Afrika ta Kudu ta kori jami'in diflomasiyyar Isra'ila

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta kori babban jami’in diflomasiyyar Isra’ila inda ta ba shi sa'o'i 72 ya bar ƙasar.
Ma’aikatar hulɗa da ƙasashen waje ta ce wannan mataki ya biyo bayan abin da ta bayyana a matsayin “take haƙƙin dokokin diflomasiyya da ba za a yarda da su ba, wanda ke ƙalubalantar ikon mallakar Afirka ta Kudu kai tsaye.”
A cikin wata sanarwa, hukumomin Afirka ta Kudu sun zargi gwamnatin Isra’ila da amfani da shafukan sada zumunta wajen harin shugaba Cyril Ramaphosa.
Sannan sun ce ofishin jakadancin Isra’ila bai sanar da su ba lokacin da manyan jami’an Isra’ila suka ziyarci ƙasar.
Hukumomin sun ƙara da cewa waɗannan ayyuka suna nuna cin zarafin haƙƙin diflomasiyya kuma suna rage amincewar da ake buƙata tsakanin ƙasashen biyu.
Sakamakon haka, hukumomin suka ayyana cewa ba sa marhaba da jami'in diflomasiyyar na Isra'ila kuma sun ba shi kwanaki uku ya bar ƙasar.
Dangantaka tsakanin Afirka ta Kudu da Isra’ila ta tsananta tun bayan da ƙasar ta shigar da ƙara a Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICJ a shekarar 2023, inda take zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi a Zirin Gaza, abin da Isra’ila ta ƙi amincewa da shi.
BBC ta tuntubi ofishin jakadancin Isra’ila a Pritoria domin jin ta bakinsa.








