Nijar ta shiga matsalar lantarki bayan katsewa daga Najeriya

Asalin hoton, NIGERIA ELECTRICITY
Niamey, babban birnin Jamhuriyar Nijar da kuma sauran wasu manyan birane kamar Maraɗi da Zinder sun fara fuskantar katsewar wutar lantarki.
Mutane na samun wutar lantarki na ne na tsawon kimanin sa'a ɗaya a wani lokaci daga nan sai a ɗauke tsawon sa'a huɗu ko biyar ba tare da an sake kawowa ba.
Wakiliyar BBC ta ce tsarin bayar da lantarki a babban birnin ƙasar ya koma zuwa bai wa wani ɓangare, a kuma kashe wa wani ɓangare a lokaci guda.
Kamfanin sarrafa lantarki na Nijar (Nigelec) ya ce matsalar na faruwa ne sakamakon katsewar lantarkin da ake samu daga Najeriya. Ƙasar dai wadda shugabanta Bola Tinubu ke jagorantar ƙungiyar Ecowas na ɗaukar wannan mataki ne a wani ɓangare na takunkuman da ƙungiyar ƙasashen ta Afirka ta Yamma ta ƙaƙaba wa Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.
Gwamnatin Najeriya dai ba ta tabbatar da iƙirari ko musanta shi ba zuwa yanzu.
Sai dai, majiyoyi daga Abuja sun ce hukumomin ƙasar sun katse wasu layukan wutar lantarki zuwa Jamhuriyar Nijar, ba tare da yin cikakken bayani ba.
Najeriya, ita ce ƙasa mafi samar da lantarki ga Jamhuriyar Nijar.

Asalin hoton, AFP
Gwamnatin mulkin sojin Nijar dai ta sanar da buɗe kan iyakokin ƙasar da makwabtanta biyar, mako guda bayan kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Manyan ƙasashen duniya da ƙungiyoyi da dama sun yi Allah-wadai da juyin mulkin, sannan ana fargabar ɓarkewar rikice a yankin Sahel sakamakon ƙwace ikon.
Cikin wata sanarwa da kakakin sojojin Kanal Manjo Amadu Abdurahamane ya karanta a gidan talbijin na ƙasar ya ce ''daga ranar 1 ga watan Agusta, an buɗe iyakokin ƙasar da ƙasashen Algeriya da Burkina Faso da Mali da Libya da kuma Chadi''.
Sojojin sun sanar da rufe kan iyakokin ne a makon jiya, daidai lokacin da suka sanar da kifar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum.
Kan iyakokin da aka sanar da buɗewa galibi, yankunan hamada ne masu nisa.
To sai dai har yanzu manyan hanyoyin hulɗar kasuwancin ƙasar na ci gaba da zama a rufe saboda takunkuman da ƙungiyar Ecowas ta sanya wa Nijar.
Juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar shi ne na bakwai da aka samu cikin ƙasa da shekara uku a yankin Afirka ta Yamma, inda wasu ƙasashen da aka samu juyin mulkin suka dunƙule waje guda domin nuna adawa da matakin da sauran ƙasashen yankin 15 ke yunƙurin ɗauka a kan Nijar.
Naɗa gwamnonin Jihohi
A cikin daren Talata ne, sojoji masu juyin mulki suka sanar da naɗa gwamnonin jihohin ƙasar bakwai.
Wakiliyar BBC da ke birnin Yamai ta ce matakin na nufin gwamnatin sojin Nijar ta kawo ƙarshen mulkin gamnonin da suka yi aiki ƙarƙashin Shugaba Bazoum.
Sanarwar sojojin ta ce sabbin gwamnonin jihohin ƙasar su ne:
- Birgediya Janar Ibro Boulama - gwaman Agadez
- Birgediya Janar Iro Oumarou - sabon gwamnan jihar Dosso
- Birgediya Janar Ibrahim Bagadoma - jihar Diffa
- Birgediya Janar Abdou Assoumane Harouna - sabon gwamnan Yamai
- Manjo Kanal Oumarou Tawayé - sabon gwamnan jihar Tahoua
- Laftanar Kanal Maïna Boukar - sabon gwamnan jihar Tillabery.
- Kanal EF Labo Issoufou - sabon gwamnan jihar Zinder
- Sai babban kwanturolan 'yan sanda, Issoufou Mamane - sabon gwamnan jihar Maradi
Kasashen Turai na ci gaba da kwashe mutanensu

