abuja zuwa Taraba ya tashi daga naira 13,000 ya koma 22,000 a motar gwamnati.
Abuja zuwa Adamawa ya tashi daga naira 12,000 ya koma 19,500 a motar gwamnati.
Man fetur
Gabanin dai shugaban na Najeirya Bola Ahmed Tinubu ya janye Tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, ana sayar da litar man fetur a babban birnin Najeriya Abuja kan kuɗi naira 195, yayin da jihohi irin su Kano da ke arewcin ƙasar ake sayar da litar kan naira kimanin 210.
A jihohin Maiduguri da Yobe da waɗanda ke makwabtaka da su an riƙa sayar da litar kan naira 220, sai Legas da ake sayar da litar kan naira 185, a Ibadan zuwa Fatakwal kuwa ake sayar da ita a kan naira 200.
A cewar Shugaban kungiyar dilllalan man fetur da iskar gas da ke arewacin Najeirya AROGMA, Bashir Dan Mallam jim kaɗan bayan shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar da ya karɓi mulki sai farashin ya yi tashin gwauron zabi, inda a watansa na farko farashin litar man man fetur ɗin ya kai naira 450 zuwa 520 a ɗaukacin fadin kasar.
Har ila yau dai Dan Malam ya ce farashin man fetur din ya sake tashi a jihohi irin su Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina da sauran jihohin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda ake sayar da litar man kan naira 710 daga watan Yuli zuwa yanzu.
Bashir Dan Mallam ya ƙara da cewa daga watan Yulin na 2023 kawo yanzu ana sayar da litar man fetur din a Kano kan naira 680 - N685, yayin da Abuja kuma ake siyar da litar kan naira 660 zuwa N670.
Yayin da sauran jihohin kasar na kudanci ake sayar da kowacce litar kan naira 700, in ji Dan Mallam.
Kayan gini
Su ma kayan gini na daga cikin abubuwan da suka yi tashin Gauron zabi a Najeriya.
Wasu daga cikin masu sayar da sumunti sun ce farashinsa na ci gaba da hauhawa a kusan kowane mako.
Siminti:
A cewar Auwal Umar daya daga cikin manyan dillalan sumunti a kasuwar simunti da ke titin Ajasa a Kano, ya ce hatta a makon da ya gabata an samu ƙarin kuɗin buhun sumunti na kamfanin BUA da kimanin naira 750.
Haka kuma a ranar Lahadin karshen mako ya ce an sake yin karin naira 1,500, wanda yanzu wasu ke sayar da shi kan naira 7,950, yayin da a wasu wuraren ake samun buhu ɗaya kan naira 8,000 saɓanin watannin da suka gabata, lokacin da aka sayar da buhun sumintin a kan naira 4,200 zuwa 4,500.
Kwanon rufi:
Shugaban masu sayar da kwanon rufi da dangoginsa Alhaji Bashir Uba Abdullahi ya ce gabanin hawan Bola Ahmed Tinubu kan mulkin Najeriya a watan Mayu, ana sayar da bandir din kwanon rufi mai ƙyalƙayali kan naira 38,000 amma a yanzu farashin ya kusa nunkawa inda ake sayar da shi kan naira 62,000.
Yanzu haka dai gwamnatin Najeriyar na cewa tana bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta daƙile yawaitar farashin kayan masarufi a ƙasar.
Lokacin wani bayani da ya yi a zauren Majalisar wakilan ƙasar a ranar Talata, sa'ilin da ya amsa sammacen da majalisar ta yi masa kan matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke ciki, gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso ya ce bankin na ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin an shawo kan lamarin.
Sai dai ya bayyana cewa ba za a samu sa'ida yadda ya kamata ba har sai Najeriya ta ƙara yawan kayan da take fitarwa daga waje tare da rage yawan kayan buƙatu da take shigowa da su daga ƙasashen na ƙetare.
Sai dai duk irin waɗannan kalamai da sukan fito daga bakin jami'an gwamnati ba kasafai suke yin ma'ana a zukatan al'ummar ƙasar ba, musamman masu ƙaramin ƙarfi waɗanda ke shan wahala wajen neman abin da za su ci a kowace rana.











