Yadda za ka gane bidiyon da kake kallo na AI ne

Asalin hoton, Serenity Strull/ Getty Images
- Marubuci, Thomas Germain
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Kafofin sadarwa a cike suke da faye-fayen bidiyo da asali na ƙirƙirarriyar basira ne wato AI. Hanya ɗaya da za ka gane cewa bidiyon na bogi ne shi ne ganin yanayin ingancin hoton.
Wataƙila an taɓa ruɗar ka wajen aminta da bidiyon bogi. A cikin wata shida da suka gabata, an samu ƙaruwar yaɗuwar bidiyon ƙarya.
Amma duk da haka, akwai wasu alamomi da za ka lura da su. Daga ciki akwai wanda ya fi muhimmanci: Da zarar ka ga bidiyo wanda hotonsa babu inganci, to lallai ka kula sosai. Akwai yiwuwar bidiyo ne na ƙirƙirarriyar basira.
"Ingancin hoto muke fara dubawa," in ji Hany Farid, farfesan kimiyyar kwamfuta a Jami'ar California, kuma shugaban kamfanin tantance bayanan ƙarya na GetReal Security.
Amma suma masu haɗa bidiyon na AI za su cigaba da inganta aikinsu, don haka nan da wani lokaci wannan shawarar ba za ta yi amfani ba. Kuma wannan lamari ne da zai iya faruwa cikin ƙanƙanin lokaci ko kuma ya ɗauki shekaru.
Amma idan ka yi amfani da wannan tsarin wajen tantance bidiyon na bogi, ko da an samu wasu sauye-sauye wajen ƙirƙirar bidiyon na bogi, za ka ji sauƙin ganewa.
Amma dai ya kamata a fahimci cewa ba duk faye-fayen bidiyon ƙirƙirarriyar basira ba ne ba su da kyau da ingancin hoto. Akwai masu kyau da haske da inganci sosai.
Sannan ba duk faye-fayen bidiyon da ba su da hoto mai kyau ba ne na bogi, kamar yadda Farfesa Mathew Stamm ya nuna, wanda darakta ne a cibiyar tantance bayanai a Jami'ar Drexel da ke Amurka.

Asalin hoton, Serenity Strull/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Har yanzu fitattun fasahohin da ke haɗa bidiyo irin su Google's Veo da OpenAI's Sora suna da alamun da za a iya gano matsala," in ji Farid.
Ko AI da suka fi inganci suna da illa, musamman wajen motsin hoto da kaɗawar gashi da tufafi. Waɗannan ƙananan matsaloli ne da suke da wahalar fahimta. Amma idan hoton ya fito fes, za a gane cikin sauƙi.
A cikin ƴan watannin da suka gabata, bidiyo da asali na ƙirƙirarriyar basira ne sun ruɗar da mutane da dama.
Wani bidiyon zomo yana tsalle na kwanakin baya ya samu masu kallo sama da miliyan 240 a TikTok. Miliyoyin mutane kuma sun danna alamar so wato "like" a wani bidiyon masoya a birnin New York kafin daga baya suka gane na bogi ne. Nima akwai wani bidiyon wani malamin coci yana wa'azi da ya shammace ni.
Faya-fayen nan duk suna nuna tamkar an naɗe su ne da tsohuwar waya. Bidiyon zomon ya nuna tamkar an ɗauka ne da tsakar dare. Shi ma bidiyon masoyan haka. Haka na malamin cocin.
Farid ya ce yawanci bidiyon AI ba su da tsawo, "yawancin tsayinsu bai ma kai tsayin irin bidiyon da aka saba gani a TikTok da Instagram ba, waɗanda yawanci tsakanin daƙiƙa 30 ne zuwa 60. Amma yawancin bidiyon da nazarta daƙiƙa tsakani 6 zuwa 10"
Ya ƙara da cewa haɗa bidiyo da ƙirƙirarriyar basira na da tsada sosai, "shi ya sa dole suke haɗa ƙananan bidiyo. Sannan akwai alamar tsayawa a kusan duk bayan daƙiƙia ɗaya."
Farid ya ƙara da cewa ɓatagari suna amfani da bidiyon AI wajen ruɗar da mutane. "Idan ina so in ruɗar da wani, sai kawai in ƙirƙiri bidiyo na bogi, sai in rage ingancin hoton bidiyon, amma ya zama za a iya kalla."

Asalin hoton, Crédit : Serenity Strull/Getty Images
Matsalar ita ce a daidai lokacin da kuke karatu domin gano bidiyon na bogi, suma kamfanonin fasaha suna kashe biliyoyin daloli wajen inganta ayyukan ƙirƙirarriyar basira.
"Idan aka yi gyara a bidiyo, akwai alamar da ake gane cewa an taɓa shi kamar yadda ake iya ganin shatan hannu a wajen aikata laifi," in ji Stamm.
Masanin harkokin intanet, Mike Caulfield ya ce ya ce babbar hanyar da ta fi dacewa ita ce mutane su canja yadda suke kalla da aminta da bayanan da suka gani a intanet.
Neman kura-kuran AI ba abu ba ne da zai wanzu domin suma kamfanonin na fasaha suna ta ƙoƙarin magance matsalolin.
"A tunanin, nan gaba bidiyo zai koma tamkar rubutu ne, inda zai zama asalinsa ake nema sama da abin da ke ciki," in ji Caufield.
Ba ma karanta rubutu sai kawai mu fara kokwanto saboda rubutacce ne. Idan muna kokwanto, komawa ga asalin rubutun muke yi da kuma inda aka samo labari. A baya bidiyo da hoto ne suka fi wahalar ƙirƙira, amma yanzu ba haka lamarin yake ba.
"Ina tunanin wannan ne barazana mafi girma kan yaƙi da bayanan bogi a intanet a ƙarni na 21," in ji Stamm.
"Amma sabuwar matsala ce, don haka waɗanda suke aiki domin magance matsalar ba su da yawa, sannan kullum suna ƙara faɗaɗa ɓangaren. Muna buƙatar horar da mutane da samar da dokoki da nemo wasu hanyoyin fasaha domin daƙile barazanar."










