Makwancin Sheikh Ahmad Al Tijani a Moroko

- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Aiko rahoto daga, BBC Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Fes el Bali birni ne da ke yankin tsakiyar arewacin ƙasar Moroko-wanda ya kasance tamkar birni a cikin wani birni.
An kafa shi a tsakanin karni na 8 da 9, kuma wannan birni (Madina) mai tarihi ba matattarar al'adun Moroko ba ne kaɗai amma ga miliyoyin mabiya ɗarikar Tijjaniya birnin ne wanda ya kasance makwancin ƙarshe na ɗaya daga cikin manyan malamai da waliyyai na Musulunci: Sheikh Ahmad al-Tijani.
Yayin da Fes el-Bali ya kasance birni na ƴan Moroko, kasancewar kabarin Sheikh a birnin ya sa ya zama wuri mai matuƙar muhimmanci ga Musulman Afrika da ma duniya baki daya.
Ba a raba wannan birnin da tarin baƙin da ke zuwa daga Senegal da Mali, da Najeriya, domin kawo ziyara ta musamman.
Muhimmancin birnin Fes el bali

Hukumar kula da al'adu da ilimi ta majalisar ɗinkin duniya (UNESCO) ta ayyana Fes el Bali a matsayin wurin tarihi na duniya a shekarar 1981 a ƙarƙashin sunan Medina na Fez.
Yanayin birnin bai sauya sosai daga yadda yake a shekarun baya ba inda ya ke da dubban tituna, ga yawan masallatai, da makarantu da kasuwanni da kuma gidaje.
Wannan birnin mai dimbin tarihi ya janyo masu ziyara sama da miliyan 1.5 zuwa Fes a shekarar 2023 kaɗai, lamarin da ya sanya Moroko ta kasance wurin yawon bude ido mafi shahara a nahiyar Afirka.
Shugaban Hukumar kula da yawon buɗe ido ta ƙasar Moroko, Ahmed Sentissi ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin ƙasar ta tashi tsaye domin inganta ababen more rayuwa a birnin: ''Kowace shekara miliyoyin mutane na zuwa wannan birni kuma ya kamata mu kula da buƙatunsu. A bara mun karɓi baƙuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika kuma a 2030 za mu shirya gasar cin kofin duniya saboda haka dole ne mu shirya wa hakan,'' in ji shi
Addini na taka muhimmiyar rawa a Fes el Bali. Ana iya jin kiran sallah daga ɗimbin masallatai da ake da su a birnin.
Kuma duk da kwararar miliyoyin masu yawon buɗe ido daga sassa daban-daban na duniya, tsohuwar madinar ta ci gaba da zama wurin ibada da kasuwanci da kuma wurin zama ga ɗimbin al'ummar yankin.

Har ila yau, a birnin Fes ake da jami'ar Al Quaraouiyine wadda ita ce akasari ake yi wa ganin jami'a ta farko a duniya wadda Fatima al-Fihri ce ta kafa ta a matsayin masallaci a shekara ta 857-859 kuma daga baya ta zama ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a duniya.
Ɗaliban jami'ar dai na zuwa ne daga fadin ƙasar Morocco da kuma Musulmai daga yammacin Afrika, wasu kuma daga ƙasashen ƙetare. An fara karɓar mata a makarantar ne a shekarun 1940 bayan ƙungiyoyin kare haƙƙin mata sun matsa lamba kan gwamnatin Faransa mai mulkin mallaka a lokacin.
Wane ne Sheikh Ahmad Al Tijani
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Sheikh Ahmad Al Tijani a ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 1737 a garin Ain Madhi da ke ƙasar Algeria.
Ya karanci Alqur'ani a ƙarƙashin koyarwar Mohammed Ba'afiyya a Ain Madhi sannan kuma ya karanci ayyukan fikihu na Khalil ibn Ishaq al-Jundi waɗanda aka rubuta ƙarƙashin mazhabar Malikiyya.
A Shekarar 1757, Tijani ya bar ƙauyensa zuwa Fez. A can ne ya shiga ƙungiyar Sufaye guda uku, wato Kadiriyya, Nasiriyya, da kuma tarikar Ahmad al-Habib bn Muhammed.
Daga baya ya yi koyarwa na tsawon shekara daya a birnin Tunis inda ya samu wasu nasarori da dama. Ya tashi daga Tunis zuwa Masar inda ya haɗu da Mahmud al-Kurdi na ɗarikar Khalwati a birnin Alkahira. Tijjani ya isa Makka a ƙarshen shekara ta 1773 ya yi aikin hajji.
A Shekarar 1781 Sheikh Ahmed Tijani ya kafa ɗarikar Tijjaniyya.
Ba da daɗewa ba koyarwarsa ta samu karɓuwa a yankunan Larabawa da ke kewaye da Abi Samghun. Shaihu Tijjani ya rayu a Abi Samghun kimanin shekaru goma sha biyar. A shekarar 1792 ya koma Fes.
A Fes, Tijani ya samu karɓuwa sosai a wurin Mawlay Sulayman, Sarkin Moroko. inda ya samar masa gida ya kuma naɗa shi dan majalisarsa ta ilimi.
Baya ga kasancewa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmed el Tijani ya kasance shararren ɗan kasuwa kuma attajiri mai kula da talakawa.
An binne shi a birnin Fes bayan ya rasu a shekara ta 1815.
Kabarin Sheikh Ahmad Al Tijani

Zaouia Thiqat al-Tijani, da ke kusa da shahararriyar jami'ar nan ta Al-Quaraouiyine, ya kasance wurin ziyara ga miliyoyin mabiya ɗariƙar Tijjaniya daga sassa daban-daban na duniya kasancewarsa makwancin ƙarshe na Sheikh Ahmad Al Tijani.
An fara gina shi a shekara ta 1800 sannan kuma aka ci gaba da faɗaɗa shi a shekarun da suka biyo baya. A lokacin bikin Maulidun-nabiy na shekara-shekara, yana kasancewa wurin ibada na musamman ga Musulmai da dama daga ƙasashen duniya, waɗanda suka haɗa da Moroko da Algeria da Masar, da kuma yankin kudu da hamadar Sahara, musamman Senegal da Mali da Najeriya.
A lokacin da al-Tijani ya rasu a shekara ta 1815 an binne shi a cikin wurin, wanda tun daga lokacin aka ci gaba da faɗaɗa shi.

Wannan wuri yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar mabiya ɗariƙar Tijjaniya da ma Musulmi baki ɗaya inda da dama ke kai ziyara domin yin addu'a, kamar yadda Sheikh Halliru Maraya, wani babban malamin addinin Musulunci a Najeriya ya bayyana ''Wuri ne da aka binne ɗaya daga cikin waliyyai, kuma kamar yadda malamai ke faɗa, duk inda aka ambaci bawan Allan na ƙwarai, rahama na sauka a wurin.''
Shiekh Maraya ya ƙara da cewa wurin na da muhimmanci sakamakon an binne mahaddacin alƙur'ani kuma mai ƙoƙarin ibada wanda ka iya zaburar da duk waɗanda ke ziyartar kabarinsa su ma su yi yunƙurin yin koyi da irin halayensa.
''Za ka ga cewa mabiya ɗariƙar Tijjaniya da waɗanda ma ba sa ɗariƙar Tijjaniya, har da da waɗanda ba Musulmi ba suna zaiyartar wannan wuri saboda wuri ne wanda Allah Ya yi masa albarka,'' in ji Sheikh Maraya.











