Yadda cire tallafin lantarki a Najeriya zai shafe ku idan farashin ya ninka uku

Asalin hoton, TCN
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
Ta tabbata gwamnatin Najeriya ta kara kudin lantarki bayan da a ranar Larabar nan hukumar da ke kula da wutar lantarki a Najeriyar ta ce ta ƙara kuɗin wutar ga abokanan hulɗarsu da ke ajin Band A - masu samun wuta tsawon sa'a 20 a rana.
Mataimakin shugaban hukumar, Musuliu Oseni ya bayyana cewa a yanzu kwastomomin za su biya N225 duk sa'a ɗaya inda a baya suke biyan N66.
A taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Laraba, Oseni ya ce abokan hulɗarsa da ke samun wuta tsawon sa'a 20 a rana su ne kashi 15 cikin 100 na kwastamomin hukumar a Najeriya.
Ya ƙara da cewa hukumar ta kuma sauke kwastamomin da ke ajin Band A zuwa Band B masu samun wuta ƙasa da sa'a 20 a rana saboda rashin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki na basu wutar da ta kamata.
Ya bayyana cewa ƙarin ba zai shafi kwastamomin da ke sauran matakan ba.
Azuzuwa biyar na masu shan lantarki
- Ajin A: Suna samun wuta na tsawon awa 20 a kullum
- Ajin B: Suna samun wuta ta tsawon awa 16 a kullum
- Ajin C: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 12 a kullum
- Ajin D: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 8 a rana
- Ajin E: Suna samun wutar lantarki ta tsawon awa 4 a rana
Abin da ya bayyana a fili yanzu shi ne cewa ba kowa da kowa cire tallafin zai shafa ba, masu amfani da wutar lantarki kashi 15 ne kawai, amma kuma su ne ke shan kashi 40% na wutar lantarki a Najeriya matakin zai shafa.
Ko da yake ba a fayyace ranar da sabon ƙarin kuɗin lantarkin zai fara aiki ba.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta Bloomberg ta ruwaito wata majiya da ke cewa ƙarin zai fara aiki ne a cikin wannan wata na Afrilu.
'Bashi ya yi wa gwamnati yawa'
Tun a tsakiyar watan Fabrairu ne, ministan lantarki na Najeria, Adebayo Adelabu ya sanar da cewa ƙasar ba za ta iya ci gaba da biyan tallafi a kan wutar lantarki ba saboda tarin basukan da kamfanonin samar da lantarki ke bin gwamnati.
Ya ce basukan da kamfanonin wuta da masu samar da iskar gas ke bin gwamnati sun zarce naira tiriliyan uku.
A cewarsa, ɗaukan matakin ya zama dole domin gwamnati ta samu damar magance basukan da ke kanta waɗanda ke ƙaruwa.
Sanarwar ta Adelabu ta janyo ce-ce-ku-ce da zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta kasancewar har yanzu ƴan Najeriya na fuskantar tarin ƙalubale tun bayan da gwamnatin Bola Tinubu ta janye tallafin man fetur - lamarin da ya jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin rayuwa da hauhawar farashi.
Bari mu duba abin da matakin ke nufi da makomar lantarki idan aka cire tallafin da kuma irin tasirin da zai yi ga ƴan Najeriya.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da Asusun Lamuni na Duniya, IMF ya shawarci Najeriya ta dakatar da biyan tallafin man fetur da na wutar lantarki.
Da ma dai shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu a kan dokar bunƙasa ayyukan lantarki ta Electricity Act Amendment Bill wadda ta sahale wa ƴan kasuwa da ɗaiɗaikun mutane damar sanya hannun jari a harkar samar da lantarki.
Kafin nan dai gwamnati ce kawai take da iko a harkar samarwa da dakon lantarki da raba ta a ƙasar.

