Komawar Abba APC: Wa ke da riba wa ke da asara?

Asalin hoton, Social handles
Komawar Gwamnan jihar Kabo, Abba Kabir Yusuf jam'iyyar APC na ci gaba da ɗaukar hankali a siyasar arewacin Najeriya.
Yayin da wasu ke ci gaba da murna wasu kuma takaici matakin ya janyo musu, sakamakon abin da matakin gwamnan ya janyo musu.
Gwamnan dai ya ce ya zaɓi komawa APC ne saboda ci gaban al'ummar Kano.
Yayin da yake jawabi a wurin taron komawar tasa, Abba Kabir ya ce ya ɗauki matakin ne domin jihar Kanio ta amfana da manyan ayyukan gwmanatin tarayya.
Matakin gwamnan zai sauya abubuwa masu yawa a fagen siyasar Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
Yayin da matakin zai yi wa wasu da dama daɗi, wasu kuwa akasin hakan ne, saboda ba yadda suka so ba.
BBC ta yi nazarin ɓangarorin siyasa da za su ƙirga riba ko asara saboda matakin an gwamnan Kano.
Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Fadar Shugaban Najeriya
Ɗaya daga cikin waɗanda matakin Abba Kabir Yusuf zai fi taimakawa shi ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu.
Jihar Kano ce kan gaba a yawan samar da ƙuri'a a lokacin zaɓe, don haka kowane ɗan takarar shugaban ƙasa zai yi burin lashe jihar.
A baya-bayan nan ne Tinubu ya gana da Abba a fadarsa da ke Villa, wani abu da masana ke hasashen sun tattauna batun komawar gwamnan APC.
Duk jihar da APC ke mulki ana sa ran Tinubu zai iya lasheta, kodayake ba dole ba ne, domin an ga yadda Tinubun ya kasa cin Kano da Legas da Kaduna a 2023, duk kuwa da cewa APC ce ke mulkin jihohin a lokacin.
Sai dai duk da haka, wannan abin maraba ne ga Shugaba Tinubu, saboda mai yiwuwa zai fi amfana da ƙaruwar idan ya sake tsayawa takara a zaɓen 2027.
Akwai masu zargin cewa gwamnatinsa na amfani da kwaɗaitarwa da razana 'yan adawa don su koma jam'iyyarsa.
Gwamna Abba Gida-gida

Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/FB
Hausawa na cewa kowa ya sha inuwar gemu bai kai ya maƙogoro ba, don haka wasu ke ganin Abba ne kan gaba cikin waɗanda matakin zai amfanar.
A lokacin bikin komawarsa APC, Abdullahi Ganduje ya ce Abba ne ɗan takarar APC ɗaya tilo a 2027.
Haka shi ma Sanata Barau ya ce ya janye ƙudurinsa na tsayawa takara a zaɓen 2027.
Abin da ya sa wasu ke ganin matakin tamkar share wa Abba hanyar sakewa tsayawa takara a 2027.
Sai dai a gefe guda wasu na ganin a yanzu gwamnatinsa za ta fuskanci cikas kasancewar wasu jiga-jiganta sun ajiye muƙamansu.
Don haka yanzu ƙalubalen da zai fuskanta shi ne rabon muƙamai musamman ga jiga-jigan APCn Kano, wani abu da in bai yi taka-tsantsan ba, zai haira wa haɗewar tasu matsala.
Jihar Kano
A lokacin komawarsa APC, Abba Kabir Yusuf ya ce daga cikin dalilansa na komawa APC shi ne samar wa Kano ayyukan ci gaba daga gwamnatin tarayya.
''Akwai manyan damarmaki daga gwamnatin tarayya da ba ma samunsu saboda ba jam'iyyarsu ɗaya ba'', in ji Gwamnan.
Don haka wasu ke ganin a yanzu jihar ka iya amfana da manyan ayyukan gwamnatin tarayya da samun damarmaki, kasancewarta ɗaya daga cikin jihohin mafiya muhimmanci a tsarin zaɓen ƙasar.
Jam'iyyar APC
Jam'iyyar APC na daga cikin waɗanda komawar gwamnan za ta amfanar, saboda ƙarin gwamana sukutum da jam'iyyar ta samu a jihar - da fi kowace muhimmanci a zaɓen shugaban Najeriya.
Kawo yanzu Abba Kabir Yusuf shi ne gwamna na bakwai da ya koma APC bayan zaɓen 2023, kenan yanzu jam'iyyar na da adadin gwamnoni 29 cikin jihohin ƙasar 36.
Kuma ana ganin idan ta shiga zaɓen 2027 da waɗannan gwamnonin, kayar da ita zai zama wani jan aiki a gaban 'yan adawa.
Haka nan kuma komawar Abba Kabir cikinta zai samar mata da ƙarin yanmajalisu wakilai na tarayya kasancewar ya koma da guda takwas, baya ga na jiha 22 ciki har da kakakin majalaisar dokokin jihar.
Abdullahi Umar Ganduje

