Ko yajin aikin ƴan kasuwar Najeriya zai samar da mafita kan tsadar rayuwa?

...

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, Abuja

Matsalar karyewar darajar kudin Najeriya - naira da tashin farashin dala a kasar na ci gaba da tayar da kura inda bangarori da dama ke nuna takaici kan yadda lamarin ke jefa rayuwarsu cikin karin kunci da tsadar rayuwa.

Tsadar kayan masarufi sakamakon tashin farashin dalar dai ta sa gamayyar kungiyar manyan kasuwanni a Kano yin barazanar rufe dukkan kasuwannin jihar.

Ko a makon da ya gabata, 'yan canji a Abuja, babban birnin Najeriya sun dakatar da hada-hadar musayar kudi saboda yadda dala ta kara tsada yayin da takwarorinsu a Kano suka rage sa'oin da suke aiki.

A wannan makala za mu duba hangen masana kan ko daukar irin wannan mataki daga wurin 'yan kasuwa ne maslaha dangane daa yanayin da ake ciki.

Dr Shamsuddeen Muhammad, kwararre kan fannin tattalin arziki ya ce daukar irin wannan mataki na shiga yajin aiki da 'yan kasuwa ke yi ba zai sauya halin da ake ciki ba.

Ya ce a kowane lokaci dan kasuwa yana duba ribar da zai samu, "duk abin da ya ga zai zamar masa tasgaro ga kasuwancinsa wannan zai janyo ya dauki matakin da yake gani shi ne mafita a gare shi."

Ya kara da cewa a kowane yini, kaya suna kara daraja ne ba wai sauki suke yi ba ta fuskar farashi.

Tasirin matakin ga tattalin arzikin Najeriya

A cewar masanin, irin wannan matakin yana iya yin tasiri ta fuska biyu - Gajere da dogon zango.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya yi tambaya kan yadda "yanzu ma da ake sayar da kayan, ya 'yan kasa suke siyan su ballantana a ce an dakatar da sayar da wadannan kayayyaki?."

Ya ce matakin dole zai sa farashin kayayyaki zai tashi sannan kayan za su yi karanci a kasuwa.

"Yan kadan din da za su rika siyarwa su kuma za su caji farashi mai yawa saboda watakila karancin kayan da bukatarsu za ta yi musu yawa", in ji masanin.

Da yake magana game da irin illar da hakan zai haifar ga yanayin da ake ciki, Dr Shamsuddeen ya bayyana cewa a gajeren zango talaka zai dada shiga wahalar da ta fi wadda ake ciki.

Zai iya jefa mutane cikin halin yunwa da karuwar fatara sannan ko halin ko da 'kudinka sai da rabonka'.

Sai dai ya ce idan aka duba dogon zango, matakin na iya amfanar da kasa saboda zanga-zanga irin haka ba sabon abu ba ne.

A cewarsa, hakan zai sa gwamnati watakila ta sake karatun ta nutsu domin sauya wasu daga cikin manufofinta da ake ganin suna da hannu a ci gaba da karyewar darajar naira da kara tashin dala.

Ya kamata gwamnati ta sake nazarin manufofinta...

Dr Shamsuddeen Muhammad wanda malami ne a jami'ar Bayero ya ce wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnati take bijiro da su a kan tattalin arzikin Najeriya na ba da gudummawa ga halin da ake ciki na hauhawar farashin kayayyaki sanadin tashin farashin dala.

Ya ce "Matakan da gwamnati ta dauka na rage darajar naira tsawon lokaci shi ne babban dalilin da ya sa su ma 'yan kasuwa suke yin abin da suka ga dama."

Ya ba da misali da yadda babban bankin Najeriya ya sha rage darajar naira da kuma irin tasirin hakan ga hada-hadar kasuwanci.

Masanin ya bayyana cewa "shi dan kasuwa ba yadda zai yi, in dai akwai irin tsare-tsaren nan dole ya zama shi ma abin da yake caja ya karu ko ya shigo da kayan daga waje,"

"Ko da ma a cikin gida ya sana'anta tun da akwai matsala ta gogayya - idan kayan waje suka yi tsada, mutane za su dawo su raja'a kan kayan da ake yi a Najeriya,"

"Ka'ida ce ta tattalin arziki cewa duk lokacin da bukatar abu ta yi yawa dole farashinsa ya daga kuma su 'yan kasuwa ba masu sadaka ba ne, suna yi don su ci riba." in ji masanin.

Mafita...

Dr Shamsuddeen ya ce babbar mafita ita ce a koma asali inda ya ba da misali da yadda gwamnati ta bijiro da wasu tsare-tsare lokaci guda - cire tallafin mai da kyale kasuwa ta yi wa naira daraja.

A cewarsa manufofin biyu suna da alaka da cinikayya da kasashen waje "tun da man fetur din nan shigo da shi muke, ita ma naira tana da alaka da kudaden kasar waje."

"A lokaci guda darajar naira ta fadi kuma 'yan kasa za su sayi makamashi a farashin kasuwa sai abin ya taru ya yi wa 'yan kasa yawa" ya zama mutane ba sa iya biyan bukatunsu da abin da ke hannunsu.

Ga 'yan kasuwa kuwa, Dr Shamsuddeen ya ce dakatar da daina siyar da kaya gaba daya ba zai amfanar da su da tattalin arzikin kasa ba kasancewar "idan ka dakatar da sayar da kaya kai kanka ka tsayar da komai kuma kana da bukatu na yau da gobe."

"Kana da ma'aikata a karkashinka wadanda za ka ci gaba da biyansu sai dai idan sallamarsu za ka yi. Idan ya zama cewa an rufe an daina sayar da komai wannan matsala su ma za ta dawo kansu - rasa abin da za yi amfani da shi na yau da gobe sannan watakila na bayu ga durkushewar tattalin arziki." in ji Dr Shamsuddeen.