Me ake tuhumar Diezani Madueke da aikatawa a kotun Landan?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Steve Swann
- Aiko rahoto daga, Southwark Crown Court
- Lokacin karatu: Minti 3
A zaman kotu da aka fara kan zargin tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya da rashawa da karɓar na goro daga kamfanonin man fetur, an ce tsohuwar ministar ta kashe sama da fam miliyan 2 a kantin kayan alfarma na Harrods da ke Landan.
Diezani Alison-Madueke mai shekara 65 na fuskantar shari'a ne kan zargin gudanar da rayuwar ƙasaita a Birtaniya.
Daga cikin abubuwan ƙasaita da ake zargi tana yi, akwai zama a gidan miliyoyin fam, da amfani da motocin haya na alfarma da amfani da jirgin sama na alfarma wajen tafiye-tafiye da kuma samun tsabar fam 100,000.
Sauran abubuwan da ake zarginta da su, sun haɗa da kashe fam miliyan 4.6 wajen gyarawa da sabunta wasu kadarori a Landan da Buckinghamshire, kamar yadda aka bayyana wa kotun Southwark Crown.
Sai dai ta ƙaryata tuhume-tuhume guda biyar da ake zarginta da su na karɓar cin hanci, da haɗa baki wajen aikata rashawa.
Alison-Madueke tsohuwar ministar albarkatun man fetur ce tsakanin 2010 zuwa 2015 a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
An bayyana wa kotun ne cewa an kashe fam miliyan 2 a madadin Alison-Madueke a babban kantin Harrods ta hanyar amfani da katin cire kuɗi na wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mai suna Kolawole Aluko da kuma katin cire kuɗin kamfaninsa Tenka Limited.
Wadda ake zargin tana da tsayayyen mai sayayya a kantin, wanda yake matakin mai hulɗa da kanti mai launin baƙi wato 'Black Tier' wanda dole ya kai cinikin sama da fam 10,000 a shekara kamar yadda aka bayyana wa kotun.
An kuma bayyana wa alƙalin cewa ta yi rayuwa a Birtaniyya, inda take da ma'aikata kamar mai kula da gida da mai kula da yara da mai yanke fulawa da sauran su.
Sannan albashin ma'aikatan da sauran kuɗaɗen kula da gidan duk suna zuwa ne daga wani kamfanin makamashi waɗanda suke kasuwanci da kamfanin man fetur na Najeriya wato NNPCL.
"Wannan tuhuma ce ta zargin cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da ɓangaren makamashi a Najeriya a tsakanin 2011 zuwa 2015," in ji mai gabatar da ƙara Alexandra Healy KC.
"A wannan lokacin ne duk wani mai neman kwantigari mai kyau daga NNPCL ko sassansa yana bayar da cin hanci ga Alison-Madueke."
Healy ya ƙara da cewa, "za a yi mamakin me ya sa ake gabatar da ƙarar abin da ya shafi Najeriya a nan Birtaniya, amma maganar ita ce lamarin ya shafi duniya ne saboda cin hanci da rashawa na jawo tsaiko a kasuwancin duniya."

Asalin hoton, PA Media
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An kuma nuna wa alƙalan hotunan kadarorin da ake zargin tsohuwar ministar tana rayuwa a ciki a Buckinghamshire wanda wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya mai suna Olajide Omokore mai kamfanin makamashi na Atlantic Energy ya saya a 2010.
Daga 2011 ne aka tunanin Alison-Madueke ta fara amfani da gidan na alfarma, inda ta zauna sau uku ko huɗu a shekara biyu, sannan ta yi mako shida tana rubuta littafi a kan tarihin shugaban Najeriya.
Ana kuma tunanin kamfanin Tenka Limited ne ya kashe kusan fam 300,000 wajen gyara gidan.
An kuma bayyana wa kotun cewa tsakanin Mayun 2011 zuwa Janairun 2014, an biya kuɗin haya a wasu gidaje biyu a Landan, inda ta zauna tare da mahaifiyarta.
Ɗan'uwan Alison-Madueke ma, Doye Agama mai shekara 69 na cikin waɗanda suke fuskantar zargin cin hanci da rashawa da kuma wani Ayinde.
Da Ayinde da Agama duk sun musanta zargin da ake musu.
Ana dai ci gaba da sauraron shari'ar, wadda ake tunanin za a yi mako 12 ana yi.
Man fetur na taka muhimmiyar rawa a tattalin arzikin Najeriya, amma duk da arzikin man da ƙasar ke da shi, mafi yawan ƴan ƙasar ba su gani a ƙasa ba.
Ƙasar na cikin ƙasashe 13 mambobin ƙungiyar da suka fi arzikin man fetur wato Opec.