Asalin hoton, Aminu Dahiru Ahmed
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Dokta Abdullahi Umar Ganduje na cikin masu ƙirga riba da wannan mataki, kasancewar a yanzu gwamnatin Kano ta koma hannunsu a matsayinsa na jagoran jam'iyyar a jihar.
Ganduje ya jima yana adawa da jam'iyyar NNPP mai mulkin Kano, da kuma jagoranta, Dokta Rabi'u Kwankwaso, kasancewar shi da jam'iyyarsa sun ƙwaci mulkin jihar a hannunsa a 2023.
Da wannan mataki na komawar Abba APC, kenan yanzu Ganduje ya yi nasara a kan babban abokin adawarsa wato Kwankwaso.
Sai dai wata matsalar da Ganduje zai fuskanta ita ce rasa muƙaminsa na jagoran APC a Kano.
Dokta Rabi'u Kwankwaso

Asalin hoton, Rabi'u Kwankwanso
Babban wanda wannan mataki ya fi kawowa nakasu ko rashin jin daɗi shi ne jagoran Kwankwasiyya, Dokta Rabi'u Musa Kwankwaso.
Matakin Gwamna Abba na nufin, Sanata Kwankwso ya rasa gwamna ɗaya tilo da ya samu a zaɓen 2023.
Komawar Abba da wasu jiga-jigan tafiyarsa ta Kwankwasiyya zuwa APC na iya ƙara dusashe fatansa na ci gaba da iko da siyasar Kano.
Zai fuskanci ƙarin matsin lambar siyasa a kan ya yi haɗin gwiwa da wata jam'iyya.
Haka kuma wannan mataki zai sare wa jagoran Kwankwansiyyar gwiwa na sake yarda da wani yaron siyasa a nan gaba, wani abu kuma da zai taɓa tasirinsa a siyasa.
Jam'iyyar NNPP
Jam'iyyar NNPP ce kan gaba cikin waɗanda matakin Abba gida-gida ba zai yi wa dadi ba.
Dama Abba ne gwamna ɗaya tilo da jam'iyyar ke da shi, don haka yanzu matakin na nufin jam'iyyar ta rasa kujerar gwamna da take tunƙaho da ita.
Haka kuma gwamnan da ta rasa ya tafi da kujerun 'yan majalisun dokokinta da dama a Kano da tarayya, wanda hakan babban rashi ne ga jam'iyyar.
Sanata Barau Jibrin

Asalin hoton, Barau i Jibrin
Duk da bai riga ya ayyana ba, amma mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin ya sha nuna aniyarsa ta tsayawa takarar gwamnan Kano a zaɓe mai zuwa.
Ya yi ta haƙilon karɓar ƴan Kwankwasiyya da hidimtawa APC don cikar burinsa da na Tinubu.
Ana yi masa kallon mutum mafi girman muƙami a jam'iyyar APC kafin yanzu da Abba ya zo.
Sojojin Baka
Sojojin baka da yawa a Kano ba za su yi farin ciki da komawar Abba APC ba a yanzu.
Saboda hakan zai rufe musu hanyar cin abinci daga 'yan siyasa masu neman takarar gwamna da suke tallatawa a gidajen rediyo.
Haka ma ƴan wankiya, masu zuwa wurin wani su ce su yaran wani ne sun zo a wanke su domin kuɗi, a yanzu kasuwarsu ta rufe.











