Caf ta dakatar da kocin Senegal, sannan ta ci tarar tawagar ƙasar

Ƴanwasan ƙasar Senegal sun nuna rashin jin daɗinsu a wasan ƙarshe na Afcon

Asalin hoton, TORBJORN TANDE/DEFODI VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Ƴanwasan ƙasar Senegal sun nuna rashin jin daɗinsu a wasan ƙarshe na Afcon
Lokacin karatu: Minti 3

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka Caf ta fitar da rahoton binciken da ta yi game da matsalar da aka samu a wasan ƙarshe na cin kofin nahiyar Afirka ta 2025 a Moroko, lamarin da ya haifar da hargitsi ana tsaka da wasa.

Bayan gasar, wadda Senegal ta lashe, hukumar ta Caf ta kafa kwamitin bincike, inda ta ce za ta ladabtar da duk wanda aka samu da hannu a rikita-rikitar da aka yi.

Kocin Senegal Pape Thiaw ne dai ya umarci ƴan'wasansa da su fice daga filin wasa bayan Moroko ta samu bugun fenariti a kusa da ƙarshen wasan.

Bayan kusan minti 17 ana kai-komo ne ɗan'wasan Senegal, Sadio Mane ya buƙaci abokan wasansa da su koma filin wasan, domin su ci gaba da fafata wasan na ƙarshe.

Sai dai kuma ɗan'wasan Moroko, Brahim Diaz ya ɓarar da bugun fenaretin, wanda hakan ya sa wasan ya shiga lokacin ɗoriya, sannan a ƙarshe Senegal ta samu nasara da ci ɗaya mai ban haushi.

Hukumomin Caf da Fifa duk sun yi Allah-wadai da abin da ƴan wasan Senegal suka yi, da ma matakin da kocin ya ɗauka na buƙatar ƴanwasan su fice daga filin wasan.

Tun bayan wasan ne shugaban Fifa Gianni Infantino wanda ya je kallon wasan na ƙarshe ya ce ba za su lamunci abin da Senegal ta yi ba, sannan ya yi kira da a hukunta duk waɗanda suke da hannu a hargitsin.

Bayan makonni ana gudanar da bincike, a ƙarshe dai Caf ta fitar da rahotonta da kuma matakan ladabtarwa da ta ɗauka kan duk wanda ta samu da laifi.

Lokacin da ƴan'wasan Morocco ke yunƙurin ɗauke tawul ɗin golan Senegal Mendy

Asalin hoton, SAMAH ZIDAN/ANADOLU VIA GETTY IMAGES

Bayanan hoto, Lokacin da ƴan'wasan Morocco ke yunƙurin ɗauke tawul ɗin golan Senegal Mendy

Hukunci kan Senegal

Kwamitin ladaftarwa na Caf ya ce ya dakatar da kocin Senegal Pape Thiaw na wasa biyar bisa abin da kwamitin ya kira saɓa dokokin ƙwallon ƙafa da lalata harkar a idon duniya, duk da cewa ya bayar da haƙuri bayan wasan.

Hukuncin da hukumar ta sanar a kan Senegal su ne:

  • Dakatar da kocin wasa 5 bisa umartar ƴan'wasansa su fice dafa fili
  • Cin tarar kocin dala 100,000
  • Dakatar da ɗan wasan tawagar Iliman Ndiaye na wasa biyu bisa karya dokokin ƙwallon ƙafa
  • Dakatar da Ismaila Sarr wasa biyu saboda karya doka
  • Cin tawagar ƙasar tarar dala 300,000
  • Cin hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar tarar 300,000 bisa laifin da ƴan'wasanta suka aikata
  • Hukumar za ta kuma ta biya dala 15,000 na katin gargaɗi biyar da ƴanwasan suka samu.
An dakatar da Thiaw wasa biyar

Asalin hoton, SENEGALESE FOOTBALL FEDERATION

Bayanan hoto, An dakatar da Thiaw wasa biyar

Tarar da aka ci Moroko da ƴan wasanta

Bayan wasan ne Moroko ta aika da kokenta zuwa ga hukumar Caf, inda ta ce abin da Senegal ta yi ya saɓa da dokokin ƙwallon ƙafa, sannan ta ce abin da ƴan wasanta suka yi ya karya gwiwar ƴan'wasanta, wanda a cewarta, shi ne ya sa Brahim Diaz ya ɓarar da fenariti.

"Sashe na 82 na kudin hukumar Caf ya nuna cewa duk tawagar da ta ƙi buga wasa ko ta fice daga filin wasan ba tare da izini ko amincewar hukumar ba, to za ta rasa wasan ne.

"Sashe na 84 na kundin ya ƙara da cewa idan tawagar ƙwallon ƙafa ta fice daga wasa, kamar wanda aka yi a wasan ƙarshe, ta rasa wasan da ci uku, inda za a ba ɗaya tawagar nasara."

Sai dai Caf ta yi watsi da ƙorafin, inda ta tabbatar da nasarar Senegal.

Ga matakan da aka ɗauka kan Morocco.

  • Dakatar da ɗan wasa Achraf Hakimi wasa biyu bisa saɓa dokokin wasan ƙwallon ƙafa
  • Dakatar da ɗan wasa Ismael Saibari wasa uku bisa saɓa dokokin wasan ƙwallon ƙafa
  • Tarar dala 100,000 kan ɗan wasa Ismael Saibari
  • Tarar dala 200,000 kan hukumar ƙwallon ƙafa ta Moroko bisa laifin da yara masu ɗauko ƙwallo suka aikata
  • Tarar dala 100,000 kan hukumar bisa yunƙurin ƴan wasan na hana alƙalin wasa duba na'urar VAR
  • Tarar dala 15,000 kan hukumar bisa laifin amfani da hasken kashe ido da magoya bayan ƙasar suka yi.

Sai dai tawagogin ƙasashen biyu suna da ƴancin ɗaukaka ƙara