Mene ne babban layin wutar lantarki na Najeriya kuma yaya yake aiki?

Asalin hoton, TCN
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
'Yan Najeriya na ci gaba da shafe ranaku da dararensu a lokuta daban-daban ba tare da wutar lantarki ba na tsawon kwanaki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasa da ake kira National Grid a turance.
Da ma dai ɗaukewar lantarki ba sabon abu ba ne a Najeriya, yayin da layin lantarkin ya lalace sau da yawa a cikin shekarar nan.
A ranar Lahadi da ta gabata, kamfanonin da ke raba lantarkin ga kwastomominsu suka tura wa 'yan Najeriya da dama irin wannan saƙon cikin harshen Ingilishi:
"Gare ku abokan hulɗarmu masu daraja, muna masu baƙin cikin sanar da ku lalacewar layin wuta babban layin lantarki na ƙasa [National Grid].
"Wannan ya shafi dukkan ayyukanmu na ƙoƙarin biyan buƙatunku da kyau.
"Muna roƙunku afuwarku yayin da muke ci gaba da aikin haɗin gwiwa da [kamfanin rarraba lantarki] TCN don shawo kan matsalar."
Ƙarshen makon da ya gabatan ya zama karo na kusan shida da babban layin lantarkin ke samun matsala cikin wata biyu.
A wannan maƙalar za mu yi duba ne kan Mene ne National Grid? Me ya sa yake lalacewa? Ta yaya ake tarawa da rarraba lantarkin?
Ƙarin wasu labaran da za ku so ku karanta
Mene ne babban layin lantarki na Najeriya?

Asalin hoton, TCN
Babban layin wutar lantarki na Najeriya - power grid a Turance - gungun layuka ne da suka haɗa tashoshin samar da lantarki da ke bai wa dukkan sassan Najeriya wuta.
A taƙaice, wata ma'dana ce da ke ɗauke da dukkan lantarkin da ake sha a Najeriya. Haka nan, ba wani wuri ba ne guda ɗaya, tarin layuka ne a wurare daban-daban.
An tsara shi ne don ya yi aiki ta wasu taƙaitattun hanyoyi musamman dangane da yawan wutar da ake da ita, da tsaron lafiyarsa.
Saboda haka duk sanda ya fita daga yanayin da ya saba zama na kwanciyar hankali, ayyukan da yake za su samu matsala kuma hakan kan sa ya lalace.
Na'urorin da ke ba da wutar lantarkin kan kashe kansu da zarar sun fuskanci cewa suna cikin matsala.
Hakan ka iya nufin ɗaukewar wutar gaba ɗaya ko kuma na wani ɓangare.
Kazalika, yanayi - iska ko ruwa ko sanyi ko zafi - kan shafi aikin babban layin a wasu lokuta, abin da ya sa ke nan ake yawan ɗauke wuta idan aka fara iska mai ƙarfi a lokuta da dama.

Sau nawa babban layin lantarki na ƙasa ya lalace a 2022?

Asalin hoton, TCN
Najeriya ta fuskanci lalacewar babban layin lantarki na ƙasa a lokuta da dama a 2022 kaɗai.
Rahotanni na cewa hakan ta faru aƙalla sau biyar, wasu na cewa sau bakwai, wasu ma na cewa ya fi haka.
Lalacewar watan Janairu: An samu lalacewar layin lantarkin a ranar 17 ga watan Janairu. Kwana ɗaya bayan an gyara, ya sake lalacewa tare da jefa kusan dukkan ƙasar cikin duhu.
Lalacewar watan Maris: A ranar 14 ga watan Maris ma layin wutar ya sake lalacewa. Kazalika, kwana ɗaya bayan haka ya kuma lalacewa bayan an gyara.

Asalin hoton, TCN
Lalacewar Afrilu: Babban layin lantarki ya lalace ranar Juma'a, 8 watan Afrilu da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin Najeriya.
A ranar Lahadi, 13 ga watan Yuni Najeriya kamfanin rarraba wutar lantarki ya fuskanci lalacewar babban layin na baya-bayan nan.
Amma an gyara matsalar da misalin ƙarfe 11:00 na daren amma ba nan take wutar ta karaɗe wurare ba.
Ta yaya ake samun lantarki a Najeriya?

Asalin hoton, TCN
Babban aikin kamfanonin da ke tattara wutar lantarki a Najeriya shi ne tara ta domin raba wa masu amfani da ita wato kwastomomi.
Akwai kamfani shida da ke aikin tara lantarki, waɗanda ake kira Generating Companies (GenCos), da kuma tashoshin lantarki 28.
Uku daga cikin tashoshin na amfani ne da ruwa wajen samar da lantarki, yayin da sauran 25 ɗin ke amfani da iskar gas.
Dukkan kamfani shida na GenCos na 'yan kasuwa ne. Su ne ke da kashi 60 cikin 100 na hannun jari a sashen, gwamnati kuma na da kashi 40.
Tsarin rarraba lantarki a Najeriya ya ƙunshi rumbu biyu na 330 kV da 132 kV da kuma ƙananan tasoshinsu.
Tasoshin da ke aiki da iskar gas na yankin kudancin ƙasar - saboda sun fi kusa da wuraren haƙo man fetur - su kuma masu aiki da ruwa suna arewaci - a Jebba, da Kainji, da Shiroro duka a Jihar Neja.

Yadda ake rarraba lantarki a Najeriya

Asalin hoton, TCN
Bayan GenCos sun samar da lantarkin, sai kuma kamfanin raba lantarkin ya yi ɗauke ta zuwa inda za a raba wa masu amfani da ita.
Daga nan kuma sai kamfanonin rarraba lantarki da ake kira Distribution Companies (DisCos) su bai wa 'yan Najeriya.
Kamfanin Rarraba Lantarki na Najeriya wato Transmission Company of Nigeria (TCN), shi ne kaɗai ke da haƙƙin rarraba wutar kumana gwamnati ne, yayin da su kuma DisCos ke aiki da TCN.
Kazalika, akwai hukumar Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC) mai kula da dukkan ayyukan samarwa da rarrabawa da amfani da lantarkin a Najeriya.

Ta yaya ake gyara babban layin idan ya lalace?

Asalin hoton, TCN
A cewar kamfanin samar da lantarki na Najeriya, Nigerian Electricity System Operator (NESO), lalacewar babban layin na nufin ɗaukewar wuta a ƙasa baki ɗaya, yayin da kuma samun tangarɗar layin ke nufin rasa wuta a wasu ɓangarori na ƙasa.
Wata majiya a kamfanin TCN ta faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa lalacewar babban layin ba abu ne da ke buƙatar gyara ba idan hakan ta faru, sai dai a sake kunna layin wato mayar da shi bakin aiki.
"Babu wanda zai iya faɗa muku yawan kuɗin da ake kashewa saboda ba haka ake yi ba.
"Ba a kashe kuɗi, ba abin gyarawa ba ne. Kamar dai a ce kun kashe injin jannareto dinku sai kuma ku sake kunna shi," a cewar majiyar.
"Saboda haka ba wai ma'aikata ne ɗebo kayan aiki su aikin gyara ba."













