ECOWAS ta bai wa sojin Nijar wa'adin kwana bakwai su mayar wa Bazoum mulki

Asalin hoton, State House
Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS sun bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa'adin kwana bakwai su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki.
A taron da ƙungiyar ta gudanar a Abuja babban birnin Najeriya ranar Lahadi da rana, ta yi kira ga hukumomin sojin na Nijar su gaggauta sakin shugaba Bazoum, tare da mayar da mulki hannun farar hula a ƙasar.
Haka kuma kungiyar ta ce ta yi watsi da takardar ajiye aiki da aka yi iƙirarin cewa daga shugaba Bazoum take.
ECOWAS ta kuma yi Allah wadai da ci gaba da tsare shugaban na Nijar da sojojin ke yi.
Kungiyar ta kuma amince da taron gaggawa na manyan hafsoshin tsaron ƙasashen yankin Afirka ta yamman.
Abubuwan da taron ya cimma
- Kungiyar ta ɗauki matakin rufe kan iyakokin tudu da na sama tsakanin Nijar da mambobin kungiyar.
- Haramta wa jiragen sama da suka taso ko suka nufi Nijar ketawa ta sararin samaniyar ƙasashen ƙungiyar ECOWAS.
- Dakatar da hulɗar kasuwanci da ta kuɗi tsakanin Nijar da ƙasashen ƙungiyar.
- Datse hanyar huldar cinikayyar makamashi tsakanin kasar da ƙasashen ƙungiyar
- Ƙwace kadarorin Nijar da ke ƙasashen ƙungiyar, tare da riƙe kuɗin ƙasar amanyan bankuna da bankunan kasuwanci da ke ƙasashen kungiyar.
- Dakatar da duk wani mataki na tallafin kuɗi ko amfani da duk wasu cibiyoyin kuɗi tsakanin ƙasar da ƙungiyar.
- Hana jami'an sojin da ke da hannu a kifar da gwamnatin shiga kasashen ƙungiyar tare da ƙwace kadarorinsu da ke ƙasashen kungiyar.
- Haka kuma an sanya makamanciyar wannan doka ga iyalan sojojin da kuma fararen hular da suka amince da shiga gwamnati,ko suka yi aiki a hukumomin da sojojin suka kafa.
Tun kafin gudanar da taron fadar shugaban Najeriya, ta ce mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Harris da Babban Sakatare Janar na MAjalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres a tattaunawar da suka yi daban-daban da shugaba Tinubu, sun bayyana goyon bayan Amurka da kuma MDD kan matsayin ƙungiyar Ecowas da shugaban na Najeriya game da taron.
Ita ma ƙungiyar haɗin kan Afirka ta AU a nata ɓangare ranar Asabar, ta ce ta bai wa sojojin wa'adin kwanaki 15 su koma barikokinsu, su kuma maido da mulkin farar hula a ƙasar da ke yankin yammacin Afirka.
Can a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ɗaruruwan masu zanga-zanga ne suka taru a harabar ofishin jakandancin Faransa a ƙasar domin nuna goyon bayansu ga sojojin da suka kifar da gwamnatin farar hula.
Sojojin ne dai cikin wata sanarwar da suka watsa a gidan talbijin na ƙasar ranara Asabar suka yi kira ga mutanen da su fito su yi zanga-zanag domin nuna goyon bayansu ga sojoin.
Haka kuma sojojin sun yi kira ga ƙasar Rasha da ta kawo musu ɗauki, tare da bukatar ƙasar Faransa da sauran ƙasashen yamma da ke ƙasar da su fice da Nijar ɗin.










