Toungo: Karamar hukumar da ba ta taba ganin lantarki ba tsawon shekara 25
Ku latsa hoton da ke kasa don kallon bidiyon:
Mazauna karamar hukumar Toungo dake jihar Adamawa basu taba ganin wutar lantarki a garin ba tun da aka kafa shi daruruwan shekaru da suka gabata.
Garin ya zama karamar hukuma ne bayan raba tsohuwar jihar Gongola inda aka samar da jihohin Adamawa da Taraba a 1991.
To sai dai labarin ya sauya a farkon shekarar 2021 bayan da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya kaiwa garin na Toungo wuta sakamakon alkawarin hakan da ya yi a lokacin yakin neman zaben shekara ta 2019.
A wannan bidiyon mazauna garin na nuna farin ciki da samun wannan gagarumin ci gaba.
Tuni matasa a karamar hukumar suka shiga sahun 'yan uwansu na sauran yankuna masu wutar lantarki wajen yin wasanni da ake bugawa da kwamfuta.
Ko da yake a yanzu garin na Toungo ya samu wutar lantarki, amma matsalar da mutane sukace suna fuskanta itace yawaitar daukewar wutar.
Suna fatan wata rana za su shiga sahun yankuna da ke samun wuta kusan ko wani lokaci.