Ƙungiyoyi bakwai na rububin Sterling, Man U ta fidda rai daga Palmer

Wakilan ɗan wasan gefe na Ingila Raheem Sterling, mai shekaru 31, wanda ya bar Chelsea a farkon wannan makon, suna tattaunawa da ƙungiyoyi bakwai na matakin gasar zakarun Turai waɗanda ke son sayan shi. (Sky Sports)
Tottenham na da ra'ayin ɗaukar Sterling, wanda yanzu haka bai da kungiya, kuma kocinta Thomas Frank yana maraba da yunkurin. (Teamtalk)
Suma Burnley, da wasu ƙungiyoyin Serie A na Italiya, kamar Juventus da Napoli, suma suna sha'awar Sterling. (Mail)
Manchester United ba za ta sayi ɗan wasan tsakiya na Chelsea Cole Palmer, mai shekaru 23 ba, a wannan bazarar, domin kudin da aka sanya masa ya zarce kima, inji shugabannin kungiyar. (Mirror)
Chelsea na shirin kashe Yuro miliyan 150 (£129m) kan ɗan wasan tsakiya na Real Madrid da Ingila Jude Bellingham, mai shekaru 22, a wannan bazarar. (Fichajes)
Ajax za ta sayi dan wasan tsakiya na Ukraine Oleksandr Zinchenko, mai shekaru 29, wanda ke zaman aro a Nottingham Forest daga Arsenal, kan yarjejeniyar dindindin kan kusan Yuro miliyan 1.5 (£1.3m). (Fabrizio Romano)
Kocin Aston Villa Unai Emery, mai shekaru 54, yana cikin jerin wadanda Real Madrid za ta zaɓa don zama sabon kocin ƙungiyar ta Spaniya a wannan bazarar. (Sky Germany)
Chelsea na ci gaba da tattaunawa da Rennes don siyan ɗan wasan baya na tsakiya na Faransa mai shekaru 20 Jeremy Jacquet kafin a rufe kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu. (Givemesport)
Real Madrid na son siyan ɗan wasan baya na Manchester United da Portugal Diogo Dalot, mai shekaru 26, saboda raunin bayansu. (Fichajes)
Manchester City ta amince da yarjejeniyar aika ɗan wasan baya na Ingila mai shekaru 17 Stephen Mfuni zuwa Watford a matsayin aro har zuwa ƙarshen kakar wasa. (Fabrizio Romano)











