Abin da muka sani kan harbe-harbe da fashe-fashen da aka ji a babban birnin Nijar

Wani hoto da aka ɗauka na filin jirgin ƙasa da ƙasa na Diori Hamari da aka ɗauka a ranar 24 ga Fabrailun 2024

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, An ji harbe-harben ne a kusa da babban filin jirgin Nijar da ke Niamey, babban birnin ƙasar
    • Marubuci, Basillioh Rukanga
  • Lokacin karatu: Minti 2

An ji ƙarar harbe-harbe da fashe-fashe a kusa da babban filin jirgin sama na Diori Hamari da ke babban birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da aukuwar lamarin, sannan wasu faye-fayen bidiyo sun bayyana yadda wasu na'urorin kariya na sararin samaniya ke ta ƙoƙarin tare wasu abubuwa da ba a iya tantancewa da tsakar dare.

Daga baya dai komai ya lafa, kamar yadda aka ruwaito daga wani jami'in gwamnati, duk da cewa bai yi ƙarin haske ba kan lamarin ba.

Har yanzu dai babu tabbacin abin da ya janyo fashe-fashen har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, sannan babu tabbacin ko akwai wanda ya rasa rai ko kuma irin ɓarnar da lamarin ya yi.

Hukumomi dai ba su ce komai ba kan batun.

Wani mazaunin birnin Niamey ya shaida wa BBC cewa "mun ji ƙarar bindigogi tun kimanin ƙarfe 12 na dare har zuwa goshin ƙarfe biyu," musamman a wajen unguwannin Gamkalea tondi-gamay Aeroport.

Ya ƙara da cewa "mutane sun kwana cikin ruɗani da fargaba sanadiyyar tsawaitar ƙarar bindigogin da suka yamutsa hazon sararin samaniyar wannan yankin."

An fara jin harbe-harbe da fashe-fashen ne da tsakar dare, kamar yadda mazauna kusa da filin jirgin sama suka bayyana wa kafar AFP. Sai dai sun ƙara da cewa bayan kimanin awa biyu ne komai ya lafa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai sansanin sojin sama a cikin filin jirgin saman, sannan akwai tafiyar kimanin kilomita 10 zuwa fadar shugaban ƙasa ta Nijar.

Kamar maƙwabtanta Burkina Faso da Mali, Jamhuriyar Nijar na fama da matsalolin tsaro, ciki har da yaƙi da mayaƙa masu iƙirarin jihadi, waɗanda suke kai hare-hare a ƙasar.

Ƙasar Nijar na cikin ƙasashen da suke da arzikin uranium a duniya.

Yanzu haka akwai uranium mai yawan gaske da ya maƙale a filin jirgin, wanda aka kasa fitar da shi saboda matsalolin shari'a da takun-saƙar diflomasiyya da ke tsakanin ƙasar da Faransa.

An fara samun matsalolin ne tun bayan da gwamnatin sojin ƙasar ta ƙwace cibiyoyin haƙar ma'adinan uranium.

"Komai ya lafa, babu wata matsala," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya ruwaito daga ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ba tare da cikakken bayani ba.

Jami'in gwamnatin ya bayyana wa kafar cewa suna ci gaba a gudanar da bincike ko fashe-fashen na da alaƙa da uraniun ɗin da ke ajiye a filin jigrin.

Nijar dai na ƙarƙashin mulkin Janar Abdourahmane Tchiani ne, wanda ya karɓi mulki bayan juyin mulkin watan Yulin 2023.