'Sun ce za su kashe mu ko da an biya kuɗin fansa'

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Ɗaya daga cikin mutane 11 da suka kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane a garin Isapa na jihar Kwara, Gbemisola ta ce ta kwashe kwanaki takwas a daji bayan ta tsere daga hannun waɗanda suka sace su.
Wannan mata da mutanenta suka fi sani da Iya Beskë an yi garkuwa da ita tare da wasu mutum 10 a garin Isapa a watan Nuwambar bara.
Da take tattaunawa da BBC, Iya Beskë ta ce babu abinci ko ruwa a dajin da take bayan ta kufce daga hannun masu garkuwa da mutane.
Ta ce baya ga mutane 11 da aka sace daga gari ɗaya, akwai sauran mutane da aka tattaro daga wasu wurare aka haɗa su wuri ɗaya.
'Mutum goma ke raba gorar ruwa ɗaya'
Misis Gbemisola ta ce, "ƴan bindigar na cin abinci mai kyau, amma suna ciyar da mu abincin da ba shi da gishiri ko mai.
"Mu takwas zuwa goma ke raba gorar ruwa ɗaya a rana."
"Da muka nemi ruwa daga wurinsu sai suka ce za su sayi ruwa bayan mutanen mu sun ki biyan kuɗin da suke nema.
"Wannan lamarin ya yi matuƙar muni har ya kai ga mun yanke shawarar guduwa domin tsira da rayukanmu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Mu da ke jin Hausa, mu ne muka fara jin masu garkuwa da mutanen suna cewa, ko mutanenmu sun biya ko ba su biya ba, za su kashe mu.''
Ta ce hakan ya sa suka ce gara su mutu a matsayin jarumai yayin da suke neman tsira a maimakon su mutu kamar ƙananan yara a hannun masu garkuwa da mutane.
Gbemisola ta ce, "Mun bi hanyoyi daban-daban a lokacin da za mu tsere don gudun kada su kama mu."
Muka tashi da misalin ƙarfe sha ɗaya na dare, na yi tafiya a cikin dajin har wayewar gari, amma ban isa wani gari ko ƙauye ba.
Ms Gbemisola ta ce, "Lokacin da nake jin ƙishirwa, sai na tsinci wata kwalbar giya, na shanye abin da ke ciki."
"Na yi haka har kwana takwas"
Ta ce ta yi tsananin gajiya har ya kai ga ba za ta iya ci gaba da tafiya ba.
Sai dai ta ce wani Bahaushe ne da ya zo wucewa ya ba ta ruwa ta sha.
Shi ne kuma ya ɗauke ta ya kai ta gidansa. A nan ne Gbemisola ta farfaɗo, ta kuma ci gaba da tafiya.
''Na isa wani gari inda suke Hausa da kuma Yarabanci, su suka ɗauke ni suka ba ni abinci da kayan sa wa.
Sunan garin Langta a ƙaramar hukumar Patigi.''
Bincike dai ya nuna cewa ita ce kaɗai wadda aka gano cikin mutum 11 da ke hannun masu garkuwa da mutane.