Asalin hoton, Getty Images
Wasu ƙasashen Turai na ci gaba da kwashe mutanensu da ke Nijar, bayan da ƙasashen Mali da Burkina Faso, waɗanda su ma ke ƙarƙashin mulkin soji suka yi barazanar shigar wa Nijar faɗa, matuƙar Ecowas ta ɗauki matakin soji a kan ƙasar.
Tuni sawun farko na jiragen sojojin Faransa da Italiya ɗauke da fararen hula mafi yawancinsu Faransawa suka sauka a biranen Paris da Roma a ranar Laraba.
Wani Bafaranshe da ke cikin mutanen da aka kwashe ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ''An shiga wani mawuyacin yanayi a Nijar, amma mun ji daɗi tun da mun fito daga ƙasar, mun dawo gida''.
''Muna fatan al'amura za su daidaita cikin kwanaki ko makonni ƙalilan masu zuwa'', in ji shi.
Manyan Ƙasashen Yamma kamar Faransa da Amurka da Jamus da Italiya na da sojoji masu yawa a Nijar da ke yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya ko suke horar da dakarun ƙasar, da kuma taimaka wa sojojin Nijar wajen yaƙar masu iƙirarin jihadi irin su al Qaeda da ISIS.
Kawo yanzu babu sanarwa daga waɗannan ƙasashe game da janye dakarun nasu.
Ministan tsaron Jamus ya ce babu wata damuwa game da tsaron sojojin Jamus da ke Nijar.
Ministan harkokin wajen Italiya, Antonio Tajani ya ce Ƙasashen Yamma ba za su ɗauki matakin soji don tilasta wa sojojin Nijar mayar da mulki hannun farar hula, don kuwa a cewarsa yin hakan ''tamkar sabon mulkin mallaka ne''.
Nijar ce ƙasa ta bakwai mafi arziƙin ma'adanin Uranium a duniya, makamashin da ake amfani da shi wajen samar da makamashin Nukiliya kuma ana amfani da shi a matsayin sinadarin magance cutar daji.
A farkon makon nan ne, Hukumar Tarayyar Turai ta ce tana da wadataccen makamashin Uranium, domin kauce wa fargabar raguwar sidanarin da za a iya samu sakamakon rikicin juyin mulkin Nijar.
End of Wasu ƙarin labarai masu alaƙa
Taron manyan hafsoshin tsaron Ecowas
Al'amuran na faruwa ne yayin da manyan hafsoshin tsaro daga ƙasashen Ecowas ke fara taro ranar Laraba inda za su tattauna batun juyin mulkin na Nijar, da kuma irin matakin da za su iya ɗauka a masu juyin mulkin.
Taron wanda ke gudana a Abuja, babban birnin Najeriya, na cikin matsayar da aka cimma a taron da ƙungiyar Ecowas ta yi a Abuja ƙarshen makon jiya, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar kuma shugaban Najeriya Bola Tinubu.
A baya dai Ƙungiyar ta gargaɗi sojin da suka yi juyin mulkin su gaggauta mayar da Shugaba Mohamed Bazoum kan karagar mulki cikin mako ɗaya ko kuma ƙungiyar ta yi amfani da ƙarfin soji a kansu.
A daidai wannan lokaci kuma ana sa ran wani ayari daga ƙungiyar Ecowas zai isa birnin Niamey domin gudanar da tattaunawa da sojojin da suka yi juyin mulkin a ƙarkashin jagorancin Janar Abdourahmane Tiani.










