Fadar Shugaban ƙasa ta musanta raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu

Bola Tinubu

Asalin hoton, PRESIDENCY NG

Lokacin karatu: Minti 2

Fadar shugaban ƙasar Najeriya ta musanta rahotannin da ke nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin fitar da shi zuwa asibiti a ƙasar waje.

A makon da ya gabata ne dai cibiyar aikin jarida mai binciken ƙwaƙwaf ta Najeriya, ICIR ta rawaito cewa wasu majiyoyinta sun tabbatar mata da cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na ta shirye-shiryen fitar da shugaba Tinubu zuwa ƙasar wajen domin neman magani.

Cibiyar kamar dai yadda ta wallafa a shafinta na intanet ta ce "rahotanni na nuna cewa shugaba (Tinubu) na kwance a gado ba ya iya zuwa ko'ina abin da ya janyo rashin gudanar da al'amuran shugabanci. Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilci shugaban a wasu ayyukan gwamnati."

ICIR ta kuma rawaito wani jami'i a fadar shugaban ƙasar da ke cewa an soke aikace-aikace da dama da ya kamata shugaban ya gudanar a farkon makon da ya gabata.

Martanin fadar shugaban ƙasa

Mai magana da yawun shugaba Tinubu, Abdu'aziz Abdul'aziz ya shaida wa BBC cewa rahotannin ba gaskiya ba ne.

"Babu ƙanshin gaskiya a waɗannan maganganun. Yanzu haka ma yana ofis", in ji Abdul'aziz.

Da ma dai tun a farkon makon da ya gabata sai da Bayo Onanuga mai taimaka wa shugaba Tinubun kan harkokin watsa labarai shi ma ya musanta batun a tattaunawarsa da ICIR.

" Shugaba Tinubu yana aikinsa. Yana da salon gudanar da aiki iri-iri. Wataran ma yana iya yin aiki daga gida. Zancen gaskiya ma ya fi yin aiki daga gida a kan na ofis. Duk mutumin da ke yin wannan batu to lallai ya sani labarin ƙanzon kurege yake yaɗawa.

Dalilan raɗe-raɗin rashin lafiyar Tinubu

Sakamakon rashin ganin shugaban a wasu ƴan kwanaki ya sa ƴan Najeriya musamman kafofin watsa labarai ya sa suka fara raɗe-raɗin.

  • Rashin ganin shugaba Bola Tinubu a lokacin karrama ƴan ƙungiyar ƙwallon kwando ta mata ta Najeriya, D'Tigress da mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilta, a ranar 3 ga watan Agusta ne ya fara janyo dasa ayar tambaya.
  • Tun dai ranar Juma'ar 1 ga watan Agusta ba a ƙara ganin gilmawar shugaba Tinubu ba, lokacin da ya halarci buɗe taron ƙoli kan aikin jarida domin raya ƙasa.
  • Kafin nan kuma Bola Tinubu ya halarci bikin karrama ƴan ƙungiyar ƙwallon mata ta Najeriya, Super Falcons bayan samun nasarar da suka yi a gasar ƙwallon mata ta Afirka ta WAFCON a Morocco.
  • To sai dai kuma a ranar 6 ga watan Agusta fadar shugaban ta saki sanarwa dangane da shirin samar da lafiya kyauta ga marasa ƙrfi waɗanda suka yi ritaya da kuma ƙarin kuɗin fanshonsu, inda sanarwar ta kunshi hotunan shugaban tare da Darekta Janar ta hukumar fansho, Omolola Oloworaran duk da cewa ba a faɗi lokacin da ganawar ta gudana ba.
  • Wani dalilin da ya sa ake raɗe-raɗin rashin lafiyar shugaban ita ce rashin gudanar da taron majalisar zartarwa da ake duk ranar Litinin, duk da cewa ba a kowane mako ake gudanar da taron ba.