Asalin hoton, getty images
Wane tasiri cirewar za ta yi?
Wani masani kuma kwararre a fannin wutar lantarki a Najeriya, Injiniya Fakhruddeen BB Farouk ya shaida wa BBC cewa "babban tasirin cire tallafin nan shi ne gwamnati za ta cire hannunta daga harkar wutar lantarki.
"Hakan na nufin gwamnati za ta daina zuba kuɗi a matsayin tallafi, inda za ta karkatar da kudin kan wasu ayyukan daban".
Gwamnati dai na zuba makudan kudade wajen sayen kayan aiki da gyara su da kuma sanya tallafin rage radadin asarar da kamfanonin da ke samar da kuma sayar da wutar ke yi.
Bangarori uku ne dai suke samar da wuta daga farko har ta zo ga mai amfani da ita kamar haka:
- Kamfanonin samar da lantarki: Su ne kamfanonin da ke samar da wutar tun daga tushe. Su ne mamallakan tashoshin samar da wutar. Kamfanonin dai ba na gwamnati ba ne.
- Kamfanin dillacin lantarki: Wannan ne yake dakon wutar daga tashoshin wutar zuwa inda za a raba ta. Ana dakon wutar ne ta hanyoyin turaku da wayoyin da ake gani a kakkafe a fadin kasa. Wannan mallakar gwamnati ne.
- Kamfanonin rarraba lantarki: Waɗannan ne kamfanonin da ke sayar da wutar ga jama'a, bayan sun saye ta daga kamfanonin da ke samar da ita. Su ne irin su AEDC, KEDCO da dai sauran su.
Ana dai samar da kaso 80 na wutar lantarki daga iskar gas inda 20 kuma ke samuwa daga ruwa.
Gwamnatin Najeriya na cike gibin asarar da kamfanonin da suke samar da wuta da masu sayar da wutar suke yi.

Asalin hoton, Getty Images
Wani ma'aikacin kamfanin da raba wutar lantarki na Abuja wato AEDC ya shaida wa BBC cewa farashin ka iya ninkawa sau biyu ko fiye da haka.
"Ai kamar man fetur ne. Lokacin da aka cire tallafin nasa sai farashin lita ya ninka sau uku. To irin haka shi ma farashin wutar zai zama."
Shi ma Engineer Fakhruddeen BB Farouk ya ce "yanzu wuta za ta zama iya kudinka iya shagalinka domin kudin zai karu sosai-sosai.."
Da ma dai ko a yanzu babu farashin bai-ɗaya na wutar, inda farashin kan bambanta daga gari zuwa gari da kuma daga unguwa zuwa unguwa.
Ko a watan Yulin 2023 sai da kamfanoni masu dillancin wutar suka yi karin kudin wutar da kaso 40.
Ko cire tallafin zai magance matsalar rashin wuta a Najeriya?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana da kwararru a sha'anin samar da wutar lantarki irin su Fakhruddeen BB Farouk sun shaida wa BBC cewa "cire tallafin abu ne mai kyau" da zai taimaka wa Najeriya wajen karkata kudade zuwa ayyukan kasa.
To sai dai sun nuna rashin tabbas dangen da ko cire tallafin zai magance matsalar karancin wutar lantarkin a Najeriya.
Engineer Fakhruddeen BB Farouk ya ce "abu daya ne kawai zai tabbatar da an samu tsayayyar wutar lantarki a Najeriya, wato idan aka daina rashawa da cin hanci. Saboda ai dama tun farko ma batun rashawar ne ya lalata sha'anin wutar lantarkin".
Gwamnatoci da dama dai sun dade suna fitar da makudan kudade ana zubawa a harkar wutar lantarki da manufar samar da isasshiyar wutar da kasar take bukata.
Duk da cewa Najeriya tana da karfin samar da yawan wutar lantarki mai yawan megawatts 22,000 amma har yanzu kasar ba ta iya cimma rabin abin da ya kamata ta samar ba.
A watan Nuwamban 2022 ne Najeriya ta iya cimma megawatts 4,594.6.
Yayin da ƴan Najeriya ke zulumin abin da cire tallafin wutar lantarkin zai haifar idan aka aiwatar, da dama ƴan kasar wadanda suka sakankance cewa babu makawa sai an cire tallafin, suna fatan hakan zai kawo karshen matsalar wuta a kasar da ta fi kowace yawan jama'a a Afirka.











